ABINDA YA JAWO WANI KE YIN TAMBAYA WAI SHIN WA YAFI JARUNTAKA TSAKANIN UMAR DA MANZON ALLAH (S. A. W. W) ?
Yana daga cikin mafi illar da magabata suka yiwa muslimci shine murguda tarihi da kuma cancanza shi daga haqiqanin ma'anarsa, domin canza abu daga haqiqaninsa yakan canza ma'anarsa kwata-kwata har ta kai ga lullube gaskiya da qarya.
HIJRAR UMAR BN KHADDAB
Cikin Tafsir na bana naji wani malamin 'Dariqa na bayani dangane da Hijrar Annabi (S. A. W. W) yadda ya fito cikin dare yana sanda (steathly) har yaje gidan Abubakar ya sanar dashi cewa anyi masa umarnin fita zuwa Hijra cikin dare, wanda hakan yasa Abubakar yayi shirin gaggawa don raka Manzon Allah (S. A. W. W).
A cigaba da bayanin yake cewa har ma an rasa wanene yafi jaruntaka tsakanin Abubakar da Aliyu, domin Abubakar ya fita tare da Annabi (S. A. W. W) ba tare da tunanin abinda zai iya samunsu ba. Shi kuma Sayyidinah Aliyu ya kwanta akan gadon Manzon Allah (S. A. W. W) a matsayin fansar ransa Manzon Allah (S. A. W. W) domin za a iya kashe shi in an rasa Annabi (S. A. W. W) cikin gidansa.
Yace, idan kuma muka dawo kan Umar da Manzon Allah (S. A. W. W) sai muga cewa Shi Annabi (S. A. W. W) da ya fito zuwa Hijra buya ya riqa yi har ma sai da ya hanya ta zuwa wani gari kimanin kilometer 40 sannan ya juyo kan ta zuwa Makkah, har ma ya buya a Kogo. Amma shi Umaru da ya fito sai da yabi ta dakin Ka'abah yana cewa;
" YANZU NA FITO HIJRA ZUWA MAKKAH, DUK WANDA KE SON MATANSA SU ZAMA GWAURAYE KO 'YA'YANSA SU ZAMA MARAYU YAZO YA TARE NI ! I am now out to migrate to Mecca, whoever want his wives to be widows or his children to be orphans should come an contact me curiously ! "
Yace, yanzu in abin ayi tambaya ne cewa wa yafi jaruntaka tsakanin Umar da Manzon Allah (S. A. W. W) wa za kuce ? Jama'a suka ce Umar !
Sai yace, to, Annabi (S. A. W. W) ba abin zargi bane, abinda yayi ya zama sunnah, domin da za ace akwai wani abin cutarwa a hanyar zuwa guri kaza sai ka canza hanya, to, da babu mai zarginka domin Annabi (S. A. W. W) ma yayi irin wannan jin tsoron. Idan kuma kaga za ka iya tafiya babu tsoro kamar yadda Umar yayi shike nan.
Subhanal-Lahi ! Wannan wanne irin gurbacewar tunani da fahinta ne haka ? Kuma ba wani abu ya jawo hakan ba face jirkita tarihi da akayi daga haqiqaninsa.
Idan da gaske haka Umar yayi, to, me yasa da Annabi (S. A. W. W) ya aika shi zuwa Makkah ranar yarjejeniyar Hudaibiyyah ya qi ya tafi wai yana tsoron kada a kashe shi ? Sai yace a aika Usman domin shi dan dangi ne ba za a kashe shi ba ?
Sannan kuma in jarumi ne wane arne ya taba kashewa cikin jaruman arnan garin Makkah wanda ya qalubalance su yayin fitarsa zuwa Hijra ?
Asali ma dai yana daga cikin wadanda suka yi Hijrar farko a boye kafin a yiwa Annabi (S. A. W. W) umarnin fita zuwa Hijra, Umar din ya zo cikin wadanda aka ce Saleem Maula Abu Huzaifata ya riqa yiwa limancin sallah a Masjidil-Qubah.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
19TH APRIL, 2021