-Yau ina su Mu’awiya da Yazidu da Sauransu da Suka Yaki bayin Allah? Mutuwa ta tilasta Musu barin abunda suka yi Fada a kai.
-Imam Hassan (as) Yace: “Matsaloli Na duniya Sun fi Sauki daga Shiga Wuta.” Wato gwanda Mutum Ya Fuskanci dukkan Matsaloli da Wahaloli Na duniya Sakamakon bin tafarkin Allah da Yayi ko Kuma rikonsa ga Ahlul-bait da Ya bari Ya je Ya Shiga wuta ranar kiyama.
-Sai Imam Hassan (AS) Yace: “Duk Wanda Yake Yawan tunanin tsawon tafiyar dake gabansa ta zuwa lahira to zai yi tattali.” Wato na zuwa lahirar.
-A Wani Wajen Kuma Imam Hassan (as) Yace: “Ya kai Dan Adam baka gushe ba Kana karar da rayuwarka tun da ka fito daga cikin Mahaifiyarka.”
-Imam Hassan (as) Yace: “Kayi tattalin tafiya zuwa lahira tun gabanin saukar ajalinka.”
-Imam Hassan (AS) Yace: “Ka Sani kana neman duniya kai kuma mutuwa tana Nemanka.”
-Imam Hassan (as) Yace, “Ka Sani duniya halal dinta hisabi ne, haramun dinta ukuba ne.” Wato ranar Alkiyama.
-Imam Hassan (AS) Yace: “Kayi aiki domin duniyar ka Kamar zaka rayu har abada, kayi aiki domin lahirarka Kamar zaka Mutu gobe.
-Yan uwa bari Mu Kammala Wadannan Hadisan da Wasiyyar da Imam Hassan (as) Ya yiwa Imam Husain (as) a ranar sa ta karshe a rayuwar duniya.
-Lokacin da Imam Husain (as) Ya je gaishe da 'Dan uwansa Sai Imam Imam Husain (as) Yace Masa: Ya jiki Ya Kuma Kake ji?
-Sai Imam Hassan (as) Yace Masa, “Ina jin Yauce Ranata ta Karshe a Wannan gida na duniya, Kuma Ranata ta farko a rayuwar lahira, ka Sani ni ba zan wuce ajalina ba.
-Imam Hasan (as) Yace: "Duk da Cewa bana Son Rabuwa da kai da Kuma Sauran ‘Yan uwanka.
-Imam Hasan (as) Yace: "A Yanzu ina gab da haduwa da Kakana Manzon Allah (S) da Mahaifina Amiril Mu'uminin (as) da Kuma Mahaifiyata Fatima, Sa'annan Zan yi Maka Wasiyya dangane da iyalinsa da kuma ‘ya’ya na, in na Rasu a Kayi Min Kabari kusa da na Manzon Allah (S), amma idan Kaga abun zai haifar da Wata Matsala to a barshi, idan mun hadu da Manzon Allah (S) zamu fada Masa dukkan abubuwan da aka yi Mana a bayansa.
-Bayan Imam Hasan (as) Yayi Wafati Haka ko aka Yi domin Sun ki Yarda abinne Shi kusa da Manzon Allah (S), Suka ma Maida abun Kamar Yaki Saboda sun fito da makamai, suka yi ma tsarkakekken gangar jikin Imam Hassan ruwan kibiya.
-Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.
-Yan uwa Barkan Ku da Yammacin Alhamis.
-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985.