Hukuncin Wanda yasha Ruwa Bisa tsammanin Lokaci Ya Yi !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ALLAH BA YA KAMA MUTUM BISA ABINDA YAYI NA RASHIN SANI


Kamar yadda muka sani ne cewa Allah (S.W. T) ya  umarce mu damu cika azumin mu zuwa dare, to,  dole ya kasance mutum ya cika azumin nasa zuwa daren kafin Allah ya karba masa. 


Duk wanda ya aikata wani aiki sabanin yadda Allah ya umarce shi ko kuma sabanin koyarwar Manzon Allah (S. A. W. W), to, wannan aiki nasa bai zai taba zama karbabbe ba.


Sai dai duk da haka akan iya samun kuskure wajen aikata abu bisa tsammanin abin haka yake, sai kuma daga baya ta bayyana cewa an aikata kuskure. To, cikin komai ma hakan kan iya faruwa. 


Ya zo cikin riwaya kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 تفسير العياشي عَنْ سَمَاعَةَ قَالَ: عَلَى الَّذِي أَفْطَرَ الْقَضَاءُ لِأَنَّ اللَّهَ تَعَالَى يَقُولُ‏ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيامَ إِلَى اللَّيْلِ‏ فَمَنْ أَكَلَ قَبْلَ أَنْ يَدْخُلَ اللَّيْلُ فَعَلَيْهِ قَضَاؤُهُ لِأَنَّهُ أَكَلَ مُتَعَمِّداً.


 تفسير العيّاشيّ ج 1 ص 84. و الآية في سورة البقرة: 187.


Daga Tafsirul-Ayashi, daga Sama'ata yace :


 " Akwai ramuwa akan wadanda suka sha, domin Allah (T) na cewa; 


" SA'AN NAN KU CIKA AZUMI ZUWA DARE  ."


" Duk wanda yaci kafin dare ya shiga, to, akwai ramuwarsa a kansa domin shi ya ci ne bisa ganganci. "


NB:- Abin nufi da ganganci anan shine, rashin sanin ilimin hukuncin shan ruwa ko shigar dare. Da ace ya san lokacin shan ruwa sai dare yayi amma yasha ba tare da shigowar daren ba, to, da kaffara ce za ta hau kansa domin ya zama cewa ya saba umarnin Allah ne da gangan. 


Amma da shike gangancin nasa na rashin sanin hukunci ne shi yasa ramuwa kadai zai yi. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


       25TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post