Hukuncin wanda watanni biyu na Azumi suka kubce masa !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


YADDA ZAI RAMA AZUMIN BARA IDAN YA HADU DANA BANA 


Hukunce-hukuncen mas'aloli mabambanta muke son fitar dasu cikin wannan rubutu namu na yau, sai dai akwai buqatar nutsuwa wajen karantawa da kuma gane bambancin mas'alolin da kuma hukuncin nasu.


Sai dai kuma maganar tamu za ta shafi wanda azumi ya kubuce masa ne bisa lalura ba wai bisa ganganci ba, domin wasu kan yi ganganci wajen rama azumin daya kubuce musu bisa lalura. 


Ku biyo mu cikin wannan nassi dake biye insha Allah. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 قرب الإسناد عَلِيٌّ عَنْ أَخِيهِ ع قَالَ: سَأَلْتُهُ عَمَّنْ كَانَ عَلَيْهِ يَوْمَانِ مِنْ شَهْرِ رَمَضَانَ كَيْفَ يَقْضِيهِمَا قَالَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمَا بِيَوْمٍ فَإِنْ كَانَ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ فَلْيَقْضِهَا مُتَوَالِيَةً- وَ سَأَلْتُهُ عَنْ رَجُلٍ تَتَابَعَ عَلَيْهِ رَمَضَانَانِ لَمْ يَصِحَّ فِيهِمَا ثُمَّ صَحَّ بَعْدَ ذَلِكَ كَيْفَ يَصْنَعُ قَالَ يَصُومُ الْأَخِيرَ وَ يَتَصَدَّقُ عَنِ الْأَوَّلِ بِصَدَقَةٍ كُلَّ يَوْمٍ مُدٍّ مِنْ طَعَامٍ لِكُلِّ مِسْكِينٍ وَ سَأَلْتُهُ عَنْ رَجُلٍ مَرِضَ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ فَلَمْ يَزَلْ مَرِيضاً حَتَّى أَدْرَكَهُ شَهْرُ رَمَضَانٍ آخَرَ فَيَبْرَأُ فِيهِ كَيْفَ يَصْنَعُ قَالَ يَصُومُ الَّذِي بَرَأَ فِيهِ وَ يَتَصَدَّقُ عَنِ الْأَوَّلِ كُلَّ يَوْمٍ مُدّاً مِنْ طَعَامٍ‏.


قرب الإسناد: 136


Ya zo cikin QARABUL-ISNAAD, daga Aliyu daga dan'uwansa (A. S) yace : 


" An tambaye shi game da wanda ke da (azumin) kwana biyu na daga watan Ramadana, ta yaya zai rama shi ?" Yace; 


" ZAI RABE TSAKANINSU DA KWANA 'DAYA , IDAN KUMA YA KASANCE SUNFI HAKA YAWA, TO, ZAI RAMA SU A JERE. "


" Sai kuma aka tambaye shi game da wanda Ramadan biyu suka jeru a kansa (yana halin cikin rashin lafiya) bai samu ya warke cikinsu ba, sa'an nan ya warke bayan haka (kafin wani azumin na uku yazo). To, yaya zai yi ?" Yace; 


" ZAI AZUMCI NA QARSHE NE KUMA YAYI SADAQA KAN NA FARKO DA SADAQAR MUDUN ABINCI A KOWACCE RANA GA MISKEENI ."


" Sai kuma aka tambaye shi game da mutumin da yayi rashin lafiya cikin watan Ramadana, bai gushe ba yana cikin rashin lafiyar har sai da wani watan Ramadana ya qara samunsa, sannan ya warke a cikinsa. To, ya zai aikata ?" Yace; 


" ZAI AZUMCI WANDA YA WARKE A CIKINSA KUMA YAYI SADAQA AKAN NA FARKO, KOWACCE RANA MUDU NA ABINCI ."


(QARABUL-ISNAAD, SH:136)


NB:- Dukka biyun hukuncinsu iri daya ne, bambancinsu kawai shine, na farko azumin shekaru biyu ne suka jeru a kansa bai samu ya rama ba. Na biyun kuma azumi daya (1) ake binsa wanda yazo ya hadu dana lokacin.


Amma da zai kasance ana binsa bashin azumi sai yaqi ramawa da gangan ba bisa wata lalura ba har wani watan Ramadana ya qara zagayowa ya same shi, to, anan zai ciyar sannan kuma ya rama daga baya. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


      21ST APRIL, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post