Hijabi a Muslumci Kashi na Huɗu (IV)


 

MENENE DALILIN SAUKAR AYAR SANYA HIJABI, DA KUMA ILLAR RASHIN SANYA SHI?


AMSA: 

1=Dalilin saukar wannan Ayar ta cikin SURATUN-NUR Aya ta 30 zuwa Aya ta 31, shi ne:


 عن الإمام الباقر(ع) قال: استقبل شاب من الأنصار أمرأة بالمدينة وكان النساء يقنعن خلف آذانهن، فنظر إليها وهي مقبلة، فلمّا جازت نظر إليها ودخل زقاق قد سمّاه يعني فلان، فجعل ينظر خلفها واعترض وجهه عظم في الحائط أو زجاجة فشقّ وجهه، فلمّا مضت المرأة نظر فإذا الدماء تسيل على ثوبه وصدره، فقال: والله لاتين رسول الله(ص) ولأخبرنّه، قال: فآتاه فلمّا رآه رسول الله(ص) قال له: ما هذا فأخبره، مهبط جبرئيل(ع) بهذه الآية: 


Yazo a cikin Littafin SHEIKH KHULAINI (KHAFI) daga Imam Baqeer (as) yace:


WANI MATASHI DAGA ANSAR WATO MUTUMIN MADINA YA HADU DA WATA MACE A GARIN MADINA, A LOKACIN MATA SUNA SANYA DAN KWALINSU A BAYAN KUNNUWANSU, DA WANNAN MATASHIN YAGA WANNAN MATAR TA TAHO SAI YANA KALLONTA HAKA BAYAN TA WUCE YACI GABA DA KALLONTA, SAI YA SHIGA WANI LUNGU YANA KALLONTA TA BAYA, KAWAI SAI YACI KARO DA BANGO WANDA JIKIN BANGON AKWAI KWALBA KO KASHI WANDA YA RAUNATA MASA FUSKARSA JINI YA FARA ZUBA, BAYAN DA MATAR TA WUCE SAI YAGA JINI YANA ZUBA A JIKINSA DA RIGARSA NA WANNAN RAUNINDA YAYI, SAI MATASHIN YACE: WALLAHI ZANJE GURIN MANZON ALLAH (S.W.A) NA GAYA MASA ABINDA YA FARU, SAI MATASHIN YAZO GURIN ANNABI LOKACINDA MANZON ALLAH (S.A.W) YA GANSHI SAI YACE MAI YAFARU DAKAI HAKA?

SAI YA BASHI LABARIN ABINDA YA FARU DASHI, LOKACIN NE JIBRA'IL (AS) YA SAUKAR DA WANNAN AYAR TA CIKIN SURATUN-NOOR SURA 24 AYA TA 30 ZUWA 31



(قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا۟ مِنْ أَبْصَٰرِهِمْ وَيَحْفَظُوا۟ فُرُوجَهُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرٌۢ بِمَا يَصْنَعُونَ(30)


MA'ANA:

KACEWA MUMINAI MAZA SU SAUKAR DA GANINSU, SU KIYAYE AL'AURANSU. WANNAN SHINE MAFI TSARKI A GARE SU. HAKIKA ALLAH, MA SANINE GA ABINDA KUKE AIKATAWA.


Wannan Hadisi yazo ne cikin TAFSIRUL-MIZAN na AYATULLAHI DABA-DABA'I na wannan Aya dake cikin SURATUN-NOOR sura 24 Aya ta 30 zuwa 31 sannan yazo cikin TAFSIRUL-AMSAL na AYATULLAHI MAKAREM, dukkannin SU sun ciro Hadisin ne daga Littafin (KHAFI) na SHEIKH KHULAINI, a karkashin Tafsirul wannan Ayar.


Duk dacewa, mutane zasu so sanin sunan wannan MATASHI ko kuma wannan Mace, amma lallai Hadisin bai fadi sunan MATASHIN ba, sannan ita Macen bai fadi sunan taba, sannan ba wata ruwaya da ta zo da sunansu saidai Hadisin wanda yazo daga Imam Baqeer (as) ya nuna dukkannin SU 'yan MADINA ne.


*ILLAR BAYYANA ZEENA WATO (ADO GA MACE).*


1. Bayyyanar da ZEENA ga Mace sabawa ummarnin Allah ne da yayi ummarni da Mace ta rufe dukkanin jikinta komai-da-komai na ta in banda FUSKA da HANNU matukar ba ADO wanda zai sabbaba jawo hankalin Namiji zuwa gare ta, kamar yadda yazo a cikin Qur'ani mai tarki da Hadisan Annabin Rahama (S.W.A).


2. Bayyanar da ZEENA sabawa ummarnin Annabi ne da A'IMMATUL-ISLAM (as), domin su ne suka nunama yadda Allah yace aboye ZEENA da kuma Illar bayyanata.


3. Bayyanar da ZEENA ga Mace ga wanda bai da ce ba, yana kawo yada FASADI a doran kasa.


4. Bayyanar da ZEENA yana gusar da KUNYA ga Mace.


5. Bayyanar da ZEENA koyi da YAHUDAWA, MASIHAWA, da LARABAWA, kafin zuwan MUSULUNCI, wanda bai dace da girman da MUSULUNCI ya bawa Mace Mumina Musulma ba, a gurguje za mu taka burki anan a takaicen-takaicewa.


2= Yanzu in mukayi la'akari da dalilin saukar da wannan Aya mai mahimmancin gasken-gaske, da kuma wannan Hadisi za muga dalilin saukar Aya shi ne bayyanar ZEENA da wata mace tayi kafin saukar da Ayar Wajabta sanya Hijabi a garin MADINA har ya jawo hankalin wani MATASHI gare ta garin kallonta har yaje yaji ciwo, dalilin wannan nema ALLAH SUBHANAHU WATA ALLAH ya saukar da wannan Aya, kuma an saukar da wannan Aya ne a garin MADINA munyi bayani a baya cewa, dama can Sauran Addinai suna Sanya MAYAFAI kafin zuwan MUSULUNCI irin su addinin Yahudanci, da Masihanci, da kuma Larabawa.


MUSULUNCI ya kammala shi ne ya kuma nuna yadda Allah yakeso a sanya shi, HIJABIN, wannan Hadisi ya nuna ILLAR bayyanar da ZEENA ga Mace wanda bai da ce yagani ba,  

bayyanar da ZEENA zai iya jawoma Mace cutarwa ga mugayan mutane kamar yadda muke gani yanzu yake faruwa a wannan zamanin da muke ciki,

Ita Mace wani girma ne da Allah ya girmamata da shi wanda wannan girman Allah ne kawai ya san irin kimarsa wanda bai kamata wannan girman ta bayyanashi ga kowa-da-kowa ba, sai wanda ya da ce gare ta.


Binya Shi'a Kauran-Wali, Kudan.

9th April, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post