Da misalin karfe 11:15am na safiyar yau Asabar aka fara gudanar da wannan muhimmiyar ibadar. Wacce duk Shekara harisawan sukan gudanar da ita a Zariya.
Sai dai tin bayan waki'ar Zariya ta shekarar 2015 abin ya canja salo. Wanda a Shekarun baya harisawan sukan wuri daya ne su gudanar da wannan faretin a gaban Sheikh Zakzaky (H).
A wannan shekarar kamar yadda shugaban Harisawa Malam Idris Katsina ya bayyana. Cewa, anyi makamacin wannan taron har yankuna guda hudu a cikin kasar nan. Wadanda suka hada da Kano, Birnin Kebbi, Suleja, Bauchi da Kudan. Sai dai duk cikar su sun hada da sauran harisawan sauran yankuna da zone.
Shi dai wannan taro da aka yi a Kano ya faro ne tin daga Junction na Mumbayya House dake takiyar Birnin Kano har zuwa masallacin kofar Fada, duk a cikin Kano. Inda a lokacin wannan Muzaharar an biyo ta wurare daban daban domin isar da sako, Kuma sakon ya isa insha Allah.
Sai dai Bayan Isa Masallacin kofar Fada ke da wuya. Aka gabatar jaddaba mubayi a ga Jagora Sayyid Zakzaky (H). Sannan daga bisani aka Mika abin magana ga shugaban Harisawa na kasa Baki daya Malam Yakubu Idris.
Inda Malamin yayi muhimman Zan tuka tare da nuna cewa har yanzu suna nan. Kuma zasu cigaba da bayar da gudummawa su har sai lokacin da Jagora (H) zai dawo a cikin mu.
Daga bisani Kuma Malam Abdulkadir Gwammaja ya rufe taro da Addu'a aka sallami kowa.
Daga Wakilinmu:
Auwal M Tukur