@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TSAKANIN SARA DA SUKA 90 AKA SAMU A JIKIN JA'AFARU-'DAYYAR
A duk lokacin da Allah ya tayar da wani bawansa wanda zaiyi aiki wajen isar da saqonsa sai kaga nau'in cutarwa kala-kala masu muni kan wannan bawa nasa. Wannan kuwa nada alaqa ne da matsayin wannan mutumi wajen Allah (T).
A tarihin wannan qasa tamu Nigeria tun daga kafuwarta har zuwa yanzu da nake wannan rubutu ba a kawo ko rubuta tarihin wani mutum wanda aka cutar dashi kamar Sayyid Zakzaky (H). Shi wannan mutum kuwa ko a wacce aqida yake ko kan wacce hanya yake ba a kawo cutarwar da akayi masa wacce ta girgiza duniya.
Bayan karkace masa mabiya marar adadi da kuma 'ya'yansa wanda azzalumar gwamnatin Buhari tayi ta zarce kan Sayyid Zakzaky (H) tayi masa ruwan wuta na Bullet wanda Allah ne kadai yasan irin mutum abinda aka yiwa wannan bawa nasa.
Ja'afarud-'Dayyar dan'uwana na jinin wajen Imam Ali (A. S) wanda ya kasance jagora cikin rundunar da Annabi (S. A. W. W) ya tura su Habasha wajen gudun Hijra. Sannan kuma yana cikin wadanda aka tura yaqin Mu'uta qarqashin jagorancin Zaid mahaifin Usamata Bn Zaid (R. A).
An samo hadisi daga Abdullahi Bn Umar yake cewa;
يقول عبدالله بن عمر: " كنت مع جعفر في غزوة مؤتة، فالتمسناه، فوجدناه وبه بضع وتسعون ما بين رمية وطعنة"..!
" NA KASANCE TARE DA ZAID A YAQIN MU'UTA , MUKA BINCIKO SU (cikin wadanda aka kashe) SAI MUKA SAME SHI AYI MASA SARA DA SUKA 90 A JIKINSA ."
(HAYATUS-SAHABA)
To, anan idan muka kwatanta abinda aka yiwa wannan Sahabi da kuma abinda aka yiwa Sayyid (H) za muga bambancin kawai shine, shi Ja'afar (A. S) ya riqa yayi shahada, shi kuma Sayyid Zakzaky (H) shahidi ne mai rai.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th April, 2021/ 22nd Sha'aban, 1442.