@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @
YADDA AKE YAQAR MAULIDIN ANNABI (S. A. W. W) CIKIN HIKIMA
Shi maqiyin Annabi (S. A. W. W) tamkar Shaidan yake, domin yakan iya fito maka ta baya gare ka ko ta gaba ko kuma ma ta inda ba ka tsammani.
Hikima ce ta yaqar Maulidin Manzon Allah (S. A. W. W) wacce idan mutum bai yi taka-tsantsan ba sai ya fada cikin wannan tarko ta yadda ba zai iya fitar da kansa ba .
Abinda za kaji suna cewa shine;
" GASKIYA YAHUDAWA SUNYI NASARA WAJEN CUSAWA MUTANE MUMMUNIYAR AQIDA CIKIN MUSLIMCI, DOMIN ZA KAGA MUTUM MUSULMI NE AMMA WAI YA KEBE WATA RANA TA MUSAMMAN DON TUNAWA DA RANAR HAIHUWARSA, KUMA KAGA YA KASHE KUDADE MASU YAWA KAN HAKA.
YANZU DA ACE MUTUM YA KASHE WADANNAN KUDADE NASA WAJEN TAIMAKON ADDINI NE AI DA HAKAN YA FI MASA ALKHAIRI, DOMIN WANNAN 'DABI'A CE TA YAHUDAWA WACCE SUKA QIRQIROTA. "
Har ma kaji suna qarawa da cewa;
" AI KOWA YASAN CEWA ANNABI BAIYI BA KUMA SAHABBANSA MA BA SUYI BA , KUMA ANNABIN YACE AYI KOYI DA SUNNARSA DA KUMA SUNNAR KHALIFOFINSA SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA. TO, GA SHI SAHABBAI BA SUYI Birthday NASU BA, IDAN MU YANZU MUKA ZO MUNA BIRTHDAY 🎊 NAMU, TO, DAWA MUKE KOYI KENAN ?"
A wannan guri wata guba (poison) ce wacce ake son a cusa maka har ka gamsu cewa eh Sahabbai fa ba suyi (birthday) nasu ba don kuwa ba a gani cikin tarihi ba, wanda hakan ke nuna cewa ba muslimci bane. Saboda haka idan aka iya gamsar dakai kan haka har ka yarda, to, abinda zai biyu baya shine su nuna maka cewa tunda hakane ba ka da wani hurumi cikin muslimci wanda ya bada damar kayi Birthday naka ko na wani.
A qarshe kuma sai ka zama fanko marar amfani wanda bai san inda ya dosa cikin addininsa ba, domin kana iqirari kai masoyin Manzon Allah (S. A. W. W) har ma kana yin Maulidinsa (Birthday), amma yanzu an cusa maka guba wacce ta rusa wannan fahinta ko aqida taka ta yin Maulidinsa (S. A. W. W).
Saboda wallahi duk wanda kaji yana sukar (Birthday) da mutane ke yi idan ranar haihuwarsu tazo, to, target nasu shine su soki Maulidin Manzon Allah (S. A. W. W) da cewa koyi ne da Yahudawa.
Sai dai kuma da shike qwaqwalwar Kifi 🐠 ce dasu sun kasa gane cewa a addini ana iya yin koyi da Yahudu cikin wani aiki wanda bai ci karo da muslimci.
Misalin daya (1) da zan basu shine, yana daga cikin aqidarsu cewa Azumin Ashura muslimci ne, amma sun manta cewa da bakinsu suka ce wai lokacin da Annabi (S. A. W. W) yayi Hijra daga Makkah zuwa Madinah ya tarar da Yahudawa suna yin azumin Ashura. Wai sai ya tambaye su cewa wannan azumi da suke yi na menene? Wai sai suka ce masa ai rana ce mai girma, domin a cikinta ne aka tseratar da Annabi Nuhu daga ruwan 'Dufana, kuma aka tseratar da Annabi Musa (A. S) daga sharrin Fir'auna. Kuma ma Annabi Musa (A. S) ya azumceta.
Wai sai Annabi (S. A. W. W) yace ai su suka fi cancanta da Musa (A. S), saboda haka idan shekara ta juyo za su azimci wannan rana.
(SAHIHUL-BUKHARI)
Idan wannan magana gaskiya ce sai muce ashe shi ma Annabin na koyi da Yahudawan kenan, kuma bai kamata idan kaga wani na koyi da abinda Yahudawa ke yi kace ba addini bane.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
27th April, 2021, 15th Ramadan, 1442.