@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BABBAN MAQIYI GA MUTUM SHINE JAHILCI
Hankali ya kasance babban ma'auni wanda ake amfani dashi wajen auna abubuwa da dama. Da shi ne ake iya tantance kyakkyawa da mummuna, abinda ya dace da abinda bai dace ba.
Hankali ya zama abinda Allah (T) ke amfani dashi wajen hukunta bayinsa, duk wanda ya kasance ba shi da hankali Allah kan dauke alqalaminsa a kansa, saboda haka za zaiyi hukunci a kansu ba har sai su san abinda suke yi.
Imam Ridha (A. S),
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
قَالَ الرِّضَا (ع): " صَدِيقُ كُلِّ امْرِئٍ عَقْلُهُ وَ عَدُوُّهُ جَهْلُهُ ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 88
" ABOKIN KOWANNE MUTUM SHINE HANKALINSA , MAQIYINSA KUWA SHINE JAHILCINSA ."
Shi kuwa jahilci a duk inda ka ji an ambace shi to, sharri ne ko fitina ko dai makamancin haka ga ma'abocinsa, saboda haka ba zai taba kai ma'abocin nasa zuwa ga alkhairi ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
3rd April, 2011, 21st Sha'aban, 1442.