Haihuwar Imam Hassan: Ranar farko da Allah (T) ya albarkaci Manzon Allah (S.A.W.W) da Jika


  

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


RANAR FARKO DA ALLAH (T) YA BAWA MANZONSA (S. A. W. W) JIKA (grandson) 


Dole ya zama ranar farin cikin ga dukkan muminai don taya Manzon Allah (S. A. W. W) samun jika na farko a doron qasa. Na san wasu za suyi baqin ciki kan wannan murnar da kuke nunawa, domin su kansu suna baqin cikin murnar da muke yi ta haihuwar Manzon Allah (S. A. W. W), saboda haka su ba za suyi murna da wannan ranar ba.


15 ga watan Ramadan, shekara 3 bayan Hijrar Annabi (S. A. W. W) shine yazo daidai da ranar haihuwar Imam Hassan Mujtaba (A. S). 


MAHAIFINSA :- Mahaifinsa shine Imam Aliyu Bn Abiy 'Dalib Bn Abdul-Mudallib (A. S). 


MAHAIFIYARSA :- Mahaifiyarsa kuwa ita ce Sayyidah Fatimah (S. A) 'yar Manzon Allah Muhammad (S. A. W. W) Bn Abdullahi Bn Abdul-Mudallib (A. S). 



Game da haihuwarsa (A. S) an sami riwaya kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 الإرشاد كُنْيَةُ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ صَلَوَاتُ اللَّهِ عَلَيْهِمَا أَبُو مُحَمَّدٍ وُلِدَ بِالْمَدِينَةِ لَيْلَةَ النِّصْفِ مِنْ شَهْرِ رَمَضَانَ سَنَةَ ثَلَاثٍ مِنَ الْهِجْرَةِ وَ جَاءَتْ بِهِ أُمُّهُ فَاطِمَةُ ع إِلَى النَّبِيِّ ص يَوْمَ السَّابِعِ مِنْ مَوْلِدِهِ فِي خِرْقَةٍ مِنْ حَرِيرِ الْجَنَّةِ كَانَ جَبْرَئِيلُ ع نَزَلَ بِهَا إِلَى النَّبِيِّ ص فَسَمَّاهُ حَسَناً وَ عَقَّ عَنْهُ كَبْش


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 252


Ya zo cikin Irshad cewa ana yin Al-Kunya ga Hassan Bn Aliyu (A. S) da Abu Muhammad, an haife shi ne a Madinah cikin daren rabi (Nisfu) daga watan Ramadan, a shekara ta uku (3) bayan Hijra. Sai mahaifiyarsa Fadimatu (S. A) tazo dashi zuwa ga Annabi (S. A. W. W) ranar bakwai daga haihuwar tasa cikin wani qyale na Al-Harinin Aljannah wanda Jibrilu (A. S) ya sauko mata dashi zuwa ga Annabi (S. A. W. W), sai ya sanya masa suna Hassan kuma ya yanka masa Rago. "


Wannan riwaya na tabbatar mana ne cewa ranar 15 ga Ramadan shekara ta 3 bayan Hijra aka haifi Imam Hassan (A. S), kuma Manzon Allah (S. A. W. W) ne da kansa ya rada masa wannan suna mai kyau da dadin ambato. 


An qara kawo wata riwaya kuma kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 المناقب لابن شهرآشوب ابْنُ بَطَّةَ فِي الْإِبَانَةِ مِنْ أَرْبَعِ طُرُقٍ مِنْهَا أَبُو الْخَلِيلِ عَنْ سَلْمَانَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ سَمَّى هَارُونُ ابْنَيْهِ شبرا [شَبَّرَ] وَ شَبِيراً وَ إِنِّي سَمَّيْتُ ابْنَيَّ الْحَسَنَ وَ الْحُسَيْنَ.



مُسْنَدُ أَحْمَدَ وَ تَارِيخُ الْبَلَاذُرِيِّ وَ كُتُبُ الشِّيعَةِ أَنَّهُ قَالَ: إِنَّمَا سَمَّيْتُهُمْ بِأَسْمَاءِ أَوْلَادِ هَارُونَ شبرا [شَبَّرَ] وَ شَبِيراً وَ مُشَبِّراً.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 253


Ya zo cikin Manaqib na Ibn Shahr-Ashwab, Ibn Baddata kuma ya kawo cikin Ibaanati ta hanyoyi har guda hudu (4), daga cikinsu akwai Abul-Khaleel, daga Salmanu cewa, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" HARUNA YA AMBACI SUNAYEN 'YA'YANSA DA SHABBAR DA SHABEERAN, NI KUMA ZAN AMBACI 'YA'YANA DA HASSAN DA HUSSAINI. "


Cikin Musnad na Ahmad da Tarikh na Balazuriy, da littattafan 'yan Shi'ah an kawo cewa yace; 


" LALLE NI ZAN AMBACE SU DA SUNAYEN 'YA'YAN HARUNA, SHABEERAN DA MUSHABBIRAN. "


Cikin wannan riwaya za mu fahinci abubuwa kamar haka :-


(1)- Imam Ali (A. S) wajen Annabi (S. A. W. W) tamkar Annabi Haruna (A. S) ne wajen Annabi Musa (A. S). 


(2)- Yadda Annabi Haruna (A. S) ya sami 'ya'ya maza guda biyu ya sanya musu suna Shabeeran da Mushabbiran, haka ma Allah ya bawa Imam Ali (A. S) 'ya'ya maza guda biyu wadanda Annabi (S. A. W. W) ya sanya musu suna irin sunayen 'ya'yan Annabi Haruna (A. S). 


Sannan kuma idan baku manta ba za ku ga cewa cikin sunayen da Annabi Adam (A. S) da Hawwa'u suka riqa wajen neman gafarar Ubangijinsu kan cin 'ya'yan Bishiyar nan wacce aka hane su ci akwai SHABEERAN da SHABBAR, wato Hassan da Husaini (A. S). 


Imam Hassan (A. S) ya rayu ne shi da dan'uwansa Imam Hussaini (A. S) qarqashin tarbiyyar Manzon Allah (S. A) har yabar duniya. 


Imam Hassan (A. S) na cikin wadanda Annabi (S. A. W. W) ya kawo cikin shugabanni a bayansa, kuma alqawari ne na Allah cewa zai yi amfani dashi wajen sulhunta tsakanin runduna biyu ta musulmi. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


(2704)-.... فقال الحسن: ولقد سمعت أبا بكرة يقول: رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم على المنبر، والحسن بن علي إلى جنبه، وهو يقبل على الناس مرة وعليه أخرى، ويقول: (إن ابني هذا سيد، ولعل الله أن يصلح به بين فئتين عظيمتين من المسلمين) 


Bukhari ya riwaito cikin Sahihinsa kamar haka; 


" ......Sai Hassan yace: " Haqiqa na ji Abubakar yana cewa; " Naga Manzon Allah (S. A. W. W) akan Mimbari kuma Hassan Bn Aliyu na gefensa, shi kuma (Manzon Allah) na kallon mutane, wani lokaci kuma ya kalle shi (Hassan) yana cewa; 


" LALLE WANNAN 'DAN NAWA SHUGABA NE, KUMA DA SANNU ALLAH ZAI SULHUNTA DASHI TSAKANIN MANYAN RUNDUNA BIYU TA MUSULMI. "


(Bukhari, hadisi mai lamba 2704)


Wannan kuwa shi ke tabbatar mana da cewa matakin Da Imam Hassan (A. S) ya dauka na sulhu tsakaninsa da Mu'awiyyah (L. A) cika umarnin Allah ne na samar da wata maslaha wacce Shi (Allah) kadai yasan hikimarSa da manugarSa.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda. 


      (08137925034)


27TH APRIL, 2021, 15TH RAMADAN, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post