... Umar Hassan Gololo...
Kowa ka gani neman yardar Allahu Ta'ala yake yi, kuma kowa da hanyar da yake ganin ita zai iya yi domin shima ya samu damar damawa a wannan harkar saboda kada ya zama dan kallo ko dan zaman jagwam.
Idan ka ga ana ta'alim mutum daya yana karantawa wasu suna saurara zaka samu kafin a fara wasu sun yi wani abu domin ganin ta'alim din ya gudana, hakanan post khutba da pre khutba.
Idan ka ga ana Muzahara ka san adadin Mutanen da suka yi yunkurin ganin ta tabbata Muzahara ta hanyar bin tsari, wurin da za a tashi a kuma rufe.?
Ka duba yadda ake gudanar da karatun Fudiyyah ta yara, manya da sistoci, Mutane nawa ne suka tsayu da karatun da kuma ganin karatun ya dore ya kuma inganta.?
Shin kowane dan-uwa ne Malamin addini ko na zamani.?
Kowane dan-uwa ne dan jarida ko lawya.?
Da'awar Malam Zakzaky(H) kamar daukar jinka ne, idan wancan ya Kama, waccar ta kama, wadannan suka kama, wadancan suka kama sai ka ga mun yi abinmu cikin lokaci kuma cikin farin ciki da kaunar juna har da raha da barkwanci.
Malam Zakzaky(H) yace ba a rabuwa da matsala a tafiya ta jama'a sai dai a koyi tafiya da matsala har lokacin da za a cimma manufa.
Kai dai kada ka yarda ka dauka cewa kai kadai ka iya kowa bai iya ba.
Ya Ubangijin Musa da Haruna kamar yadda muke murnar cikar Malam Zakzaky(H) shekaru saba'in da haihuwa ka faranta mana rayuka da fitowarsa alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa Sallam....