Farkon wanda ya soma canza Khudubar Juma'a !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @



Cikin wani rubutunmu na can baya wanda muka ce an canza komai na muslimci har muke bada misali da sallah da azumi da kuma Khudubar juma'ah. Muka ce a zamanin Manzon Allah (S. A. W. W) ana yin Khudubar juma'ah ce bayan sallah, amma sai aka canza ta daga muhallinta zuwa bin son zuciya.


Kuma muka ce hakan ya faru ne sakamakon tsinewa Imam Ali (A. S) cikin Khuduba, sai ya zama mutane ba sa tsayawa don kada suji. Saboda haka sai aka canza ta ta dawo kafin sallah don a sami damar cigaba da tsine masa ko da kuwa mutane ba sa so. 


Akan haka sai wasu mutane suka yi mana caaaaaa wai mu kawo wanda ya canza. 


Ganin ba wai lalle sai mun kawo sunan wanda ya fara din ne sannan maganar ta zama gaskiya ba sai muka kau da kai, amma yanzu ga shi nan cikin Tirmidhi da iznin Allah. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


حدثنا بندار حدثنا عبد الرحمن بن مهدي حدثنا سفيان عن قيس بن مسلم عن طارق بن شهاب قال أول من قدم الخطبة قبل الصلاة مروان فقام رجل فقال لمروان خالفت السنة فقال يا فلان ترك ما هنالك فقال أبو سعيد أما هذا فقد قضى ما عليه سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول من رأى منكرا فلينكره بيده ومن لم يستطع فبلسانه ومن لم يستطع فبقلبه وذلك أضعف الإيمان قال أبو عيسى هذا حديث حسن صحيح


Bundar ya bamu labari, Abdurrahman Bn Mahdi ya bamu labari, Safyanu ya bamu labari daga Qais Bn Muslim, daga 'Dariqu Bn Shihaab yace; 


" Farkon wanda ya fara yin Khuduba kafin sallah shine Marwan. Sai wani mutum ya miqe ya cewa Marwan,  


" KA SABAWA SUNNAH ! "

Sai (Marwan) yace, " Yaa kai wane ! Kai dai kawai ka bar wannan abu (don ni nasan dalilin barin sunnar da nayi !"


Sai Abu Sa'eed yace, 


" AMMA WANNAN YA SAUKE (haqqin) ABIN KE KANSA (na fadar gaskiya). NA JI MANZON ALLAH (S. A. W. W) YANA CEWA; 


" DUK WANDA YAGA WANI ABIN QI DAGA CIKINKU, TO, YA CANZA SHI DA HANNUNSA. WANDA KUMA BA ZAI IYA BA, TO, DA HARSHENSA, WANDA KUMA BA ZAI IYA (da harshen nasa) BA, TO, YA QI A ZUCIYARSA. SAI DAI HAKAN SHINE MAFI RAUNIN IMANI. "


Abu Isah (Al-Tirmidhi) yace wannan hadisi mai kyau ne kuma ingantacce. 


(JAMI'US-SAHIH LI TIRMIDHI, BABIN CANZA MUMMUNAN AIKI DA HANNU KO DA BAKI)


Sai kuma ya kasance sauran al'umma sun zabi subi abinda wani yazo dashi wanda ya canza abinda Annabi (S. A. W. W) yazo mana dashi. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


      (08137925034)


30th April, 2021/ 18th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post