Falalolin Khalifa Umar Bn Khaddab guda uku (3) waɗanda yake fahari da su !!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DUK WANDA YA SAME SU YA CANCANTA DA ZAMA ANNABI 


Kowanne mutum a rayuwarsa yana son yayi wani abu na alkhairi wanda zai sami lada wajen Ubangiji, kuma zai zama abin daukaka gare shi cikin al'ummar da yake raye cikinsu dama wadanda za su zo a bayansa. 


Kowanne Sahabi daga cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) yana da wasu abubuwan da ya kebanta dasu (khaasatan) wadanda ke daukaka darajarsa ko kuma dai akasin haka.


A yau muna dauke ne da wasu falaloli guda uku (3) na Ibn Khaddab wadanda yake alfahi dasu, kuma za mu kawo muku su don fito da darusan dake cikinsu.


Ku shiga cikin wannan hadisi dake tafe ba tare da bata lokaci ba. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



155- حَدَّثَنَا هُشَيْمٌ ، أَنْبَأَنَا حُمَيْدٌ ، عَنْ أَنَسٍ ، قَالَ : قَالَ عُمَرُ : وَافَقْتُ رَبِّي فِي ثَلَاثٍ ، قُلْتُ : " يَا رَسُولَ اللَّهِ ، لَوْ اتَّخَذْنَا مِنْ مَقَامِ إِبْرَاهِيمَ مُصَلًّى ؟ فَنَزَلَتْ : وَاتَّخِذُوا مِنْ مَقَامِ إِبْرَاهِيمَ مُصَلًّى سورة البقرة آية 125 ، وَقُلْتُ : يَا رَسُولَ اللَّهِ ، إِنَّ نِسَاءَكَ يَدْخُلُ عَلَيْهِنَّ الْبَرُّ وَالْفَاجِرُ ، فَلَوْ أَمَرْتَهُنَّ أَنْ يَحْتَجِبْنَ ؟ فَنَزَلَتْ آيَةُ الْحِجَابِ ، وَاجْتَمَعَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نِسَاؤُهُ فِي الْغَيْرَةِ ، فَقُلْتُ لَهُنَّ : عَسَى رَبُّهُ إِنْ طَلَّقَكُنَّ أَنْ يُبْدِلَهُ أَزْوَاجًا خَيْرًا مِنْكُنَّ سورة التحريم آية 5 ، قَالَ : فَنَزَلَتْ كَذَلِكَ."


Hushaim ya bamu labari, Humaid ya bamu labari daga Anas yace; Umar yace; 


(1)- " Ubangijina ya datar dani cikin abubuwa uku, nace yaa Ma'aikin Allah ! Ina ma ace mu riqi maqama Ibrahim ya zama gurin sallah ?" Sai aka saukar da,


" KUMA KU RIQI MAQAMA IBRAHIM YA ZAMA GURIN SALLAH (Baqara, aya ta 125) ."


(2)- " Kuma nace; Yaa Ma'aikin Allah ! Lalle matanka fa mutanen kirki da mutanen banza na shiga gare su (kai kuma kana kallo baka dau mataki ba), me zai hana ka umarce su dasu riqa sanya Hijabi ? Daga nan sai (Allah) ya saukar da ayar Hijabi (matan Annabi suka soma sanyawa idan mutane na shiga gidansa). "


 (3)- " Matan Annabi (S. A. W. W) sun taru a kansa saboda suna yi masa rashin mutunci. Sai nace musu:


" AKWAI TSAMMANIN IDAN YA SAKE KU (saboda rashin mutuncinku) UBANGIJINSA YA CANZA MASA WASU MATA WADANDA SUKA FI KU ALKHAIRI. " (Suratul-Tahrim, aya ta 5).


 Yace, sai ta sauka. "


(MUSNAD-AHMAD, KITABUN FADHA'ILUS-SAHABA, BABIN FALALOLIN UMAR, HADISI MAI LAMBA 155)


                DARASI 


(1)- Umar ne yaga ya dace ace su koma cikin Ka'aba su riqa yin sallah a ciki bayan shekaru bakwai da Annabi (S. A. W. W) ya share suna sallah su uku, Shi da Khadijah da Ali yayin da Umar din ma bai san muslimci ba. 


(2)- Allah ya yiwa Umar tunani na sanin mutuntakar dan Adam dama mata baki daya har shi yana tsare matansa daga ganin mazajen wasu, amma Allah bai qaddara Annabi na da irin wannan tunani ba.


(3)- Allah ma bai san daidai ba har sai Umar ya sanar da Shi, kuma abinda Umar ya hango daidai shi Allah ke koyi. 


(4)- Ashe matan Annabi (S. A. W. W) ba mutanen kirki bane tunda sun iya cin mutumcinsa ba tare da ganin matsayinsa ba. 


(5)- Annabi (S. A. W. W) ya riqa zaman haquri ne da matansa amma ba don biyayyarsu gare shi ba, kuma akwai buqatar muma mu zama masu koyi dashi wajen haqurin zamantakewarmu da namu matan komai munin halinsu. 


(6)- Umar ne yafi cancanta da zama Annabi tunda shi yafi kowa sanin tarbiyyar muslimci.


Wadannan kadan ne daga cikin darusan, don nasan wani zai fini fito dasu don sanin matsayin wannan Sahabi cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W). 


FALALAR UMAR BN KHADDAB KAN DALILIN SAUKAR AYOYI !!!


DASHI ALLAH KE KOYI WAJEN SAUKAR DA HUKUNCI


Wanda Allah ya bawa irin wadannan matsayi ba zai taba yiwuwa ace an sami wanda ya fi shi matsayi ba sai dai in shi Annabi ne. Amma dai ban san dalilin da yasa ake cewa Abubakar ya fi shi girman matsayi, alhali ko sau daya ba a kawo gurin da ke nuna cewa ta dalilin maganarsa an sami ayoyin da aka saukar ba. 


Ga dai irin ayoyin da aka saukar ta dalilin addu'o'insa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


368- حَدَّثَنَا خَلَفُ بْنُ الْوَلِيدِ ، حَدَّثَنَا إِسْرَائِيلُ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ أَبِي مَيْسَرَةَ ، عَنْ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ ، قَالَ : " لَمَّا نَزَلَ تَحْرِيمُ الْخَمْرِ ، قَالَ : اللَّهُمَّ بَيِّنْ لَنَا فِي الْخَمْرِ بَيَانًا شَافِيًا ، فَنَزَلَتْ هَذِهِ الْآيَةُ الَّتِي فِي سُورَةِ الْبَقَرَةِ : يَسْأَلُونَكَ عَنِ الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ قُلْ فِيهِمَا إِثْمٌ كَبِيرٌ سورة البقرة آية 219 ، قَالَ : فَدُعِيَ عُمَرُ ، فَقُرِئَتْ عَلَيْهِ ، فَقَالَ : اللَّهُمَّ بَيِّنْ لَنَا فِي الْخَمْرِ بَيَانًا شَافِيًا ، فَنَزَلَتْ الْآيَةُ الَّتِي فِي سُورَةِ النِّسَاءِ : يَأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَقْرَبُوا الصَّلاةَ وَأَنْتُمْ سُكَارَى سورة النساء آية 43 ، فَكَانَ مُنَادِي رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا أَقَامَ الصَّلَاةَ نَادَى : أَنْ لَا يَقْرَبَنَّ الصَّلَاةَ سَكْرَانُ ، فَدُعِيَ عُمَرُ ، فَقُرِئَتْ عَلَيْهِ ، فَقَالَ : اللَّهُمَّ بَيِّنْ لَنَا فِي الْخَمْرِ بَيَانًا شَافِيًا ، فَنَزَلَتْ الْآيَةُ الَّتِي فِي الْمَائِدَةِ ، فَدُعِيَ عُمَرُ ، فَقُرِئَتْ عَلَيْهِ ، فَلَمَّا بَلَغَ : فَهَلْ أَنْتُمْ مُنْتَهُونَ سورة المائدة آية 91 قَالَ : فَقَالَ عُمَرُ : انْتَهَيْنَا ، انْتَهَيْنَا " .



Halafu Bn Waleed ya bamu labari, Isra'ila ya bamu labari daga baban Ishaq, daga baban Maisarata, daga Umar Bn Khaddab, yace:


" Yayin da aka saukar da haramcin Giya, yace; 


" YAA ALLAH KA BAYYANAR MANA GAMSASSEN BAYANI GAME DA HUKUNCIN GIYA , SAI AKA SAUKAR DA WANNAN AYA DAKE CIKIN SURATUL-BAQARATI; 


" SUNA TAMBAYARKA GAME DA (hukunci) CIKIN GIYA DA CACA, KACE, " CIKINSU AKWAI ZUNUBI MAI GIRMA ." (Baqara, aya ta 219) Yace :


Sai (Annabi) ya kira Umar ya karanta masa (ayar), sai (Umar) yace; 


" Yaa Allah ka bayyanar mana da hukuncin Giya qarara kowa ya fahinta, sai aka saukar da ayar dake cikin Suratul-Nisa'i :


" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KADA KU KUSANCI GIYA ALHALI KUNA CIKIN MAYE. " (Suratun-Nisa'i, aya ta 43)


Sai mai yiwa Manzon Allah (S. A. W. W) yekuwa (who carries the message and deliver it to the people ) ya kasance duk lokacin da za ayi sallah sai yayi kira; " Kada ku kusanci sallah a cikin maye. " 


Sai ya kira Umar ya karanta masa, sai (Umar) yace; 


" YAA ALLAH KA BAYYANAR MANA DA GAMSASSEN HUKUNCI CIKIN GIYA, SAI AKA SAUKAR DA AYAR DAKE CIKIN SURATUL-MA'IDAH. "


Sai (Annabi) ya kira Umar ya karanta masa. Yayin da ya iso kan " SHIN, KO ZA KU HANU ? (Suratul-Ma'idah, aya ta 91) Yace :


Sai Umar yace; " MUN HANU ! MUN HANU !! "


(Musnad Ahmad, Kitabul-Fadha'il, babin falalar Umar, hadisi mai lamba 368)


Wadannan kadan kenan daga cikin irin riwayoyin da ake kawowa cikin falalar Umar. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


           (08137925034)


7th April, 2021/ 25th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post