-Daga Mufaddal ibni Umar Yace "Abu Abdullahi (AS) Yace "Duk Wanda Ya bada Wani labari akan Wani Mumini, da Nufin bata Shi ko Rusa Mutuncinsa, Ko Kuma don Ya Wulakanta Shi a idon Mutane, to Allah Zai Fitar dashi daga Wulayarsa, Yasa Shi Cikin Wulayar Shedan, Kuma Shedan ma ba Zai Karbe Shi ba Saboda Muninsa."
-Daga Abu Abdullahi (AS), Yace "Al'auran Mumini akan Mumini Haramun ne" Imam Yace ba wai wani abu nashi (tsiraicin sa ya bayyana ba, ka gani! A'a! Shine, ka bada labarinshi Wanda zai sa Mutuncinsa ya Zube ko kuma ka aibatashi!
-Don haka ya kai Dan'uwa mai neman tsira! Ka guji bada labari ko Posting a social Media don ka bata Dan'uwanka, ko ka zubar da Mutuncinshi a idon mutane.
-Saboda daga karshe kai ne zaka fadi babu nauyi, mutuncin ka zai zube a idon kowa ka fadi kasa warwas.
-Gobe kiyama kuma kasha azaba a wurin Allah.
-Kaga kayi biyu babu, kenan, shi wanda kake masa hassada Allah zai daukakashi ta inda baka yi tsammani ba, kai kuma zaka kaskanta a idon mutane.
-Allah Ya tsare mu fadawa tarkon Shaidan.
-Muhammad Jiddah Nguru.