... Umar Hassan Gololo...
Buhari ne yayi wa Yara da manya maza da mata abinda Geneva Convention yake kira Genocide, ko Massacre ko kuma extra judicial killing, kisan da har Yau Gwamnatin Buhari ta kasa tabbatar da halascinsa.
Babu Wanda ya goyi bayan ta'addancin Zaria, ko ya ji dadin kisan kiyashin da aka yi, ko yayi murna da kisan dabbancin Zaria sai karnukan azzaluman Nigeria da kuma dabbobin da suke ganin babu wani Musulmi idan ba su ba.
Dukkan Mutanen da aka kashe babu Wanda aka kama shi aka kai shi kotu ta yanke masa hukuncin kisa.
Dukkan wadanda aka kashe babu mutum daya da aka same shi da makami irin Wanda Boko-Haram, Barayin shanu, kidnappers da mahara suke rikewa.
Dukkan wadanda aka kashe a Zaria babu wani mutum daya da aka samu da laifin kashe Mutanen gari ko jami'in tsaron Nigeria Soja ko Dansanda.
Shin Buhari Annabi ne ko wani waliyyi da Allahu Ta'ala ya aiko da zai yi ta'addanci kuma mu ce yayi daidai ko kuma mu yi shiru saboda shi dan Arewa ne kuma Musulmi.?
Ba zamu daina cewa kisan kiyashin Zaria dabbanci ne da zalunci ba, hakanan ba zamu daina cewa kisan dabbancin Zaria da Buhari ya bada umurnin yinsa zalunci ne ba, sai dai duk Wanda ya ji haushi ya mana abinda Buratai yayi a zaria.
Muna rokon Allahu Ta'ala ya gaggauta daukar mana fansar zaluncin da Buhari ya mana a Zaria alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa Sallam...