Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa sarkin Lere, ta jahar kaduna Brig. Abubakar Garba Muhammad Rasuwa a safiyar yau asabar !


  A safiyar yau asabar 10 ga watan Afrilu, 2021. Allah (T) ya karbi ran sarkin Lere,  BRIG, Gen. Abubakar Garba Muhammad II (Rtd) Bayan yayi fama da jinya da ta kai har ana shirin kaishi kasar waje duba lafiyarsa.


A safiyar yau din ne dai ayi ta yaɗa jita-jita kan ya mutu, wanda daga baya aka tabbatar da yana numfashi. Wanda zuwa yanzu wakilinmu ya tabbatar mana da Allah ya karbi numfashinsa.


Wannan shine mutuwa ta biyu da akayi a garin Lere wanda ya girgiza wannan yanki.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post