-An samo Hadisi daga Imam Ali (AS) Yace: Manzon Allah (S) Yace: “Mutum Hudu Ni zan cece su gobe Kiyama, (1) Mai girmama zuriyyata, (2) Mai biya masu bukatunsu, (3) Mai kai-koma cikin al’amuransu a lokacin tsananinsu, (4) Mai Son su da zuciyarsa da Kuma harshensa”.
-Imam Sadik (AS) Yace Manzon Allah (S) ya ce; “Wallahi ba zan yi ceto ga duk wanda ya cutar da zuriyya ta ba”. Manzon Allah (S) Yace; “Cetona ya tabbata ga duk Wanda ya taimaki Zuriyyata da hannunsa da harshensa da kuma dukiyarsa”.
-Manzon Allah (S) ya ce; “Ku so Zuriyyata kuma ko l girmamasu”. bayan haka An samo daga Imam Ridha (AS) ya ce; “Dubi zuwa ga zuriyata ibada ce, (shi wanda ya ruwaito wannan Hadisi ya ce wa Imam Ridha (AS) dubi zuwa ga A’imma daga cikin zuriyar ko kuma dubi zuwa ga Zuriyar Annabi?
-Imam Ridha (AS) Yace masa a’a, dubi zuwa ga dukkan zuriyyar Manzon Allah (S) ibada ce, amma matukar su ba su bar tafarkinmu ba. Kuma ba su cakuda da sabo ba.”
-Haka nan idan akayi duba zuwa ga darajoji da kuma matsayi na Sayyida Fatima (AS), za mu ga akwai Hadisai da dama da suka zo a kan haka.
-Manzon Allah (S) ya ce, “Fatima Shugabar mataye ce baki daya.” Sai aka tambaye shi Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta
-Haka nan ya zo cikin littafin Kanzul Ummal da kuma Mizanul i’itidal, daga Manzon Allah (S) ya ce; “Farkon wanda zai soma shiga Aljannah Fatima ce.”
-Haka nan ya zo a kan cewa Fatima (AS) ita ce Shugabar matayen Aljannah. Manzon Allah (S) ya ce, Allah (T) yana fushi da fushin Fatima (AS) yana yarda da yardarta.
-A wani Hadisi kuma Manzon Allah (S) ya ce; “Duk wanda yake son Fatima (AS) hakika yana so na, duk wanda ya fusata ta hakika ya fusata ni.”
-A wani Hadisi kuma, Manzon Allah (S) ya ce; “Da a ce kyau mutum ne, to da Fatima ce.” Da dai sauran Hadisai masu yawa a kan fada’il dinta.
-Kai ko dama a ce babu Hadisai da suke bayani dangane da matsayinta, kasantuwarta ’ya ga Fiyayyen Halitta, mata ga Imam Ali (AS) Uwa ga Imam Hasan da Husain (AS) ya isa ya zame mata babbar daraja da kuma matsayi, ballantana kuma ga ‘nusus’ a kan haka, wato Hadisai da wasu ayoyi.
-Da mutum ya duba da kyau zai ga cewa komai na Sayyida Fatima (AS) tun daga wiladarta zuwa wafatinta ‘SAMAWIY’ ne. Wato ko dai daga sama ya zo, ko aka aiko da shi, ko kuma aka yo wahayinsa.
-Ga misalai; Ya zo a Hadisai cewa ‘Nudfa’ wanda ya kasance sabab na daukar cikin Fatima (AS) ya kasance ne daga ’ya’yan itace da Manzon Allah (S) ya ci a Aljanna,
wadanda suka karbi haihuwarta daga Aljanna suka zo,
-Sune Mahaifiyar Annabi Isa (AS), wato Maryam ’yar Imran, ’yar uwar Annabi Musa (AS), Kulsum, Asiya ’yar Muzahim wadda Fir’auna ya kashe, da kuma Saratu matar Annabi Ibrahim (AS).
-Ga mai bukatar karin bayani ko ganin haka. Ya duba littafin Muntahal Amal juz’i na daya na Shaikh Abbas Alkummy, wato marubucin Littafin Mafatihul Jinan.
-Shi ma wannan suna nata, FATIMA, saukakke ne daga sama, wato an yo wahayi ne a sa mata wannan suna. Haka nan kuma daurin aurenta sai da aka yi a sama, sannan aka yi a kasa Likafaninta daga Aljannah yake. Da dai sauran ababe nata samawiyya.
-Ya ma zo daga Ma’asumai (AS) cewa; “Talauci ba ya shiga gidan da yake akwai mai suna Fatima (AS)”. Akwai Hadisi da ya zo daga Imam Sadik (AS) da ke nuni dangane da girmama sunan, da kuma girmama wadda aka sa wa sunan.
-A takaice dai darajoji da falaloli na Sayyida Fatima (AS) suna da yawan gaske.
-Allah ta'ala ya gaggauta dawo Mana da Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) Cikin izza da koshin lafiya.
#FREE SAYYID ZAKZAKY (H)
Muhammad Jiddah Nguru.