Ashe Sayyid Zakzaky (H) bai rubuta littafi ba ???


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @


DA RUBUTA LITTAFI SHINE ILIMI DA BABU WANDA YA KAI ANNABI (S. A. W. W) RASHIN ILIMI A FAHINTAR SUNNAH


Ba zai taba zama adalci ba gare ka kayi saurin yanke min hukunci ba tare da ka karanta kuma ka nazarci wannan rubutu nawa zuwa qarshensa ba. 


Qur'ani ya tabbatar da muhimmanci rubutu da kuma fa'idarsa ga wanda ya rubuta da kuma wadanda za su biyo bayan wadannan marubuta, domin za su sami ilimin dake tattare cikin wadannan rubutu da aka rubuta kuma aka wallafa. 


Nima kaina mai wannan rubutu ina ganin fa'idodi marar adadi cikin littafan da aka dawwanar dasu har suka zo kanmu muke karantawa kuma muke fahari da abinda muka samu rubuce cikin littafan. 


A'immah (A. S) sunyi rubuce-rubuce masu yawa tare da yin umarnin cewa a rubuta abinda aka sani, domin dukkan abinda aka rubuta ba za a manta shi ba. Har ma wasu masu ilimin zamani sunyi wannan aiki na rubuce-rubuce kan fannoni dabam-dabam na ilimi. 


Imam Khomain (Q. S) yayi nasa rubuce-rubucen, kamar yadda Sheikh Usman Bn Fodiyo yayi nasa har a cikinsu ya ambaci haihuwa da ilimi da kuma bayyanar Sayyid Ibrahim El-Zakzaky (H). Wannan rubutu nasa kuwa ya taimaka mana sosai wajen fahintar wanene Zakzaky da kuma haqqoqinsa wadanda suka hau kan al'ummar musulmi baki daya, har ma kan wadanda ba musulmi ba. 


Ba don irin wadannan rubuce-rubucen ba ma da bamu san haqiqanin wanene Sayyid Zakzaky (H) ba. Idan muka gangaro nan qasa-qasa za mu sami maluma da dama wadanda suka wallafa littattafai har ya zama abin alfahari ga dalibansu. 


Rashin ganin rubuce-rubucen Sayyid (H) na yawo cikin kasuwanni da kuma zaurukan karatu yasa wasu daga cikin masu amsa sunan Shi'ah da wasu masu amsa sunan Sunnah ke cewa wai Sayyid Zakzaky (H) ba shi da ilimi, wannan dalili ya hana shi iya rubuta littafi da hannunsa wanda zasu amfanar da al'umma (in there future). 


To, abinda nake son nusar da mutane shine, rubuta littafi ba shine ilimi ba, sannan rashin rubutawa ba shine rashin ilimi ba. Na'am, yin rubuce-rubuce ko wallafe-wallafe na daga cikin manyan ayyuka wadanda ba kowa ne zai iya yi ba, sai dai rashin yin nasa ba zai taba zama abin zargi ko naqasu ga wasu bayin Allah (Khass) ba.


                 TAMBAYA 


Annabawa da A'immah (A. S) da Mujaddadai sunyi rubuce-rubuce, amma me yasa babu rubuce-rubucen Sayyid (H) masu yawa ?


Neman sanin wannan amsa tamkar Ridda ne da kuma neman cin zarafin Manzon Allah (S. A. W. W), domin ba za ka taba samun amsar wannan tambaya ba har sai ka tuhumi Manzon Allah (S. A. W. W). Sayyid Zakzaky (H) ba Annabi ko Imami bane daga cikin jerin Imamai 12, amma akwai wani al'amari mai girma tare da shi. 


  ABINDA YA HAU KANMU 


Babban abinda ya hau kanmu almajiran Sayyid Zakzaky (H) shine mu kasance masu bibiya tare da taskake dukkan wani abinda muka ji ko muka gani daga Sayyid (H). Mu zama tamkar Sahabban Manzon Allah (S. A. W. W) masu saurare da kunnuwan gaskiya masu taskace zantukansa da ayyukansa (S. A. W. W). 


Allah (T) yana fada dangane da Annabi Isah (A. S) cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ ( ٨٤)


" KUMA YANA SANAR DASHI RUBUTU DA HIKIMA (ilimi) DA ATTAURA DA KUMA LINJILA ."


    (ALI-IMRAAN:48)


Hakan kuwa na tabbatar mana ne da cewa Isah (A. S) ya san karatu da rubutu. 


Idan muka yiwo qasa zuwa kan Manzon Allah (S. A. W. W) za muga inda Allah (T) ke cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ.......


" ...... SUNE WADANDA KE BIN MANZO ANNABI BA'UMMIYE WANDA SUKA SAME SHI RUBUCE TARE DASU CIKIN ATTAURA DA LINJILA. "


       (A'ARAF:157)


Da kuma inda yake cewa; 



1-اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ


" KAYI KARATU DA SUNAN UBANGIJINKA WANDA YA HALICCE KA ."


(SURATUL-ALAQ :1)


To, dangane da haka malaman sunnah sunce wai Annabi bai iya rubutu ba tunda aka kira shi UMMIYYI, sun manta da cewa sun kawo magana dake nuna wasu daga Sahabbansa sun iya rubutu, ko a ina suka koyi wannan rubutu wanda Annabi (S. A. W. W) ya gagara alhali ya girme su kuma ya fi su basira? 


Har ma suke fada dangane da wanna aya ta qarshe cewa wai yayin da Mala'ika yazo masa yace yayi karatu wai sai yace, 


حتى فجأه الحق وهو في غار حراء فجاءه الملك فيه فقال اقرأ قال رسول الله صلى الله عليه وسلم فقلت ما أنا بقارئ 


Har sai da gaskiya tazo masa yana cikin Kogon Hira'a, sai Mala'ika yazo masa a cikinsa, sai yace, " Kayi karatu !" Wai sai Annabi (S. A. W. W) yace; 


" NI BAN IYA KARATU BA ."



   (TAFSIR IBN KATHEER)


Abinda malaman Sunnah ke fada game da wadannan ayoyi shine, wai Annabi (S. A. W. W) bai iya rubutu ba. Wai bai taba yin rubutu da hannunsa ba sai dai yasa Sahabbansa su rubuta abinda yake so su rubuta. 


Mu kuma a aqidarmu shine, Annabi (S. A. W. W) ya iya karatu da rubutu ko da kuwa bai taba rubuta littafi da hannunsa ba. Ambatonsa da cewa bai iya rubutu ba naqastawa ne da kuma fifita Sahabbansa a kansa. 


Za mu iya fahintar cewa Annabi (S. A. W. W) ya iya rubutu a daidai lokacin da Sahabbansa suka yi masa tawaye har yace musu; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(114)-حدثنا يحيى بن سليمان قال: حدثني ابن وهب قال: أخبرني يونس، عن ابن شهاب، عن عبيد الله بن عبد الله، عن ابن عباس قال: 

لما اشتد بالنبي صلى الله عليه وسلم وجعه قال: (اتئوني بكتاب أكتب لكم كتابا لا تضلوا من بعده)


Yahya Bn Sulaiman ya bamu labari yace, Ibn Wahbin ya bani labari yace, Yunusa ya bani labari daga Ibn Shihaab, daga Ubaidullahi Bn Abdullahi, daga Ibn Abbas (R. A) yace; " Yayin da tsananin rashin lafiya ya kama Annabi (S. A. W. W) sai yace; 


" KUZO MIN DA ABIN RUBUTU NA RUBUTA MUKU ABINDA IN KUNYI RIQO DASHI BA ZA KU BATA BA ."


(BUKHARI, KITABUL-ILMI)


Yanzu wanda bai iya rubutu ba zai buqaci a bashi abin rubutu da nufin ya rubuta masu abinda in sunyi riqo dashi ba za su bata ba a bayansa ?


Imam Ali (A. S) ya rubuta Mus-hafi na zantukan Manzon Allah (S. A. W. W), kuma ya rubuta Qur'ani a bayan wafatinsa (S. A. W. W). 


Ga shi kuma dukkan hadisansa ba shi ya rubuta da hannunsa ba, a'a, Sahabbansa ne suka rubuta ba kuma tare da cewa ba zai iya bane. 


Yanzu mai imani zai ce Sahabbai sunfi Annabi (S. A. W. W) ilimi kenan tunda su sun rubuta Qur'ani da hadisai yayin da shi bai rubuta ba ?


Saboda haka mune za mu tashi haiqan mu rubuta tare da taskake dukkan ilimummukan Sayyid (H) na zahiri kamar yadda Imam Ali (A. S) ya rubuta zantukan Annabi (S. A. W. W) kuma ya taskake su. 


Allah yasa an fahinci saqon da nake son isarwa anan. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


4th April, 2021/ 22nd Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post