Ashe ba a wannan zamanin aka fara jayayya tsakanin Malamai kan hukunci ba !!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


TUN ZAMANIN SAHABBAI AKA FARA SAMUN IRIN WANNAN JAYAYYA A TSAKANINSU 


A matakin farko idan kaga ko kaji ana samun wani jayayya kan hukunce-hukuncen da suka shafi muslimci sai abin ya baka mamaki, domin za kaga a tunaninka bai kamata ace an sami irin wannan rigima ba. 


Sabani cikin hukunce-hukuncen addini ba zai auku ba har sai in an sa bin son zuciya cikinsa, domin Annabi (S. A. W. W) bai barmu cikin duhu ba har sai da ya fayyace mana komai. 


A daidai lokacin da naji malamai sunyi caa kan al'amarin Sheikh Abdul-Jabbar sai na tuna yadda suke yin caa kan ilimummukan da Sayyid Zakzaky (H) ke bayyanar dasu. 


Cikin haka sai naci karo da wannan hadisi kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


360- حَدَّثَنَا بَهْزٌ . قَالَ : وَحَدَّثَنَا عَفَّانُ ، قَالَا : حَدَّثَنَا هَمَّامٌ ، حَدَّثَنَا قَتَادَةُ ، عَنْ أَبِي نَضْرَةَ ، قَالَ : قُلْتُ لِجَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ : إِنَّ ابْنَ الزُّبَيْرِ يَنْهَى عَنِ الْمُتْعَةِ ، وَإِنَّ ابْنَ عَبَّاسٍ يَأْمُرُ بِهَا ، قَالَ : فَقَالَ لِي : عَلَى يَدِي جَرَى الْحَدِيثُ ، تَمَتَّعْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ عَفَّانُ : وَمَعَ أَبِي بَكْرٍ ، فَلَمَّا وَلِيَ عُمَرُ ، خَطَبَ النَّاسَ ، فَقَالَ : " إِنَّ الْقُرْآنَ هُوَ الْقُرْآنُ ، وَإِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هُوَ الرَّسُولُ ، وَإِنَّهُمَا كَانَتَا مُتْعَتَانِ عَلَى عَهْدِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : إِحْدَاهُمَا مُتْعَةُ الْحَجِّ ، وَالْأُخْرَى مُتْعَةُ النِّسَاءِ " .


Bahzu ya bamu labari, kuma Affan ya bamu labari, suka ce : Hammad ya bamu labari, Qatadata ya bamu labari daga baban Nadhrata, yace : Na cewa Jabir Bn Abdullahi; 


" Lalle Ibn Zubair yana yin hani game da Mutu'ah, shi kuma Ibn Abbas (R. A) yana yin umarni da ita. " 


Yace, Sai yace min : Bisa yanayi na hadisi wanda ake cewa Jar, 


" MUNYI MUTU'AH TARE DA MANZON ALLAH (S. A. W. W). "


Affan yace, " Tare da Abubakar, amma yayin da Umar ya hau kan karagar mulki sai ya yiwa mutane Khuduba, yace; 


" LALLE QUR'ANI DAI QUR'ANI NE (babu qarya cikinsa), KUMA MANZON ALLAH (S. A. W. W) SHINE MANZO (wanda aikinsa da haninsa da shirunsa shine addini) . KUMA SU SUN KASANCE MUTU'O'I BIYU (ne) A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W.W); 'DAYARSU ITA CE MUTU'AR HAJJI, KUMA 'DAYAR MUTU'AR MATA. "


(MUSNAD AHMAD, KITABUL-FADHA'IL, BABUN MANAQIBU UMAR, HADISI MAI LAMBA 360)


Cikin wannan hadisi za mu fitar da darusa kamar haka:-


(1)- Sabanin abinda Ibn Zubair da Ibn Abbas suka yi akwai bin son zuciya ta bangaren wani. 


(2)- A zamanin Annabi (S. A. W. W) da Abubakar da Umar ana yin Mutu'ar Hajji da Mutu'ar mata, wanda hakan ke nuna mana ashe ba Annabi (S. A. W. W) ne ya haramtasu ba. 


(3)- Umar na nuna mana cewa matsayin Qur'ani da Manzon Allah (S. A. W. W) suna nan kan matsayinsu, sai dai bai zama dole ayi aiki da umarninsu ba.


(4)- Idan kaga dama za ka iya hana abinda ya tabbata daga Allah da Manzonsa (S. A. W. W), kuma ka maida son zuciyarka ya zama shine addini. 


Sannan kuma idan muka koma cikin Bukhari za muga wani hadisi dake cewa;


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(4518) - حدثنا مسدد: حدثنا يحيى، عن عمران أبي بكر: حدثنا أبو رجاء، عن عمران بن حصين رضي الله عنهما قال: 

أنزلت آية المتعة في كتاب الله، ففعلناها مع رسول الله صلى الله عليه وسلم، ولم ينزل قرآن يحرمه، ولم ينه عنها حتى مات، قال رجل برأيه ما شاء."


Musdaad ya bamu labari , Yahya ya bamu labari daga Imrana baban Bukar; baban Rajaa'i ya bamu labari daga Imraana Bn Hussain (R. A) yace; 


" AN SAUKAR DA AYAR MUTU'AH CIKIN LITTAFIN ALLAH, KUMA MUN AIKATA TARE DA MANZON ALLAH (S. A. W. W). QUR'ANI BAI SAUKO DA HARAMCINTA BA, KUMA (Annabi) BAI HANE SHI BA HAR YA RASU, WANI MUTUM NE KAWAI YA FADI ABINDA YAZO DA RA'AYINSA (amma ba haramcin Allah ko na Ma'aikinsa (S. A. W. W) ba). "


(BUKHARI, KITABUL-TAFSIR, HADISI NA 4518)


Anan kuma za mu qara fahintar cewa ashe dai Sahabban na aikata abinda suka so komai cin karonsa da ayar Alqur'ani ko hadisi. 


Saboda haka yanzu don ka sami jayayya tsakanin malamai wanda wasu ke tabbatar da hukuncin Allah dana Ma'aikinsa wasu kuma na qoqarin rusa wannan hukunci ba zai zama abin mamaki ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


7th April, 2021/ 25th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post