An sha a ce mana; bazai yiwu addini ya kafu ba.. — Muji Daga Bakin Sayyid Zakzaky (H)


 

To kuma ina iya cewa, loƙacin kama mu na farko, a kurkukun Sakkwato wani mai tsaron kurkukun ya kalle mu, yayi shiru ya ce "yanzu kai bakayi karatun jami'a ba?" Nace 'eh nayi karatun jami'a' sai ya kaɗa kai yace Wallahi kuna ɓata loƙacin kune akan abinda ba zai taɓa yiwa waba wani kuma an kaimu kotu, ɗan sanda ne yake cewa waɗannan basu san Opportunity Cost' bane irin abinda suke 'Loosing basu san shi bane shiyasa suke wannan! haziƙan yara suna makaranta.


Amma kuma kawai suje suna wai addini! Ba su san Opportunity Cost' bane sai ya dinga faɗin haka, zuwa can saina ce 'Opportunity cost mun sanshi ne yasa kaga muna yin abinda mukeyi' sai na fassara masa ma'anar Opportunity cost nace "Opportunity cost shine in kana da kuɗi, kana da zaɓi tsakanin biyu ko ka sayi wannan, ko ka sayi wannan to in kasayi wannan, kuɗinsa shine ɗayan daba ka sayaba. Sai yayi wuf ya wage baki ashe na sani.


Nace "ta yiwu ka karanta ordinary level Economics ne ko? Sai yace eh! Yanzu nema yake karantawa bai gamaba nace to ni na karanta, na kuma ci na kuma karanta 'Advance leɓel' kuma na ci kuma na karanta a jami'a duk economics na Kuma ci. Sai ya wage baki Hahhh, University economics? Sai nace to ai kaga na san ma'anar Opportunity cost' kenan sai yayi shiru, shock ya samu sai yake cewa wani kaga wannan University yayi fa kuma economics' ( ya karanta), sai wancan ɗin yace ai wannan oga kwata -kwata ne!''


Saboda mun san wannan ne yasa muke abinda muke yi, wato in bakagane ba, Opportunity cost ɗin shine, akwai lahira akwai aljanna to abinda zamu ɗauka anan, madadin lahira shine muka ajiye, don mu ɗauki na lahira to anan ma na san ba zaigabeba, alal aƙalla ba musulmi ne ba shi.


Amma dai ai abin yayi 'shocking ɗinsa. An san ma'anar abinda ake yi, amma ake abinda akeyin. Don da can an ɗauka addini na wanda talauci ya dame shine, ina mutum yazo yana wa'azi sai a aiko masa da sadaka, an ɗauka ɗan allazi - wahidin ne, inka ga mutum yana wa'azi yana neman abashi ɗan abin taɓawa ne, sai ɗan wurgo yana Allah ya saka da alheri, a ɗan samu yan kwabbai.sayyd zakzaky (H) 


Faruq sani Kudan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post