-Manzon Allah (S) yace, “Kashedinku da girman kai, domin Iblis girman kai ya kai shi ga kin yin sujuda ga Adam.”
-An ruwaito hadisi daga Imam Ali (AS) yace, “Ku lura da karshen Iblis, ya bata ayyukansa da yayi tsawon lokaci sakamakon girman kan da yayi a lokaci guda.”
-An ruwaito daga Imam Sadik (AS) yace, “Ba zai shiga Aljanna ba wanda a cikin zuciyarsa akwai kwayar zarra na girman kai.”
-Haka kuma a wani hadisi da aka samo daga Imam Bakir (AS) yace, “Girman kai komin kankantarsa ba zai shiga zuciyar mutum ba face sai ya samu raguwar hankalinsa dai dai gwargwadon abin da ya shiga.”
-Manzon Allah (S) yace, “ Wadanda nafi ki daga cikin ku, kuma suka fi nesa da ni ranar kiyama sune masu girman kai.”
-A wani hadisi kuma yace, “Duk wanda ya kasance mai girman kai to zai hadu da Allah yana mai fushi da shi.”
-Imam Ali (AS) yace, “Ina mamakin Dan Adam farkonsa digon maniyyi, karshensa mushe, tsakiyarsu kuma yana dauke da najasa amma kuma yana girman kai.”
-Manzon Allah (S) yace, “Mafi kin mutane shine mai girman kai.”
-Imam Ali (AS) yace, “Duk wanda ya yi girman kai ga mutane to sai ya kaskanta.”
-Muhammad Jiddah Nguru.