@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KUNGA AYAR DA ALLAH YA AIKOWA AL'UMMAR AFRICA
Yana daga cikin al'ada ko nace dabi'un al'ummun farko qaryata gaskiya da yin jayayya da ita tare da daukar batattu a matsayin shiryayyu.
A duk lokacin da Allah ya aiko musu da Manzo sai sun qaryata shi tare da neman wannan Annabin nasu ya kawo musu wata aya daga Allah. Sai kuma ya kasance ko da ace an aiko musu da ayar basa yin imani da ita. Wannan dalili yasa a duk lokacin da suka nemi zuwan wata aya, sai kuma tazo musu, to, abinda ke biyo bayanta shine bala'i da musiba.
Al'ummar Nigeria ta fada cikin rudu da baganniya har takai yadda suke nemawa kansu mafita ta hanyar siyasa ko cikin wani tsari wanda ba na Allah ba, amma sakamakon ba suna neman mafitar a inda take bane sai ya zamana sun qara dulmiya/nutsewa cikin duhu.
Allah ya aiko musu da wata aya a matsayin hujjarsa a kansu amma sun kasa fahintar hakan. Memakon su riqi wannan ayar hannu bibiyu sai suka bijire mata.
Allah (S. W. A) na cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
" وَمَا مَنَعَنَآ أَن نُّرۡسِلَ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّآ أَن كَذَّبَ بِهَا ٱلۡأَوَّلُونَۚ وَءَاتَيۡنَا ثَمُودَ ٱلنَّاقَةَ مُبۡصِرَةٗ فَظَلَمُواْ بِهَاۚ وَمَا نُرۡسِلُ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّا تَخۡوِيفٗا ." (٩٥)
" BA WANI ABU NE KE HANA MU AIKO DA AYA (akan su ba) FACE MUTANEN FARKO SUN QARYATA TA. MUN ZOWA SAMUDAWA DA TAGUWA (a bayyane) SUNA GANINTA, AMMA SAI SUKA YI ZALUNCI DA ITA (ta hanyar soke ta). LALLE BA MA AIKO DA AYA (cikin al'umma) FACE DON TSORATARWA. "
(SURATUL-ISRA'I:59)
To, mu ayar da Allah ya saukar mana a wannan nahiya tamu ta Africa shine SAYYID ZAKZAKY (H). Da ace wannan al'umma mai hankali da tunani ce da ta riqe wannan aya da hannaye biyu (Firmly), amma sai ya zamana ta zalunci kanta ta hanyar cutar dashi kamar yadda al'ummun farko suka riqa yi.
Ita kuwa al'umma a duk lokacin data zalunci kanta babu abinda ke biyo bayan haka face qunci da bala'i da musiba kala-kala.
YAA ALLAH KA GANAR DA WANNAN AL'UMMA TUN LOKACI BAI QURE MATA BA 😭😭😭😭😭
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
28th April, 2021/ 16th Ramadan, 1442.