Abubuwan da ya kamata a nisanta cikin Azumi !!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KA KIYAYE SU DON INGANTA AZUMINKA 


Cikin rubutunmu na baya munyi bayani kan cewa Azumi shine nisantar ci da sha da kuma jima'i tun daga ketowar Alfijri har zuwa shigar dare , sannan kuma muka ambaci wasu abubuwa masu inganta shi.


A yau kuma za mu qara muku wasu abubuwa ne wadanda akayi hani wajen aikata su ga mai azumi don gudun bata azumi ba tare da an sani ba. 


Yazo daga Imam Ridha (A. S) kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



 فقه الرضا عليه السلام‏ اجْتَنِبُوا شَمَّ الْمِسْكِ وَ الْكَافُورِ وَ الزَّعْفَرَانِ وَ لَا تُقَرَّبْ مِنَ الْأَنْفِ وَ اجْتَنِبِ الْمَسَّ وَ الْقُبْلَةَ وَ النَّظَرَ فَإِنَّهَا سَهْمٌ مِنْ سِهَامِ إِبْلِيسَ وَ احْذَرِ السِّوَاكَ الرَّطْبَ وَ إِدْخَالَ الْمَاءِ فِي فِيكَ لِلتَّلَذُّذِ فِي غَيْرِ وُضُوءٍ فَإِنْ دَخَلَ مِنْهُ شَيْ‏ءٌ فِي حَلْقِكَ فَقَدْ فَطَّرَكَ وَ عَلَيْكَ الْقَضَاءُ اجْتَنِبُوا الْغِيبَةَ غِيبَةَ الْمُؤْمِنِ وَ احْذَرِ النَّمِيمَةَ فَإِنَّهُمَا يُفَطِّرَانِ الصَّائِمَ وَ لَا غِيبَةَ لِلْفَاجِرِ وَ شَارِبِ الْخَمْرِ وَ اللَّاعِبِ بِالشِّطْرَنْجِ وَ الْقِمَارِ وَ لَا بَأْسَ لِلصَّائِمِ بِالْكُحْلِ وَ الْحِجَامَةِ وَ الدُّهْنِ وَ شَمِّ الرَّيْحَانِ خَلَا النَّرْجِسِ وَ اسْتِعْمَالِ الطِّيبِ مِنَ الْبَخُورِ وَ غَيْرِهِ مَا لَمْ يَصْعَدْ فِي أَنْفِهِ فَإِنَّهُ رُوِيَ أَنَّ الْبَخُورَ تُحْفَةُ الصَّائِمِ وَ لَا بَأْسَ لِلصَّائِمِ أَنْ يَتَذَوَّقَ الْقِدْرَ بِطَرَفِ لِسَانِهِ وَ يَزُقَّ الْفَرْخَ وَ يَمْضَغَ لِلطِّفْلِ الصَّغِيرِ فَإِذَا صُمْتَ فَعَلَيْكَ أَنْ تُظْهِرَ السَّكِينَةَ وَ الْوَقَارَ وَ لْيَصُمْ سَمْعُكَ وَ بَصَرُكَ عَمَّا لَا يَحِلُّ النَّظَرُ إِلَيْهِ وَ اجْتَنِبِ الْفُحْشَ مِنَ الْكَلَامِ وَ اتَّقِ فِي صَوْمِكَ خَمْسَةَ أَشْيَاءَ تُفَطِّرُكَ الْأَكْلَ وَ الشُّرْبَ وَ الْجِمَاعَ وَ الِارْتِمَاسَ فِي الْمَاءِ وَ الْكَذِبَ عَلَى اللَّهِ وَ عَلَى رَسُولِهِ وَ عَلَى الْأَئِمَّةِ ع وَ الخناء [الْخَنَا] مِنَ الْكَلَامِ وَ النَّظَرَ إِلَى مَا لَا يَجُوزُ وَ إِنْ نَسِيتَ فَأَكَلْتَ أَوْ شَرِبْتَ فَأَتِمَّ صَوْمَكَ وَ لَا قَضَاءَ عَلَيْكَ وَ لَا بَأْسَ أَنْ يَذُوقَ الطَّبَّاخُ الْمَرَقَةَ وَ هُوَ صَائِمٌ بِطَرَفِ لِسَانِهِ مِنْ غَيْرِ أَنْ‏



(1) علل الشرائع ج 2 ص 71.


(2) المحاسن ص 318.


Imam Ridha (A. S) na cewa; 


" Ka nisanci shafa (Turare) Miski da Kafur da Za'afaran kada su kusanci hanci (Norse ). Kuma ku nisanci shafa da sumba (touch and kiss) da kuma kallo ( looking ), domin su kifiya ce daga kifiyoyin Iblis. 


Kuma ku nisanci yin asuwaki (brush) da danyen (fress stick) da kuma shigar da ruwa cikin bakinka don jin dadi in ba wajen alwala ba, domin idan wani abu ya shiga maqogoronka haqiqa ka karya (azumin naka), kuma akwai ramuwa a kanka. 


Ka nisanci gibar mumini kuma ka tsoraci annamimanci, domin su suna karya azumi. Hakama kada kayi gibar fajiri da mai shan giya, da yin wasa da Dara da caca.


Babu laifi ga mai azumi ya sanya kwalli da yin Qaho da shafa mayi da sanya wani abin qamshi koma bayan abu mai najasa. Da kuma wata qura mai kauri ta wajen aiki da makamantansu matuqar dai basu wuce cikin hancinsa ba , domin an riwaito cewa ita (Qura mai kauri) tana bata azumi (matuqar ta wuce cikin hanci ko maqogoro). 


Kuma babu laifi ga mai azumi ya dandana (test) wani abinci/sha da deshin harshensa (with the tip of his tongue) ko kuma ya gwada ta hanyar bawa qanqanin yaro, idan (yaron) yayi shiru, to, sai ka nutsu da samun kwanciyar hankali (da wannan abinda ka sa cikin abincin naka ko abin sha). 


Kuma ka kiyaye jinka (hearing) da ganinka ga abinda bai halatta gare ka ka kalle shi ba, sannan kuma ka nisanci alfasha daga magana. Kuma ka nisantar da abubuwa biyar (5) ga azuminka wadanda zasu iya karya maka shi. 


(1)- Ci (eating) da


(2)- Sha (drinking) da 


(3)- Yin jima'i (sexual intercourse) da 


(4)- Nutsewa cikin ruwa, da 


(5)- Yin qarya ga Allah da Manzonsa da A'immah (A. S). Da kuma ha'inci a magana da yin kallo zuwa ga abinda bai inganta a kalle shi ba.


Kuma idan ka manta har kaci (ate) ko ka sha, to, ka cika azumin naka babu ramako a kanka. Kuma babu laifi a kanka don ka dandana girkin romo (miyar nama, ko ma sai dai wani nau'in girki) da deshin harshenka alhali kana azumi matuqar bai wuce cikin maqogoronka ba.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)


   16TH APRIL, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post