@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KHUDUBAR ANNABI (S. A. W. W) GA SAHABBANSA GAME DA AZUMI
Cikin kowanne lokaci na rayuwa mutum na da buqatar ya aikata abubuwan da za su kusanta shi ga Allah kuma su zama wata garkuwa wacce za ta shiga tsakaninsa da Shaidan.
Musamman ma cikin wannan wata wanda ake ninninka ladar ayyukan bayi na alkhairi wanda ba a samun irin wannan dama sai cikin watan Ramadan.
Annabi (S. A. W. W) ya yiwa Sahabbansa wata gajeriyar Khudba mai fadi'idantarwa musamman a irin wannan mata mai alfarma.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
الأمالي للصدوق ابْنُ الْمُغِيرَةِ بِإِسْنَادِهِ عَنِ السَّكُونِيِّ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص لِأَصْحَابِهِ أَ لَا أُخْبِرُكُمْ بِشَيْءٍ إِنْ أَنْتُمْ فَعَلْتُمُوهُ تَبَاعَدَ الشَّيْطَانُ مِنْكُمْ كَمَا تَبَاعَدَ الْمَشْرِقُ مِنَ الْمَغْرِبِ قَالُوا بَلَى قَالَ الصَّوْمُ يُسَوِّدُ وَجْهَهُ وَ الصَّدَقَةُ تَكْسِرُ ظَهْرَهُ وَ الْحُبُّ فِي اللَّهِ وَ الْمُوَازَرَةُ عَلَى الْعَمَلِ الصَّالِحِ يَقْطَعَانِ دَابِرَهُ وَ الِاسْتِغْفَارُ يَقْطَعُ وَتِينَهُ وَ لِكُلِّ شَيْءٍ زَكَاةٌ وَ زَكَاةُ الْأَبْدَانِ الصِّيَامُ[3].
أمالي الصدوق: 37 و 38.
Yazo cikin Amaliy Lis-Sudduq daga Ibn Mugirata da isnadinsa daga Sakuniyyi, daga Sadiq daga iyayensa (A. S) yace: Manzon Allah (S. A. W. W) ya cewa Sahabbansa;
" BA NA BAKU LABARI GAME DA WANI ABU WANDA IN KUN AIKATA SHI SHAIDAN ZAI NISANTA DAGA GARE KU KAMAR YADDA YA NESANTA TSAKANIN MAHUDAR RANA DA MAFADARTA BA ?"
Suka ce; " Na'am yaa Ma'aikin Allah. " Yace;
(1)- SHI AZUMI YANA BAQANTA FUSKARRSA. (Wato a duk lokacin da kuke azumi fuskar Shaidan za tayi baqi-qirin saboda bacin rai).
(2)- KUMA SADAQA TANA KARYA QASHIN BAYANSA. (Ita sadaqa tana bishe fushin Allah akan bawansa, kuma tana toshe masifun da kan iya samun mutum).
(3)- SOYAYYA KUMA DOMIN ALLAH DA DAGEWA KAN KYAWAWAN AYYUKA (duk biyun) MASU YANKE BAYANSA NE. (Wato kaji kana so tare da nuna soyayya ga mutum don mabiyin Allah ne da kuma dagewa kan kyawawan ayyuka suna yanke bayan Shaidan kamar dai yadda Allah ya yanke bayan Abu Lahabin yadda yanzu babu mai iya miqewa yace shi zuriyar Abu Lahabin ne).
(4)- SHI KUMA ISTIGFARI YANA KATSE MASA TSATSONSA (spinal cord). (A duk lokacin da mutum yayi Istigfari yakan yanke lakar Shaidan ta yadda ba zai iya yin wani motsi wanda zai iya cutar da mutum ba). KO WANNE ABU NA DA ZAKARSA, ZAKKAR JIKI SHINE AZUMI. "
Sannan kuma yazo cikin wani hadisi daga Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ ص أَنَّهُ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ الصَّوْمُ لِي وَ أَنَا أَجْزِي بِهِ وَ لِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ وَ فَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ وَ الَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ.
" ALLAH MAI GIRMA DA MADAUKAKI NA CEWA; " SHI AZUMI NAWA NE, KUMA NI NAKE BADA LADARSA.
GA KOWANNE MAI AZUMI YANA DA FARIN CIKI BIYU. FARIN CIKI YAYIN DA YAKE YIN BUDA BAKI, DA KUMA FARIN CIKI YAYIN DA YAKE HADUWA DA UBANGIJINSA.
NA RANTSE DA WANDA RAN MUHAMMADU KE HANNUNSA, LALLE WARIN BAKIN MAI AZUMI YAFI DADI (qamshi) WAJEN ALLAH FIYE DA QAMSHIN (Turare) MISKI. "
NB:- Ko wanne aiki ibada Allah ne ke bada ladarsa ba wani ba, sai dai saboda girman azumi a wajen Allah yasa yace Shi ne ke bayar da ladarsa, kuma shi azumi wani aiki ne wanda Allah kadai yasan mai yinsa (Khass). Domin abu wanda ba a fahinci mai yinsa da marar yinsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda
(08137925034)
13TH APRIL, 2021.