Ishaq Muh'd Dan Goma |
...Tun Kafin Azumi Ya Zo, Na Ga Masu Gidajen Radiyo Sun Fara Bada Sanarwar Cewa; 'Kofarsu a Bude Take Ga Mutane; Su Zo Su 'Dauki Nauyin Shirye-Shirye Tafsiran Azumi, Wanda Hakan Zai Laqume Miliyoyin Naira, Kuma Na San Attajiranmu Da 'Yan Siyasa Zasu Amsa 'Kiran, Kamar Yanda Suka Saba Duk Shekara.
Muna 'Kira Ga Masu Hannu Da Shuninmu, Da Su Dubi Girman ALLAH Su Karkata Wadannan Kudaden Wajen Siyo ABINCI Da KAYAN MASARUFI Don Tallafawa Masu 'Kananan 'Karfi Dake Kewaye Da Su a Unguwanninsu, Don Suma Su Samu Yin Azumin Da 'Karfinsu, Cikin Walwala Da Farin Ciki.
Don Wallahi Wallahi, Mutane Da Dama Suna Cikin Mawuyacin Hali, Babu Wani Mai 'Karfin Da a Unguwarsu Za'a 'Kirga Gidaje 1 Zuwa 5 Ba'a Samu Mai Matsanancin Bukata Ba, Wallahi Akwai a Cikin Al'ummarmu Wanda Da Ruwa Da Kunu Suke Sahur Da Buda Baki Kusan Kullum, Su Zurawa Sarautar ALLAH Ido
In An Yi Haka(Ciyar Da Marasa 'Karfi) Sai Mutum Ya Fi Samun Lada Da Haske, a Wurin MAHALICCI(S.W.T) Fiye Da 'Daukar Nauyin Tafsiran Azumi.
Duk Wanda Yake Son Ya Saurari Tafsirai, To Na Tabbata a Cikin Fitattun Malaman 'Kasar Nan Babu Wanda Bashi Da Tafsirai Daga BAQARA Zuwa NASI Ba, a Computer Sai Ya Je a Tura Masa, Yayi Ta Ji Daga Farkon Ramadan Har 'Karshensa, Shikenan!
ALLAH Ya 'Kara Horewa Kowannenmu Abin Masarufin Da Zai Yi Amfani Da Shi a Wannan Watan Na RAMADAN(Mai Shirin Kamawa), Don Arzikin ANNABI MUHAMMADU(S.A.W)