17 Ga Ramadan: Ranar da aka fara yakin Badr !


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Yaqin Badr shine yaqi na farko wanda aka fare shi a muslimci domin daukaka addinin Allah (S. W. A). Anyi shekaru 13 a garin Makkah ana cutar da musulmi ba tare da sunyi laifin komai ba in har ka cire kiran da suke yi na tsarkake Allah wajen bauta.


Bayan tsanani yayi tsanani sai Allah ya umarci Annabi (S. A. W. W) da cewa suyi Hijr daga Makkah zuwa Madinah tare da duk wadanda suka bi shi daga muminai. Wannan umarni yayi sanadin barin musulmi garin Makkah zuwa Madinah don su sami damar bautar Allah da kadaita shi. 


Ganin karbar da mutanen Madinah suka yiwa musulmi tare da ganin muslimci na cigaba sai Kafiran Makkah suka soma tunanin ya za suyi su kawo qarshen muslimci da wanda yazo dashi. Saboda haka sai suka fara kai hare-hare zuwa yankunan dake kusa da Madinah suna lalata kayayyakin musulmi na amfanin gona da 'ya'yan itatuwan bishiyoyin musulmi. 


Ganin wannan hali da ake ciki don gudun kada kafirai su cimma musulmi da muslimci sai Allah (T) ya yiwa musulmi iznin yaqi wanda a baya basu sami hakan ba. 


" ANYI IZNI (na yaqi) GA WADANDA AKE YAQARSU CEWA AN ZALUNCE SU, KUMA ALLAH GAME DA TAIMAKONSU MAI IKO NE ."


           (QUR'AN) 


Saboda haka sai Annabi (S. A. W. W) ya qudiri aniyar kai hari ga wasu hanyoyin kafirai da suke samun kudaden shiga suna amfani dasu wajen kaiwa musulmi hari.


A bangaren kafirai kuwa suna can suna ta shirye-shiryen sojojinsu don kawo gaggarumin hari na murqushe musulmi. Sun hada rundunar soji da takai ta mutane 1000, wacce ta hada da Raquma 700 da Dawakai 100 don aiwatar da wannan qudiri nasu. 


Da labari ya isowa Manzon Allah (S. A. W. W) sai shima ya hada runduna ta mutane 313 da nufin tunkarar wadannan mutane dubu (1000). Da musulmi suka iso wani guri da ake kira BADR sai Annabi (S. A. W. W) ya umarce su da su tsaya anan su jira isowar kafirai, kuma ya miqa Tuta a hannun Imam Ali (A. S). 


Wannan yaqi an fare shi ne a ranar 17 ga Ramadan, shekara ta biyu (2) bayan Hijrar Annabi (S. A. W. W). 


Kamar yadda larabawa suka saba yin yaqinsu ne, jarumai ne ke fara fitowa cikin kowanne bangare su fara gwabzawa (physical combat) kafin yaqi ya barke na baki daya !


Sabida haka a wannan rana an sami mutane uku(3) cikin kafirai sun fito don fara gwabzawa. 


WALID,


SHAYBA, DA 


UTBAH sune jaruman da suka fito daga cikin kafirai, sai Annabi (S. A. W. W) ya umarci HAMZA da ALI da UBAIDAH cewa su fito daga rundunarsa. 


Ya cewa Hamza ya qwama da Shaybah, Aliyu kuma da Walid, shi kuma Ubaidah da Utbah. Imam Ali (A. S) yayi nasarar kashe Walid, Hamza ma ya kashe Shaybah, shi kuma Ubaidah Utbah yaji masa ciwo, a qarshe Imam Ali (A. S) ya zaburanto ya kashe shi, daga nan sai yaqi ya barke !


Musulmi sun jikkata, amma dai a qarshe Allah ya basu nasara na kashe mutane 70 daga cikin kafirai tare da kama 70 daga cikinsu a matsayin fursunonin yaqi. 


Wannan nasarar da suka samu ne Allah ke bamu labari ta hanyar ce musu; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



" وَلَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ بِبَدۡرٖ وَأَنتُمۡ أَذِلَّةٞۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ. ( ٣٢١)


" HAQIQA ALLAH YA TAIMAKE KU A BADR YAYIN DA KUKE MASU RAUNI (na rashin yawa da rashin makamai da qarancin abin hawa), KUJI TSORON ALLAH (kan haka) KO ZA KU GODE (masa kan wannan nasara da ya ba ku). "


(SURATUL-BAQARATA :123)



Saboda tsananin wahalar da suka sha tare da munanan raunuka shine yake qarfafarsu da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" إِن يَمۡسَسۡكُمۡ قَرۡحٞ فَقَدۡ مَسَّ ٱلۡقَوۡمَ قَرۡحٞ مِّثۡلُهُۥۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيۡنَ ٱلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَيَتَّخِذَ مِنكُمۡ شُهَدَآءَۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّٰلِمِينَ."( ٠٤١)


" IDAN MA WANI MIKI NE YA SHAFE KU (sakamakon wannan yaqi) TO, HAQIQA MISALIN WANNAN MIKI YA SAMI JAMA'AR (da kuka yi yaqin tare dasu). WADANNAN RANAKU NE DA MUKE JUJJUYA SU CIKIN MUTANE (yau wadannan su kasance masu nasara gobe wadancan da nasara DOMIN ALLAH YASAN WADANDA SUKA YI IMANI (na gaskiya daga cikinku) KUMA YA 'DEBI SHAHIDAI DAGA CIKINKU. KUMA LALLE ALLAH BA YA SON AZZALUMAI !"


(SURATUL-BAQARATA :140)


A wannan rana munafukai da masu rauni (weak) cikin zukatansu sun zargi muminan cikinsu da cewa wai addininsu ya rude su. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


إِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ غَرَّ هَٰٓؤُلَآءِ دِينُهُمۡۗ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ ( ٩٤)


 وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ يَتَوَفَّى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ (٠٥ )


ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ ( ١٥)


" YAYIN DA MUNAFUKAI DA MASU CUTA CIKIN ZUKATANSU KE CEWA, " LALLE WADANNAN ADDININSU YA RUDE SU !" TO, DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH (daga cikinku) LALLE ALLAH MABUWAYI NE MAI HIKIMA (cikin komai nasa) ."


" KUMA DA ZA KAGA A LOKACIN DA MALA'IKU KE 'DAUKAR RAN KAFIRAI SUNA DUKAN FUSKOKINSU DA BAYANSU (suna ce musu) KU 'DANDANI AZABAR GOBARA (ta hannunmu da Takuban muminai ) ! "


" HAKAN KUWA YA FARU NE (a kanku) SAKAMAKON ABINDA HANNAYENKU YA GABATAR (na zaluntar muminai), KUMA LALLE ALLAH BAI KASANCE MAI ZALUNTAR BAYI BA. "


(SURATUL-ANFAL:49-51)


Wannan shine karo na farko wanda musulmai suka maida martani ga kafirai, kuma Allah ya taimake su kamar yadda ya alqawaranta musu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


29th April, 2021/ 17th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post