15 Ga Ramadan: Haihuwar Imam Hassan Bn Aliyu Bn Abu Dalib (A.S) Jikan Manzon Allah (S.A.W.W)


 

Takaitaccen tarihinsa


An haifi Imam Hassan Bn Aliyu Bn Abi Dalib (A.S) a watan Ramadan 15, 625 kuma an haifeshi ne a garin Madina bayan hijira. Imamancin Daga Ramadan 21, har tsawon shekara 6 zuwa takwas, wasu ruwayan kuma sunce shekaru 10 ne. Yayi shahada a 28 ga watan Safar 670 a garin Madina, wanda yayi shahada din ne ta dalilin bashi guba, an bisne shi a makwancin Al-Baqi.


Imami kafin sa shine Imam Ali bn Abu Dalib (A.S), wanda kuma ya biyo bayansa shine dan uwansa Imam Al-Husayn bn Ali (A.S), wanda mahaifinsa kuma kuma shine Imam, Ali bn Abi Dalib (a) din, mahaifiyarsa kuma diyar Annabin mu wato Fatima bnt. Muhammad (S.A), yana da yan uwa Imam Al-Husayn, 'Abbas, Muhammad,... Mace kuma itace Zaynab (S.A)..


Laqubbansa sune 

Al-Mujtaba (zaɓaɓɓe)

Al-Sibt (jika)

Sayyidash Shababu ahl jannah (shugaban samarin aljanna)

Al-Zaki ( tsarkakakke)

Al-Taqi (mai takawa)

Al-Sayyid (Shugaba)


Imam Hasan bn Ali (A.S)) shine farkon Dan Imam Ali (A.S) da Fatima (S) kuma jikan farko ga Manzon Allah (S). An ruwaito cewa Annabi (S) ya zaba masa sunan al-Hasan ne sabida yana matukar kaunarsa. Shekarun farko na rayuwar Imam Hasan sun kasance a lokacin rayuwar Manzon Allah (S). Ya kasance a cikin Mubaya'ar Ridwan da kuma cikin labarin Mubahala tsakanin Annabi (S) da wakilin Kiristocin Najran.


Tushen Shi'a da na Sunni sun kunshi riwayoyi masu yawa na kyawawan halayya na Al-Hasan. A cewar wadannan ruwayoyi, yana daya daga cikin Mutanen da Annabi ya lullube da mayafi, wanda aka saukar da Ayar Tsarkaka (Kur'an 33:33). Ayoyin da suka hada da 76: 8, 42:23, da 3:61 suma an saukar dasu game dashi, iyayensa, da dan uwansa. Imam Ya ba da duk dukiyarsa sadaka domin Allah da daukakar addinin kakansa, kuma saboda irin waɗannan ayyukan karimci, sai aka zo ana kiransa "Mai karimci daga Iyalan Annabi (S) ". Ya tafi hajji sau ashirin da biyar ba tare da takalmi ba.


Allahu Akbar, Allah kai dadin tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad da ahlayensa managarta. Ina mai farin cikin taya al'ummar Muslimin duniya murna da zagayowar haihuwar jikan Manzon Allah (S) Imam Hassan Al-Mujtaba (S.A)


Bin Haroun Sigau

08065008703



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post