An haifi Mukhtar a Ta'if a shekara ta 622 (shekarar da annabin Musulunci Muhammad yayi hijira zuwa Madina), Mahiafinda shine Abu Ubayd al-Thaqafi , kwamandan sojojin musulmi daga kabilar Banu Thaqif, shi da ne ga Dawma bint Amr bin Wahb bin Muattib.
Bayan wafatin Annabi Muhammad (S.A.W.W) a 632, Abubakar ya zama khalifa. Shi kkma ya rasu bayan shekaru biyu sannan kuma Umar ya gaje shi , wanda ya faɗaɗa yaƙe-yaƙen Musulmi wanda Abubakar ya fara, kuma ya tura mahaifin Mukhtar Abu Ubayd zuwa fagen daga Iraki. An kashe Abu Ubayd a yakin Gada a watan Nuwamba na 634. Mukhtar, sannan yana da shekaru goma sha uku, ya kasance a Iraki bayan mamayar musulmai da wannan yankin, kawunsa Sa'd ibn Masud al-Thaqaf ne ya raine shi.
Bayan an shafe shekaru, a cikin shekarar 687, Mus'ab bn al-Zubayr, gwamnan Basra kuma kane ga Abdallah bn al-Zubayr, ya ƙaddamar da farmaki a kan mutanen Kufa. Wani bangare mai yawa na sojojinsa ya kunshi manyan mutane Kufan, wadanda a baya suka tsere daga matakan ladabtarwar da Mukhtar ya yi.
Mukhtar dai jarumi ne kuma sadauki wanda ya addabi Azzalumai, wanda suka kashe Imam Hussain (A.S) da sahabbansa a karbala. Inda ya yi ta bi ɗaya bayan ɗaya yana yakarsu, ba gazawa yana karkashe su.. kuma shidin jarumi ne babansa ma jarumi. Hakan yasa a lokacin kowa shakkarsa yake.
Wanda daga baya, zuwa smwasu yan shekaru takai yawan sojojin Mukhtar a Kufan babu tabbacin ko sun kai dubu uku zuwa sittin, ya dogara da tushen don an sami sabani kan yawarsu. Mutanen Kufa sun koma bayan an ci galabarsu a yaƙe-yaƙe na Madhar, wanda yake kusa da Tigris tsakanin Basra da Kufa, da Harura, wani ƙauye kusa da Kufa. Daga nan Mus'ab ya yiwa fadar Mukhtar kawanya har tsawon wata hudu. Ibn al-Ashtar, wanda a lokacin yana gwamnan Mosul, bai yi yunƙurin sauke Mukhtar ba, ko don saboda ba a kira shi zuwa aiki ba ne, ko saboda ya ki sammacin Mukhtar ne. Koma dai yane, daga baya Mus'ab ya ƙare ya fadawa Mukhtar. A ranar 3 ga watan uku 687 kamar yadda yazo a ruwaya Mukhtar ya fito daga faada tare da rakiyar magoya bayansa goma sha tara, (inda sauran sun ki yin yaki), wanda yasa aka kashe Mukhtar inda shi Mukhtar an kashe shi yana faɗa (Yaƙi) ne sabida bai sallama ba, bayan an kashe shi, ragowar 'yan bangaran sa, wadanda yawansu ya kai dubu shida, su mika wuya kuma Mus'ab ya kashe su. Ita daya daga cikin matan Mukhtar, mai suna Umrah bint Nu'man bn Bashir al-Ansari, ta ki yin Allah wadai da ra'ayin mijinta don haka ita ma aka kashe ta, yayin da dayar matar tasa ta yanke masa hukunci tana mai tsine masa hakan ya saka aka barta a raye. A wannan lokaci an yanke hannun Mukhtar aka rataye a bangon masallaci.
An ruwaito cewa, qabarin Mukhtar yana cikin Raundar Muslim ibn Aqil, a bayan gidan Babban Masallacin Kufa. Amma wasu bayanan sun nuna cewa Mus’ab ya kona gawarsa.
Bin Haroun Sigau