@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
FASIQI SUNAN DA ALLAH YA KIRAKA DA SHI CIKIN ALQUR'ANI
Nayi nufin rubuta wannan budaddiyar wasiqa zuwa gare ka ne sakamakon wasu kalaman da kayi da sunan wa'azi a garin Guda dake qaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi ranar asabar 13th March, 2021 da sunan wa'azin walimar auren dan yayana Musa Abdullahi Guda.
Karatun da wasu sukayi kafin naka dana wadanda sukayi bayan naka ya ratsa zukata saboda duk abinda suka fada gaskiya ne kuma haka ya kamata a aikata cikin addini muslimci, musamman ma wa'azin na qarshe, wato shugaban majalisar malaman Izala na qasar Ningi Ustaz Abubakar Musa (Baban Yamu).
Cikin karatun naka ka kawo misali da cewa riqe Carbi a hannu ko rayata shi a wuya ba shine imani ba, sannan shimfida Buzu a hau ana karatu ana rishi/rangwadi ba shine imani ba, imani shine aikata abinda Allah yayi umarni da aikata shi, da kuma nisantar abinda yayi hani a kansu.
Na'am, abinda ka fada gaskiya , domin duk wani aikin da mutum yayi shi babu ikhlasi cikinsa ba imani bane, sai dai wannan kalaman naka ka yi sune da nufin muzanta wasu masu siffantuwa da wadannan siffofi daka kawo a matsayin misali.
Ganin ba ka kawo misali da irin siffantuwar da kuke siffantuwa da ita ba yasa naga ya kamata nayi maka tambaya wata kamar haka.
Shin, wannan daura kwali da kake yi a kanka tare da riqe microphone a hannunka kana wa'azi shine imani in har ba ka aikata abinda Allah ya umarce ka da shi tare da nisantar abinda ya hane ka aikatawa ba ?
Gaskiya da ace kana da tunani haqiqa da ba za ka bar masu gabatar da kai yayin fara wa'azinka su riqa ambaton cewa,
" Malaminmu na gaba wanda zai yi wa'azi shine Alqali Umar Ishaq. " ba, . Na san a tunaninsu hakan fitar da wani matsayi ko daraja ce gare ka kamar yadda suke ambaton wasu falaloli na takwaranka ta hanyar cin zarafin Manzon Allah (S. A. W. W), amma a gare ku ba wata falala bace face muzantaku a wajen wadanda ke kallonku.
A duk lokacin da mai hankali da ilimi ya ji anyi maka irin wannan gabatarwa farkon abinda zai fara bijiro masa a ransa shine, yau wanne irin fasiqi ne za mu gani wanda zai yi mana wa'azi ?
SUNAN DA ALLAH YA RADA MAKA SHI CIKIN ALQUR'ANI
Na san kana karanta Qur'ani tunda har wa'azi kake yi, amma ka taba cin karo da wannan aya dake cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" وَلۡيَحۡكُمۡ أَهۡلُ ٱلۡإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱ
لَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ ." (٧٤)
" KUMA MUTANEN LINJILA SUYI HUKUNCI DA ABINDA ALLAH YA SAUKAR CIKINTA. KUMA DUK WANDA BAI YI HUKUNCI DA ABINDA ALLAH YA SAUKAR BA WADANNAN SUNE FASIQAI !"
(SURATUL-MA'IDA, AYA TA :47)
To, ga shi kai alqali ne wanda hakan ya zama maka Title wanda ake amfani dashi wajen gabatar da kai yayin wa'azinka. Sannan kuma kowa ya sani cikin wannan Qasa Nigeria ana bin tsarin Bature ne (constitution) wajen hukunci cikin kotuna, wanda kai ma baka fice daga cikinsu ba tunda ba da abinda Allah ya saukar kuke yin hukunci ba.
Kenan kai ma Fasiqi ne wanda shari'ar muslimci bata yarda da shaidarka ko maganarka ba. Saboda haka maganarka ba za ta zama hujja abin riqewa ko amfani da ita ba.
MAGANARKA GAME DA 'YAN SHI'AH
A cigaba da karatun da kayi wajen wannan walima ka kawo sharudan yadda ake neman aure har zuwa yadda ake yinsa , har kake cewa;
" IDAN AKA CE IYAYE SUN YARDARWA MUTUM DA NEMAN 'YARSU SAI YA CIGABA DA NEMA HAR ZUWA LOKACIN AURE, AMMA BA ZAI RIQA KWANCIYA DA ITA KAMAR YADDA 'YAN SHI'AH KE YI BA. "
Wannan maganar taka sai ta zama baquwar a wajena, domin iya sani na ban taba ji ko ganin dan Shi'ar da yake kwantawa da wacce yake nema kawai don an yarje masa nemanta ba.
Sakamakon kai fasiqi ne bisa sunan da Allah ya rada maka na asali sai naga ba zan iya gaskata maganar ka ba tunda Allah (T) ya umarce mu da cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن جَآءَكُمۡ فَاسِقُۢ بِنَبَإٖ فَتَبَيَّنُوٓاْ أَن تُصِيبُواْ قَوۡمَۢا بِجَهَٰلَةٖ فَتُصۡبِحُواْ عَلَىٰ مَا فَعَلۡتُمۡ نَٰدِمِينَ ."( ٦)
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! IDAN FASIQI YAZO MUKU DA LABARI KUYI BINCIKE (kafin gaskatawa) DON KADA KU AFKAWA WASU JAMA'A BISA JAHILCI, SAI KU WAYI GARI KUNA NADAMA KAN ABINDA KUKA AIKATA ."
(SURATUL-HUJRAT, AYA TA :6)
Abinda na sani cikin 'yan Shi'ar garin Ningi akwai wadanda matansu 'ya'yan 'yan Izala ne, domin nima tawa 'yar dan Izala ne haifaffiyar garin Jos wacce babanta na daga cikin mabiyan Sheikh Sani Yahya Jingir, wasu kuma iyayensu 'yan 'Dariqu ne, amma ban taba ji ko ganin haka ta faru ba sai a bakinka.
Saboda haka nake tambayarka, shin, ko za ka iya kawo mana sunan wani a garin Ningi ko wani gari wanda ya aikata haka? Idan muka sami sunansa sai muyi bincike don gaskata maganarka kamar yadda Allah ya umarce mu.
Idan kuwa ka kasa, to, ka dada tabbatar mana cewa kai cikakken fasiqi ne maqaryaci lamba 1. Kuma abin kunya ne ma ace ana sanya ka cikin masu wa'azi matuqar da'