Yanzu Haka Za Ku Bar Sheikh Abdul-Jabbar Ya RiQa Barna A Cikin Kasa ???




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


ITA BIYAYYA ANA YINTA NE KAN AIKIN ALKHAIRI


Gaskiyar magana ita ce, ITTIFAQAN malaman MAJA sun hadu kan cewa abinda Sheikh Abdul-Jabbar yake yi ya saba koyarwar muslimci wanda cigaba da yin abinda yake yi zai iya zama wata fitina cikin al'ummar musulmi tare da canza tunanin wasu su dawo kan wannan kiran nasa. 


Da gaske ne matuqar zai cigaba da yin irin wadannan karatun nasa zai canza tunanin wasu daga kan abinda suka shekara dubu (1000) a kansa zuwa kan kiran da yake yi, domin munga hakan ta faru cikin da'awar Sayyid Zakzaky (H)  yadda ya canza tunanin miliyoyin mutane har ta kai za a iya kashe su kan wannan fahinta tasu ba tare da sun juya baya ba. 


Tunda kun tabbatar abinda yake yi ba daidai bane, to, wajibi ne a kanku ku yaqi wannan fahinta tasa domin ta wannan hanya ce za ku tsira kuma ku tseratar da dinbim mabiyanku. Idan kuwa ba kuyi haka ba fushin Allah da tsinuwarsa za ta tabbata a kansu, domin zai zama ku ne kuka ci amanar musulmi da muslimci don ku kuka isa ku fada a ji.


Kada ku manta da abinda kuke karantawa cikin Qur'ani inda Allah (T)  ke cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 " لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ ٨٧ كَانُواْ لَا يَتَنَاهَوۡنَ عَن مُّنكَرٖ فَعَلُوهُۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ." ٩٧


" AN LA'ANCI WADANDA SUKA KAFIRTA DAGA BANU ISRA'ILA BISA HARSHEN DAWUDA DA ISAH 'DAN MARYAMA. HAKAN (kuwa ta faru ne) SAKAMAKON SUN SABA NE KUMA SUN KASANCE SUNA QETARE IYAKA. SUN KASANCE BA SA YIN HANI GAME DA ABIN QI DA AKE AIKATA SHI, TO, TIR DA ABINDA SUKA KASANCE SUNA AIKATAWA (na yin shiru kan abinda ake yi ba daidai ba)  ."



(MA'IDAH, AYA TA 78-79)


Hanya mafi sauqi ta samu yadda aka baku dama ku zauna ku tattauna dashi, ta hanyar haka za ku iya tattaro shi ku takwaikwaya shi ku nuqurqusa shi sannan ku kunyata shi ta hanyar kafa masa hujjoji na ilimi da hankali yadda ba zai iya kare kansa ba, daga nan sai duniya ta shaida cewa ashe da gaske ne abinda yake yi din ba daidai bane kamar yadda kuke fada, a qarshe sai ya kunyata ya tozarta ya wulaqanta kuma mabiyansa su dawo daga rakiyarsa. Yin hakan zai iya zama babban jihadi a gare ku. 


Sai dai kuma ban san hujjar da za ku dogara da ita wacce za ace ita ta hana ku yin zaman wannan Muqabalar ba, domin na ji ance Sarkin Musulmi ne yace kada ayi wannan zama, amma maganar kotu bata hana Sheikh ya tattauna (dialogue) da wani ba. 


Har na tuno wani hadisi da yake magana kan Sahabban da Annabi (S. A. W. W) ya tura su qarqashin wani Sahabi, sai ya kasance wannan Sahabi jagoran nasu ya hada wuta yace musu duk su faffada ciki a matsayin biyayya gare shi. Sai suka qi fadawa, da suka dawo sai suka fadawa Manzon Allah (S. A. W. W) abinda ya faru. Sai yace musu; 


" AI DA KUN KUSKURA KUN FADA CIKI DA KUWA BAKU FITO BA, AI ITA BIYAYYA ANA YINTA NE KAN AIKIN ALKHAIRI  ."


Yanzu kuna nufi Sarkin Musulmi ne zai hane ku aikata abinda zai zama shine maslahar muslimci da 'yanto musulmi daga fitinar data tunkaro su kamar yadda kuka fada yayin da kuka kai qararsa  ?


To, wallahi in dai har gaskiya ne abinda kuke fada kan cewa abinda Shehin malamin ke yi sharri ne da fitina cikin muslimci, to, shurunku kan abinda yake yi zai iya zama har ku ma kanku ba za ku tsira ba, domin Annabi (S. A. W. W) ya fadi haka ciki wannan hadisi da ke biye. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


23 - باب في الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر


حديث رقم :187


الرابع: عن النعمان بن بشير رضي الله عنهما، 


عن النَّبيّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: (مَثَلُ القَائِمِ في حُدُودِ اللهِ وَالوَاقعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَومٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ فَصَارَ بَعْضُهُمْ أعْلاها وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، وَكَانَ الَّذِينَ في أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوا مِنَ المَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقهُمْ، فَقَالُوا: لَوْ أنَّا خَرَقْنَا في نَصِيبِنَا خَرْقاً وَلَمْ نُؤذِ مَنْ فَوقَنَا، فَإِنْ تَرَكُوهُمْ وَمَا أرَادُوا هَلَكُوا جَميعاً، وَإنْ أخَذُوا عَلَى أيدِيهِمْ نَجَوا وَنَجَوْا جَميعاً) رواه البخاري.(القَائِمُ في حُدُودِ اللهِ تَعَالَى) معناه: المنكر لَهَا، القائم في دفعِها وإزالتِها، وَالمُرادُ بالحُدُودِ: مَا نَهَى الله عَنْهُ. (اسْتَهَمُوا): اقْتَرَعُوا.



"..MISALIN MAI TSAYUWA CIKIN DOKOKIN ALLAH (mai kiyayewa)  DA WANDA KE FADAWA CIKINTA (yana aikatawa), KAMAR MUTANE NE WADANDA AKA 'DAUKE SU CIKIN JIRGIN RUWA, WASU DAGA CIKINSU SUNA SAMANSA WASU KUMA NA QASANSA. SAI YA KASANCE IDAN WADANDA SUKE QASANSA SUNA BUQATAR RUWA SAI SUN HAURA TAKAN NA SAMANSU. SAI SUKA CE, " DA DAI ACE ZA MU HUDA (wannan Jirgi ta qasa) MUNA SAMUN TABONMU, DA DAI BA ZA MU CUTAR DANA SAMANMU (ta hanyar hausawa muna taka su) BA. "


TO, IDAN KUKA BARSU SUKA AIKATA ABINDA SUKA YI NUFI (na huda wannan Jirgi ta qasa), ZA KU HALAKA GABA 'DAYA  (domin ruwa zai iya shiga cikinsa) ! IDAN KUWA KUKA KAME HANNAYENSU (daga aikata wannan abinda suka yi nufi) SAI SU TSIRA, KU MA KU TSIRA GABA 'DAYA ! "........


-Bukhari ne ya riwaito. 


(RIYADUS-SAALIHEEN, HADISI MAI LAMBA 187)


Kun san kuwa wannan Muqabala ta fi sauqi wajen hana wannan Shehin matuqar kun yi nasara a kansa, amma dogaro da cewa an bi umarni Shugaba ne wannan qarya ce, domin ba a yin biyayya sai kan abinda ya zama alkhairi, ku kuma kun ce abinda malamin yake yi sharri ne ba alkhairi ba. 




Idan kuka bibiyi qissar AS-HABUS-SABTI za kuga masu yin hani kuma mummunan aiki ne kadai suka tsira yayin zuwan azaba. Kamar yadda Allah (T) ya bamu labari cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



" فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦٓ أَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذۡنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ بِعَذَابِۭ بَـِٔيسِۭ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ  ."٥٦١


" YAYIN DA SUKA MANTA DA ABINDA MUKA TUNATAR DASU SHI SAI MUKA TSERATAR DA WADANDA KE YIN HANI GAME DA MUMMUNA , KUMA MUKA KAMA WADANDA SUKA YI ZALUNCI DA AZABA MAI MUNI SAKAMAKON ABINDA SUKA KASANCE SUNA (aikatawa) NA FASIQANCI. "


(SURATUL-A'ARAAF, AYA TA 165)


To, gaskiya dai abinda kuke gudu ne ya auku, domin kunce wai in kun zauna dashi kun qara daukaka shi ne, kuma rashin zaman ma babbar daukaka ce gare shi, domin kowa ya san tsoro kuka ji ba wai biyayya bace, domin ko wata murya guda ba aji daga bakinku wacce ke nuna cewa kun yi jayayya dasu wajen nuna musu yin Muqabalar shine mafita ko maslaha ba.


Wannan abinda kuka yi sai ya tuna min maganar Sayyid Zakzaky (H) inda yake gargadin Gwamnati cewa idan ta afka mana ta dada tallata da'awarsa ce. Kuma abinda ya faru kenan, lokacin da Gwamnati ta afka mana sai ya zama har ma wadanda basu taba jin da'awarsa ba sun san shi kuma sun sallama masa.  Kamar hakane yadda kuka yi taron dangi kan Sheikh Abdul-Jabbar ya dada tumbatsa ambatonsa da kuma son jin karatuttukansa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


7th March, 2021/  24th Rajab, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post