@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DARASI CIKIN ZAMANTAKEWAR ABU-SUFYAN DA MATARSA HINDU
Yana daga cikin irin koken da ake samu daga bakin mata 🧕🏼🧕🏼🧕🏼🧕🏼 cikin kowanne bangare na aqidun da ake dasu cikin muslimci cewa mafi yawan mazajensu na yi musu qwauro wajen basu abinda za suci.
Abinda yasa ban ambaci wani bangare wadanda ba musulmai ba shine, dama su an san 75% daga cikinsu matansu ne masu ciyar dasu , mu kuma addininmu na muslimci yace komai dukiyar mace haqqin ciyar da ita da tufatar da ita na wuyan mijinta ne komai rashinsa, sai dai hakan bai hana ita matar tasa ta taimaka masa wajen sauqaqa masa halin quncin rayuwa ba.
Ba zai zama laifi ko abin zargi ba idan aka ce rashi ne yasa ake ganin gazawar miji wajen daukar takalifin iyalinsa, amma abin zargi ne ga wanda ke da hali sannan kuma ace yana quntatawa iyalinsa wajen abincin da za suci su sami qarfin bautawa Ubangijinsu.
Da Allah (T) ya jero siffofin muminai shine har yazo inda yake cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَنفَقُواْ لَمۡ يُسۡرِفُواْ وَلَمۡ يَقۡتُرُواْ وَكَانَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ قَوَامٗا ."
" KUMA SU NE WADANDA IDAN SUKA CIYAR (da abinci) BA SA YIN BARNA (albazaranci wajen bayarwa) KUMA BA SA QUNTATAWA (yin qwauro wajen bayarwa), SUN KASANCE A TSAKANIN HAKA SUKE TSAYAWA (ba sa bayar da abinda yayi yawa wanda zai zama barna, sannan ba sa bayar da kadan yadda ba zai ishi iyalansu ba). "
(FURQAAN:67)
To, su kuma wasu mazajen marar sa adalci sai suka dauki quntatawa a matsayin aikin yinsu ba wai don sun rasa ba. Yin hakan nasu yasa wasu mata sai su riqa daukar wani abu daga cikin dukiyar mazajen nasu suna qarawa kan abinda ake basu don su samu ya wadace su.
Kan hakan idan wasu mazajen nasu suka gano sai su riqa rigima a tsakaninsu har suna fassarasu a matsayin barayi don rashin adalci.
To, a gaskiya zalunci ne ace mutum bai rasa ba amma yana quntatawa iyalinsa abinda za suci ko abinda za su sanya a jikinsu.
Su kuma matan nasu bai zama laifi ba don sun dau wani abu na mazajen nasu suyi amfani dashi ba bisa saninsu ba matuqar dai ba barna suke yi musu ba.
Bari dai mu kawo misalai da wasu hadisai guda biyu wadanda suka zo kan abinda ya kasance cikin zamantakewar aure tsakanin Abu-Sufyan Bn Harb da matarsa Hindu Bnt utbatu Bn Rabi'a.
Ga riwayoyin nan kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وقال ابن سيرين: يقاصه، وقرأ: "وإن عاقبتم فعاقبوا بمثل ما عوقبتم به" النحل: 126
(2460) - حدثنا أبو اليمان: أخبرنا شعيب، عن الزهري: حدثني عروة: أن عائشة رضي الله عنها قالت: جاءت هند بنت عتبة بن ربيعة فقالت:
يا رسول الله، إن أبا سفيان رجل مسيك، فهل علي حرج أن أطعم من الذي له عيالنا؟ فقال: (لا حرج عليك أن تطعميهم بالمعروف)
Ibn Sirina yace : Yana yin qisasi sai yace :
" KUMA IDAN KUNYI SAKAYYA (kan zalunci ko cutar da akayi muku), TO, KUYI SAKAYYAR (ramuwa )DA MISALIN IRIN ABINDA AKAYI MUKU..... "
(SURATUL-NAHLI :126)
Baban Yamaniy ya bamu labari, Shu'aib ya bamu labari daga Zuhriy : Urwata ya bamu labari : Lalle A'isha (R. A) tace; " Hindu 'yar Utbata Bn Rabi'a ta zo sai tace; " Yaa Ma'aikin Allah, lalle Abu Sufyan mutum ne mai damqe hannu, shin, akwai laifi ne a kaina na ciyar da iyalanmu daga abinda yake da shi (ba tare da ya sani ba) ?" Sai yace :
" BABU LAIFI A KANKI DA KI CIYAR DASU GWARGWADON SHARI'A ."
(KITABAUL-MAZAALIMI, BABIN QISSAR WANDA AKA ZALUNTA IDAN AKA SAMI DUKIYAR AZZALUMIN, HADISI MAI LAMBA 2460)
Idan muka koma cikin wata riwayar kuma za mu gani kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
(2211)- حدثنا أبو نعيم: حدثنا سفيان، عن هشام، عن عروة، عن عائشة رضي الله عنها:
قالت هند أم معاوية لرسول الله صلى الله عليه وسلم: إن أبا سفيان رجل شحيح، فهل علي جناح أن آخذ ماله سرا؟ قال: (خذي أنت وبنوك ما يكفيك بالمعروف)
Abu Na'eem ya bamu labari, Sufyan ya bamu labari daga Hishaam, daga Urwata, daga A'ishatu (R. A) : " HINDU UWAR MU'AWIYYAH TA CEWA MANZON ALLAH (S. A. W. W), " LALLE ABU SUFYAN FA MUTUM NE MAI QWAURO, SHIN, AKWAI LAIFI NE A KAINA NA 'DEBI DUKIYARSA A SIRRANCE (secretly) ?" Yace;
" KI 'DIBA KE DA 'YA'YANKI GWARGWADON ABINDA ZAI ISHE KI TARE DA KYAUTATAWA (ba da nufin ki zalunce shi ba ) ."
(BUKHARI, KITABUS-SAUMI, HADISI NA 2211)
Saboda haka duk wanda ke quntatawa iyalinsa wajen abinci sunansa azzalumi, kuma ba zai zama laifi ga matarsa ba don ta qara mudu kan adadin mudun da yake basu.
Kada ku qara zaluntar kanku da kanku mata ta wajen zama da yunwa alhali mazajenku na da abinda za su iya ba ku wanda zai qosar daku, sai dai kuma kada kuyi amfani da wannan damar ku riqa dibar abinda yafi qarfin buqatunku don biyan wata buqata ta qashin kanku, domin yin hakan zai iya mayar daku ku zama azzalumai kamar yadda mazajen naku ke zakuntarku.
RAQE MUDU BA YA HANA AWU A WANNAN ZAMANI NA BUHARIYYAH.
#Free Sayyid Zakzaky (H) !!!
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
25th March, 2021/ 12th Sha'aban, 1442.