Yakamata Kasani Idan Ba Irin ta Kake Yi ba, To Ba Irin Sallar Annabi Bace !!!




SIFFAR SALLAR ANNABI (S. A. W. W)  A AIKACE KO KASANI KO BAKA SANI BA  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

IDAN BA IRINTA KAKE YI BA TO BA SALLAR ANNABI (S. A. W. W) BACE 

Cikin rubutunmu na baya mun kawo cewa Anas Bn Malik yace yanzu ba irin sallar da Annabi (S. A. W. W) ya koyar dasu ake yi ba, har wasu suna Cece-kuce kan wannan magana, alhali cikin littafan sunnah aka kawo. 

Ban san dalilin da yasa mutane suke qaryatawa ba, ko don bai ce ga yadda ya koyar dasu din bane ko kuma dai mutane sun fi so su riqa yin sallar Sarakuna ne ba irin ta Annabi (S. A. W. W)  ba?  Ko kuma dai qin karbar gaskiya ce tayi musu yawa  ?

To, bari dai mu kawo siffar yadda Annabi (S. A. W. W) ke yin sallar tasa wacce ya koyar da Sahabbansa, kuma hujja daga littafan sunnah.

Bukahari ya kawo cikin Sahihinsa qarqashin babi mai cewa WANDA YA YIWA MUTANE SALLAH WACCE BA KOMAI YAKE NUFI BA SAI DAI DON YA KOYAR DASU SALLAR ANNABI (S. A. W. W) DA KUMA SUNNARSA 

Ga misalai biyu nan kamar haka; 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(45) - صلى بالناس وهو لا يريد إلا أن يعلمهم صلاة النبي صلى الله عليه وسلم وسنته

(677) - حدثنا موسى بن إسماعيل قال: حدثنا وهيب قال: حدثنا أيوب، عن أبي قلابة قال: 
جاءنا مالك بن الحويرث في مسجدنا هذا، فقال: إني لأصلي بكم وما أريد الصلاة، أصلي كيف رأيت النبي صلى الله عليه وسلم يصلي فقلت لأبي قلابة: كيف كان يصلي؟ قال: مثل شيخنا هذا قال: وكان شيخا، يجلس إذا رفع رأسه من السجود، قبل أن ينهض في الركعة الأولى 


Musa Bn Isma'il ya bamu labari yace : Wahaib ya bamu labari yace: Ayuba ya bamu labari daga baban Qilabata yace : Malik Bn Hurairith yazo mana cikin wannan masallacin namu, sai yace; 

" LALLE NI ZANYI MUKU SALLAH, AMMA BA SALLAR NAYI NUFI BA SAI DAI DON NA NUNA MUKU YADDA NAGA ANNABI (S. A. W. W)  YAKE SALLAH  ."

Sai na cewa Baban Qilabata, to, yaya ya kasance yake sallar  ?Yace : " MISALIN (sallar) WANNAN TSOHON NAMU. " Yace :

" TSOHON YA KASANCE YANA YIN ZAMA YAYIN DA YA 'DAGO KANSA DAGA SUJADAH KAFIN YA MIQE DAGA RAKA'AR FARKO  ."

(Abin nufi idan yayi sujadah biyu a raka'ar farko yakan zauna kafin ya miqe zuwa raka'ah ta biyu). 

Misali na biyu wanda ya fitar mana da haqiqanin siffar sallar ita ce yadda yazo cikin Mustadrak na Hakeem kamar haka; 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

وقد روى ابن أبي حاتم فقال حدثنا وهب بن إبراهيم الفامي سنة خمس وخمسين ومائتين حدثنا إسرائيل بن حاتم المروزي حدثنامقاتل بن حيان عن الأصبغ بن نباتة عن علي بن أبي طالب قال لما نزلت هذه السورة على النبي صلى الله عليه وسلم « إنا أعطيناك الكوثر فصل لربك وانحر » قال رسول الله صلى الله عليه وسلم ياجبريل ماهذه النحيرة التي أمرني بها ربي فقال ليست بنحيرة ولكن يأمرك إذا تحرمت للصلاة ارفع يديك إذا كبرت وإذا ركعت وإذا رفعت وإذا رفعت رأسك من الركوع وإذا سجدت فإنها صلاتنا وصلاة الملائكة الذين في السماوات السبع وإن لكل شيء زينة وزينة الصلاة رفع اليدين عند كل تكبيرة وهكذا رواه الحاكم في المستدرك « 2/537 » من حديث إسرائيل بن حاتم به


Ibn Abiy Haateem ya riwaito yace, Wahbin Bn Ibrahim Al-Faamiy ya bamu labari cikin shekara ta 255 , Isra'eel Bn Haateem Al-Muruzeey ya bamu labari, Maqatil Bn Hayyan ya bamu labari daga Asbaghu Bn Nabatata, daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S) yace; 

" Yayin da aka saukar da wannan surah ga Annabi (S. A. W. W),  " LALLE MUN BA KA ALKHAUTHAR. KAYI SALLAR DOMIN UBANGIJINKA DA KUMA NAHR. " Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 

" YAA JIBRILU  ! WANNE IRIN NAHARI NE UBANGIJINA YA UMARCE NI DA YINSA  ?

Sai (Jibrilu (A. S)) yace; 

" BA SUKA AKE NUFI BA, SAI DAI YANA UMARTARKA NE IDAN KAYI HARAMA DOMIN SALLAH TO, KA 'DAGA HANNAYENKA YAYIN DA KAYI KABBARA DA LAKACIN DA KAYI RUKU'I DA LOKACIN DA KA 'DAGO KANKA DAGA RUKU'I DA LOKACIN DA KAKE YIN SUJADAH 
, DOMIN HAKAN SHINE SALLARMU DA KUMA SALLAR MALA'IKUN DAKE SAMAN BAKWAI.  KUMA KOWANNE ABU YANA DA ADO (OINTMENT), KUMA ADON SALLAH SHINE 'DAGA HANNAYE YAYIN KOWACCE KABBARA. "

(Mustadrak Haakeem, J:2, Sh:537)

            ABIN LURA

Cikin sallar za muga an nuna mana cewa Annabi (S. A. W. W) na yin zama bayan sujadah biyu kafin miqewa zuwa raka'a ta gaba. 

Sannan kuma cikin riwaya ta biyu an nuna mana yadda Jibril (A. S) ya koyar da Manzon Allah (S. A. W. W)  cewa a kowacce kabbara ta cikin sallah ana daga hannaye. 

To, yanzu wa kuka ga yake yin irin wannan sallah?  Duk wanda kuka ga yana siffanta irin wannan sallah, to, shine mai yin sallah irin wacce Annabi (S. A. W. W) ya koyar. 

Sannan kuma duk wadanda ka kalli sallarsu sai kaga ba irin wannan sallar suke yi ba, to, kace musu ba irin sallar Annabi (S. A. W. W) suke yi ba.

ASHE DAI DA GASKE NE AN CANJA YADDA AKE  SALLAH   !

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.

         (08137925034)

7th March, 2021 /  24th Rajab, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post