YADDA SHARI'AR SU SAYYID ZAKZAKY TA KAYA YAU A BABBAR KOTUN JIHAR KADUNA:

 

              8 March, 2021


Salaam yan uwa masu daraja yau ma mun sake dawowa babbar kotun jihar Kaduna don kawo muku abubuwan da ke gidan a wannan Shari'a.

Yanzu haka Lauyoyin Malam sun halara karkashin jagorancin Femi Falana SAN.

Lauyoyin Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Barista Bayero Dari.

Shaida na farko shi ne DSP Bala Abdullahi.

Bala Abdullahi ya ci gaba da bayyana cewa an sanya shi ya yi bincike kan laifukan da suka shafi Kisan kai, tare hanya da kuma wasu laifukan da ake zargin yan Shia sun aikata a Zaria sakamakon tare wa Buratai hanya. Ya ce kwamandan Nigerian Army Depot Zaria ne mai suna Brig Gen CG Musa ya kawo wa yan sanda qara.

Bala Abdullahi ya bayyana cewa a shekarar 2015  yana da muqamin Inspector ne. Kuma yana karkashin ofishin bincike na rundunar yan sanda ta Kaduna. Amma yanzu yana Hedikwatar yan sanda ta Abuja.

 Ya ci gaba da cewa an kawo musu abubuwan da aka kama wadannan mutane da su ka hada da bindiga, kakin soji, gwafa, sim cards da sauransu.

Bala Abdullahi ya bayyana cewa shi ya dauki bayanan mutane 3 daga cikin 253. Ya ce dukkan su kuma sun tabbatar da cewa su yan Shia ne na IMN.

Ya ce bingigogi 10 da wuqaqe 64 da sauransu.

Bayero Dari ya roki kotu ta ba da dama a shigo da makaman da ake magana domin Bala Abdullahi ya gani ko sune wadanda ya ke magana a kai. 

Kotu ta ba da dama an shigo da makaman. An tambayi Bala Abdullahi ko su ne ya ke magana a kai? Ya tabbatar wa da Kotu cewa su ne makaman.

CanKotu ta nemi Bala Abdullahi da ya lissafa makaman

Kwari da baka 14

Motorola Radio message 29

Ya lissafa takobi 68

Kakin soji 4

Bindiga kirar gida 10

Bala Abdullahi ya bayyana cewa wadannan kayan ne suka gabatar a babbar kotun jihar Kaduna. Don haka Bayero Dari ya roki kotu da ta karbe su a matsayin hujja. 

Sai dai Femi Falana SAN ya qi amincewa da wannan roko. Ya bayyana cewa ba yan sanda ba ne suka karbo makaman. Sojoji ne suka kawo musu kamar yadda shaida ya bayyana da bakinsa. Ya ce dole sai an yi abin da doka ta ce.

Lauyan Malama ya bayyana goyon bayansa kan abin da Femi Falana SAN ya fada.

Bayero Dari ya nemi kotu ta yi watsi da abin da Femi Falana SAN ya fada. Ya ce a doka duk wani abu da jami'in tsaro ya gabatar a gaban kotu ana karbarsa a matsayin hujja.

Ya bayyana cewa ba wata takarda ko wani abu da aka gabatar wa da Kotu na cewa ga wanda ya kawo makaman. Don haka ana iya nemo su don biyan wata bukatar.

Falana SAN ya ce dole idan an kaiwa kotu evidence a rubuta mata kafin a karbo su. Idan takardar da suka aikawa kotu har ta ba su wadannan makaman? Ai suna hannun kotu ne tunda ana gabatar da su a wata kotu.

 KOTU TA TSAYA ANA JIRAN ZUWAN FEMI FALANA(SAN)

Yanzu haka kotu ta dakata,ana jiran Femi Falana ya iso daga Lagos, sakamakon matsalar jirgin sama da ya samu,amma dai yana hanyar sa ta shigowa Kaduna din.

Kotu ta amince da makaman a matsayin shaida.

Alkali ya bayyana cewa wanda ya gabatar da wadannan makaman a wannan kotu wato Bala Abdullahi yana da ikon gabatar da su. Saboda shi aka mika wa yan uwa 253 tare da makaman.

Saboda haka ba ruwan kotu da gabatar da su da aka yi a wata kotu. Domin waccan kotun ta kammala aikin.

Falana SAN ya a tambayi Bala Abdullahi ko mutum nawa ka dauki bayanan su? Ya ce mutane 3.

Ko kai aka kawo wa Malam Zakzaky da matarsa? Ba ni aka mika wa su ba.

Kana da labarin cewa dukkan wadanda ake zargi su 253 ana zargin su ne da kashe soja?

Ya eh  haka ne

Ko kana da labarin kotu ta sallamesu su dukkan su?

Ya ce bai sani ba.

Ko har yanzu ana ci gaba da shari'ar? Ya ce bai sani ba.

Ko Brig Gen CG Musa ya fada maka a hannun wa ya sami wadannan makaman? Ya ce bai fada masa ba.

Falana SAN ya fada wa Bala Abdullahi cewa ya fadin a daya kotun cewa makaman sau biyu aka ba shi su. Na farko an kawosu ranar 14/12/2015 na biyu kuma ranar 27/12/2015 me ya sa bai fada wa kotu haka ba?

Ya ce ko zai babbance wadanda aka kawo musu ranar 14/12/2015? Ya ce duka makaman.

Falana SAN ya sake tambayarsa to wadanne ne suka karbo a Zaria? Ya ce a tambayi na sama da shi. Falana SAN ya ce shi yaka tambaya. Amma ba ya ce bai sani ba.

Falana SAN ya a tambayi Bala Abdullahi cewa wacce shaida ya ke so kotu ta karba? Wadda ya ba da a baya sannan yanzu ya canza ko kuma wadda yake badawa yau? Ya ce wadda ya ke badawa yau.

Falana SAN ya ce a shekarar 2016 ka shaidawa kotu cewa kwari da baka 19 ne, yau kuma ka ce 14.

Bala Abdullahi ya ce bai san in da ya sami takardar da yake karantawa ba. Falana SAN ya ce ina karantawa ne daga abin da ka shaida wa kotu a bayananka. Don haka Falana SAN ya nemi gabatar da wannan littafi a a matsayin shaida.

Bayero Dari ya roki kotu da ka da ta karbi wannan littafi a matsayin shaida. Ya ce dole ne a gabatar fa takardar ta ainihi ba photo copy ba.

Falana SAN ya bayyana cewa ba wata takarda ba ce da aka samo a wani wuri.  Takardar babbar kotun jihar Kaduna ne. Don haka kayanta ne. Saboda haka ya ce ta amshi abin da a matsayin shaida.

Waya ta za ta iya mutuwa a kowane lokaci daga yanzu. Saboda ina fada da matsalar batiri.

Kuma yanzu Hon Muhammad Ali zai shigo. Idan an ji shiru wayar ta mutu ne

Alkali ya amince da takardar a matsayin shaida

Falana SAN ya ce yau ka fada wa kotu cewa kun gabatar da bingigogi 10 kirar gida. Alhali a baya ka shaida wa kotu a 21/11/2016 cewa bindigogin 8 ne. Ya aka yi aka sami kari? Ya ce ba zai iya tunawa ba

Ya ce ya tuna sun aika da bindigogi 2 zuwa Legas don a gwada su. Shi ne aka dawo da su yanzu suka zama 10

Falana SAN ya ce yaushe suka je Lagos yin gwaji? Ya ce 2015. Yaushe aka dawo da bindigogin? Ya ce 2016.

Me ya sa da ka zo ba da shaida a 2018 ba ka hada bindigogin ka ba? Ya ce bai sani ba.

Falana SAN ya tambayi Bala Abdullahi cewa bayan wadannan makaman da kuka kawo akwai sauran abubuwan da ba ku kawo ba? Ya ce eh akwai. Suna ina? Ya ce bai sani ba.

Falana SAN a baya ka gabatar da sim cards 1200 yanzu suna ina? Ya ce bai sani ba.

Kotu ta sallami Bala Abdullahi.

Kotu ta kira dan sanda Muhammad Shehu.

Kotu ta kira dan sanda Muhammad Shehu.

Ya bayyana kotu cewa sunan sa Muhammad Shehu kuma shine Mataimakin kwamishinan (DC) yan sanda ne a jihar Edo. Amma a 2015 AC ne a Zaria Area Command.

Daga Wakilinmu da yayi hidimar hada muku rahoton.

~Auwal M Tukur

Note: Wannan shine abinda ya samu Kenan, sakamakon rashin chaji da Wakilinmu da ke kawo labarin Kai tsaye daga kotun.


Insha Allah idan samu sauran bayanin zamu kawo muku...

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post