D
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HUJJAR DA IMAM ALI (A. S) YA DOGARA DA ITA WAJEN RASHIN YAQAR MASU FASHIN KHALIFANCI
Wasu mutane da dama basu san hadisar Ghadeer ba ballantana ma su san cewa Annabi (S. A. W. W) ya nasabta Imam Ali (A. S) a matsayin Khalifah bayansa. Saboda hakane ma har suke kafawa mutane hujja cewa da akwai wannan magana me yasa shi Imam Ali (A. S) yayi mubaya'a ga wadanda suka gabace shi bai yaqe su ba ?
A duk lokacin da aka bijiro da irin wannan tambaya sai kan mutum ya kulle wajen bada amsar wannan tambaya matuqar bai yi karatu ko kuma ji daga bakin wadanda sukayi karatu na gaskiya ba.
Abu na farko da za mu kawo anan shine hadisin Ghadeer cikin littafin Sunnah don sanar da mutane abinda basu sani ba ko suke kokwanto a kansa sakamakon rashin ganin hadisin (in Arabic text) wanda hakan yasa suke gani kamar tatsuniya ce ake kawo musu.
HADISIN GHADEER
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
926- حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ حَكِيمٍ الْأَوْدِيُّ ، أَنْبَأَنَا شَرِيكٌ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ وَهْبٍ ، وَعَنْ زَيْدِ بْنِ يُثَيْعٍ ، قَالَا : نَشَدَ عَلِيٌّ النَّاسَ فِي الرَّحَبَةِ : مَنْ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ إِلَّا قَامَ ، قَالَ : فَقَامَ مِنْ قِبَلِ سَعِيدٍ سِتَّةٌ ، وَمِنْ قِبَلِ زَيْدٍ سِتَّةٌ ، فَشَهِدُوا أَنَّهُمْ سَمِعُوا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ لِعَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ : " أَلَيْسَ اللَّهُ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ ؟ " ، قَالُوا : بَلَى ، قَالَ : " اللَّهُمَّ مَنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلَاهُ ، اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالَاهُ ، وَعَادِ مَنْ عَادَاهُ " ، حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ حَكِيمٍ ، أَنْبَأَنَا شَرِيكٌ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ عَمْرٍو ذِي مُرٍّ ، بِمِثْلِ حَدِيثِ أَبِي إِسْحَاقَ ، يَعْنِي عَنْ سَعِيدٍ وَزَيْدٍ وَزَادَ فِيهِ : " وَانْصُرْ مَنْ نَصَرَهُ ، وَاخْذُلْ مَنْ خَذَلَهُ " ، حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنَا عَلِيٌّ ، أخبرنا شَرِيكٌ ، عَنِ الْأَعْمَشِ ، عَنْ حَبِيبِ بْنِ أَبِي ثَابِتٍ ، عَنْ أَبِي الطُّفَيْلِ ، عَنْ زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، مِثْلَهُ .
Abdullahi ya bamu labari, Aliyu Bn Hakeem Al-Audiy ya bamu labari, Sharik ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Sa'eed Bn Wahbin, kuma daga Zaid Bn Yuthai'u suka ce : " Aliyu ya hada mutane da Allah a Haraba : " WANDA YAJI MANZON ALLAH (S. A. W. W) YANA FADA A RANAR GHADEER-KHUUM YA MIQE ." Yace,
Sai mutane shida daga bangaren Sa'eed suka miqe, daga bangaren Zaid ma mutane shida, suka shaida cewa lalle su sun ji Manzon Allah (S. A. W. W) yana fada ga Ali (R. A) ranar Ghadeer-Khuum :
" ASHE BA ALLAH NE MAFI CANCANTA GA MUMINAI BA ?"
Suka ce, "Na'am " Yace;
" YAA ALLAH DUK WANDA NA KASANCE SHUGABANSA NE TO, ALIYU SHUGABANSA NE. YAA ALLAH KA JIBINCI WANDA YA JIBINCE SHI, KAYI ADAWA DA WANDA YAYI ADAWA DASHI. "
Abdullahi ya bamu labari, Aliyu Bn Hakeem ya bamu labari, Shareek ya bamu labari daga baban Ishaq daga Amruu Zee-Murri da misalin irin hadisin baban Ishaq, yana nufi daga Sa'eed da Zaid, sai kuma ya qara a cikinsa;
" KA TAIMAKI WANDA YA TAIMAKE SHI, KA TABAR DA WANDA YA TABAR DASHI !"
Abdullahi ya bamu labari, Aliyu ya bamu labari, Shareek ya bamu labari daga A'amashi, daga Habeeb Bn Abiy Thaabit, daga baban 'Dufail, daga Zaid Bn Arqaam, daga Annabi (S. A. W. W), misalinsa ."
(MUSNAD-AHMAD, HADISI MAI LAMBA 926)
Wannan nassi ne da aka kawo mana a aikace (practically) ba ishara ba.
Saboda haka duk wanda ke son qaryata wannan hadisi dole ya zama ya kawo nassin da ya warware wannan a ilimance.
BAI'AR IMAM ALI (A. S) GA MAGABATANSA
Lalle an kawo nassosi cikin dukkan bangarori biyu Shi'ah da Sunnah cewa Imam Ali (A. S) yayi mubaya'a ga wadannan masu qwacen halifanci daga ma'abotansa (A. S). Hakan kuwa ba wai yana nuna yardarsa ne halifancin nasu ba, a'a, lalura ce kawai wacce ta kasance yin hakan shine mafi maslahar addinin muslimci a wancan lokacin.
Kuma za mu gaskata hakan ta yadda ya kasance shine mai gyara musu wasu abubuwa da suke yi na ba daidai ba, domin su buqatarsu kawai ita ce mulkin, tunda kuwa suka samu ba su da matsala.
HUJJARSA (A. S) TA ZAMA A QARQASHINSU
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
677- حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنِي مُحَمَّدُ بْنُ أَبِي بَكْرٍ الْمُقَدَّمِيُّ ، حَدَّثَنَا فُضَيْلُ بْنُ سُلَيْمَانَ يَعْنِي النُّمَيْرِيَّ ، حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ أَبِي يَحْيَى ، عَنْ إِيَاسِ بْنِ عَمْرٍو الْأَسْلَمِيِّ ، عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " إِنَّهُ سَيَكُونُ بَعْدِي اخْتِلَافٌ ، أَوْ أَمْرٌ ، فَإِنْ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَكُونَ السِّلْمَ ، فَافْعَلْ " .
Abdullahi ya bamu labari, Muhammad Bn Abubakar Al-Muqdamiy ya bani labari, Fudhail Bn Sulaiman (yana nufin Numair) ya bamu labari, Muhammad Bn Abiy Yahya ya bamu labari daga Iyaasin Bn Amruu Al-Aslamiy, daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (R. A) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" LALLE DA SANNU SASSABAWA ZAI AUKU A BAYANA KO KUMA WASU AL'AMRA, IDAN DAI AKWAI YIWUWAR A SAMAR DA ZAMAN LAFIYA TO, KA AIKATA ."
(MUSNAD-AHMAD, HADISI MAI LAMBA 677)
Kamar yadda kowa yasan Imam Ali (A. S) da yin biyayya ga Manzon Allah (S. A. W. W) sai yaga abinda ya bashi labari ya auku, kuma ya ba shi shawara kan wannan al'amari, sai ya duba yaga abinda zai fi zama maslahar al'umma a waccan lokaci shine yayi haquri ya barsu su aikata abinda zukatansu suka riya musu, domin shiryar dasu ba a hannunsa yake ba.
Abinda ke kansa shine ya nuna musu gaskiya in da mai rabo ya cikinsu ya bi ta ya rabauta. Wannan dalili yasa bai yi Mubaya'a da farko ba har sai bayan wata shida (6) kamar yadda aka kawo.
Amma kafin lokacin sai da yayi iya qoqarinsa na nuna musu gaskiya ko za su bita, amma suka nuna ba ita ce a gabansu ba.
Abinda zai qara tabbatar maka da cewa mulkin ne kawai ya sallamar musu shine, bayan mutuwar Umar da kuma yin komitin Shura, sun buqace shi kan cewa ya yarda bisa sharadin zai bi sunnar Abubakar da Umar a matsayin qa'ida ta samun Khalifancinsa, sai yace musu;
" ZANYI AIKI DA LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABINSA DA KUMA TAWA FAHINTAR. "
Kan hakane suka qara hana shi suka bawa Usman bisa wannan sharadin, domin shima 'DAN INA DA MULKI NE !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
31st March, 2021/ 18th Sha'aban, 1442.