SALLAR DA AKE YI YANZU BA IRIN TA ANNABI (S. A. W. W) BACE IN JI ANAS BN MALIK !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADA KU ZARGI 'YAN SHI'AH DON SUN CE AN CANCANZA AL'AMRAN ADDINI
Adalci shine mutum ya karbi gaskiya ko daga bakin wa ta fito, amma ba zai zama yiwa kai adalci ba ace komai gaskiyar maganar mutum matuqar ta saba fahinta ko abinda mutum ya sani yace ba daidai bane.
Duk wanda ke karatu tare da nazari da kuma neman sanin gaskiya zai riqa cin karo da abubuwan da ake aikata su cikin muslimci da sunan ibada, amma kuma sunyi hannun riga da yadda Annabi (S. A. W. W) da Sahabbansa ke yi zamanin Manzon Allah (S. A. W. W).
MISALI
Zakkah,
Rabon gado da kuma Azumi.
Taqaitawa nayi a matsayin babin misali, amma har sallah ma ba yadda Annabi (S. A. W. W) ya koyar damu ake yi ba.
Kada kuce 'yan Shi'ah ne kadai ke irin wannan magana , a'a ba haka bane, domin har manya daga cikin Sahabbai sun bayyana haka.
Bari mu kawo misali da wani Sahabi duk kafa hujja. Ka shi kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
11757- حَدَّثَنَا زِيَادُ بْنُ الرَّبِيعِ أَبُو خِدَاشٍ الْيُحْمَدِيُّ , قَالَ : سَمِعْتُ أَبَا عِمْرَانَ الْجَوْنِيَّ ، يَقُولُ : سَمِعْتُ أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ ، يَقُولُ : " مَا أَعْرِفُ شَيْئًا الْيَوْمَ مِمَّا كُنَّا عَلَيْهِ عَلَى عَهْدِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ : قُلْنَا لَهُ : فَأَيْنَ الصَّلَاةُ ؟ ، قَالَ : أَوَلَمْ تَصْنَعُوا فِي الصَّلَاةِ مَا قَدْ عَلِمْتُمْ ؟ " .
۞۞۞۞۞۞
Ziyad Bn Rabi'i baban Khidashin Al-Yuhmadiy ya bamu labari yace, na ji baban Imrana Al-Jauniy yana cewa ; Na ji Anas Bn Malik yana cewa,
" BAN SAN WANI ABU A WANNAN ZAMANI WANDA AKE KANSA A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W. W) ."
(Abu Imrana) yace, sai muka ce masa; " TO, INA SALLAH TAKE? " Yace,
" YANZU (kun ga) ANA AIKATA WANI ABU WANDA KUKA SANI CIKIN SALLAH ?"
(MUSNAD-AHMAD)
Sallar Annabi (S. A. W. W) ya kasance yana yin basmala a farkon kowacce surah cikin sallolinsa, sannan kuma yana yin kabbarori bayan idar da sallah har sai wadanda ke waje ma sun ji sautin.
Ya zo cikin Sahihul-Bukhari kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
الذكر بعد الصلاة
-842- حدثنا إسحق بن نصر قال: حدثنا عبد الرزاق قال: أخبرنا ابن جريج قال: أخبرني عمرو: أن أبا معبد، مولى ابن عباس، أخبره: أن ابن عباس رضي الله عنهما أخبره:
أن رفع الصوت بالذكر، حين ينصرف الناس من المكتوبة، كان على عهد النبي صلى الله عليه وسلم
Ishaq Bn Nasri ya bamu labari yace, Abdul-Razaq ya bamu labari yace, Ibn Juraij ya bamu labari yace, Amru ya bani labari daga baban Ma'abadin bawan Ibn Abbas yace, ya ba shi labari cewa Ibn Abbas ya ba shi labari cewa;
" LALLE 'DAUKAKA SAUTI NA AMBATON ALLAH YAYIN DA MUTANE SUKA JUYO DAGA SALLOLI NA WAJIBAI YA KASANCE A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W. W) ."
Riwaya ta gaba kuma tana cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
843-وقال ابن عباس: كنت أعلم إذا إنصرفوا بذلك إذا سمعت كنت أعرف انقضاء صلاة النبي صلى االله عليه وسلم بالتكبير
Ibn Abbas (R. A) yace,
" NA KASANCE INA SANI IDAN SUKA JUYO DAGA HAKA (yin zikiri) IDAN NAJI INA GANE CEWA ANNABI (S. A. W. W) YA IDAR DA SALLAH TA HANYAR YIN KABBARORI
"
(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUS-SALAT, BABUN ZIKR BA'ADA SALAT, HADISI MAI LAMBA 842-843)
TAMBAYA
Tsakani da Allah mutane 40% suna karanta basmala kafin karanta kowacce surah cikin sallolinsu ?
Ko kuma idan sun idar da sallah suna yin kabbarori ?
Yanzu mutane ba shan ruwa suke yi kafin faruwar rana ba ?
Ashe Imam Malik bai kawo mana cikin Muwaddah nasa cewa Umar Bn Khaddab da Usman Bn Affan sai sunyi sallar magriba suke shan ruwa ba?
Ba Allah (T) ya hana yin azumi a halin tafiya ba ? Har ma Annabi (S. A. W. W) yake cewa,
" BA YA DAGA CIKIN AYYUKAN ALKHAIRI YIN AZUMI A HALIN TAFIYA ." Ba?
حدثنا آدم: حدثنا شعبة: حدثنا محمد بن عبد الرحمن الأنصاري قال: سمعت محمد بن عمرو بن الحسن بن علي، عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهم قال:
كان رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر، فرأى زحاما ورجلا قد ظلل عليه، فقال: (ما هذا) .........
^ليس من البر الصوم في السفر^
Bukhari yace, Adam ya bamu labari, Shu'ubatu ya bamu labari , Muhammad Bn Abdurrahman Al-Ansari ya bamu labari yace, na ji Muhammad Bn Amruu Bn Hassan Bn Aliyu ,daga Jabir Bn Abdullahi (R. A) yace; Manzon Allah (S. A.W.W) yana cikin wata tafiya sai yaga Zihaam da wani mutum sun shiga qarqashin wata bishiya (saboda zafin rana), sai yace,
" MWNENE WANNAN ?"
Aka ce masa, " Mai Azumi ne ." Sai yace;
" AI BA YA DAGA CIKIN AIKIN ALKAHIRI YIN AZUMI A HALIN TAFIYA ."
(BUKHARI, KITABUS-SIYAAM, BABUN LIMAN ZULLILA ALAIHI WASH-TADDAT HARRA, HADISI MAI LAMBA :1946)
Yanzu me mutane suke yi ? Kace min azuminsu suke yi cikin halin tafiya domin suna gudun ramuwa. Amma da shike sallar qasaru ba ramawa ake yi ba sai suna dabbaqawa.
ALLAH YA QARA HASKAKA MANA SHIRIYA.
#FREE SAYYID ZAKZAKY (H) !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
5th March, 2021/ 22nd Rajab, 1442.
Ya kamata a sanya sunan wanda yayi maganar a cikin sharhin gundarin maganar
ReplyDelete