WA KE ZAGAYE MATANSA HUDU DA JIMA'I CIKIN DARE 'DAYA ???

 




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  


WAI ANNABI NA ZAGAYE DUKKAN MATANSA CIKIN DARE DA WANKA 'DAYA


Nakan rasa hikima ko darasi da malaman sunnah ke qoqarin sanar da mutane cikin hadisai na cin zarafin Manzon Allah (S. A. W. W), domin cikin kowacce magana ko qissa akwai darusan da ake fitarwa cikinsa. 


A iya tunani ma irin na 'yan Adam za kaga bai kamata ace wani abu na sirri wanda Allah ya boye shi don mutunta bayinsa ace kuma su suke fita suna bayyanar dashi ba. TO, idan kuwa hakane ya za ayi ace Annabi (S. A. W. W) zai kasance yana bayyanar da wani sirri nasa wanda ya shafi tsakaninsa da matansa  ? Ko kuma dai qarya ake masa don cin mutumcinsa  ?


Wata riwaya na karanta kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


11726- حَدَّثَنَا هُشَيْمٌ ، عَنْ حُمَيْدٍ ، عَنْ أَنَسٍ ، أَنّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ " يَطُوفُ عَلَى جَمِيعِ نِسَائِهِ فِي لَيْلَةٍ بِغُسْلٍ وَاحِدٍ " .


Shuhaim ya bamu labari daga Humaid, daga Anas  cewa, lalle Annabi (S. A. W. W) ya kasance;  " YANA KEWAYAWA AKAN DUKKAN MATANSA (da Jima'i) CIKIN DARE DA WANKA 'DAYA  ."



(MUSNAD-AHMAD)



Ba za muce wani abu kan wannan hadisi ba tukunna har sai mun koma cikin wani hadisi muji me Annabi (S. A. W. W) ke fada. 


An kawo cikin Sahihul-Muslim , kuma Imam Nawawi ya kawo cikin Riyadus-Saliheen nasa cikin Rubutu kan ladubba a qarqashin Babi mai magana kan boye sirri kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



2 - بابُ حفظ السِّر


حديث رقم :683


وعن أَبي سعيد الخدري رضي الله عنه قَالَ:


قَالَ رسول الله صلى الله عليه وسلم: (إنَّ مِنْ أشَرِّ النَّاسِ عِنْدَ اللهِ مَنْزِلَةً يَوْمَ القِيَامَةِ الرَّجُلَ يُفْضِي إِلَى الْمَرْأةِ وتُفْضِي إِلَيْهِ، ثُمَّ يَنْشُرُ سِرَّهَا) رواه مسلم


Daga Abu Sa'idul-Khudriy   (R. A) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" YANA DAGA CIKIN MAFI SHARRIN MASAUKI WAJEN ALLAH RANAR ALQIYAMA MUTUMIN DA ZAI BIYA BUQATARSA DA MATARSA, ITA MA TA BIYA BUQATARTA DA SHI SANNAN YAZO YANA BUDE SIRRINTA  ."


(KITABUL-ADAAB, BABUN HIFZUS-SIRRI , HADISI NA :683)


To, yanzu anan za mu iya bude baki mu yiwa Anas tambaya kamar haka :-


(1)- Shin, Annabi (S. A. W. W) ne ya ba ka labari ko kuma kana binsa cikin dare ne kana leqa shi cikin dakunan matansa  ?


(2)- Dan Allah me kake son koyar damu ko darasin da kake son fitarwa cikin wannan magana taka  ?


(3)- Ko kuma so kake ka nuna mana cewa wannan hadisi wanda ya la'anci masu bayyanar da sirrin da ya auku tsakaninsu da matansu ya hau kansa (S. A. W. W)  ?


(4)- Ku kuma malaman sunnah da kuka san yadda ake yin ladabi har kuna fitar da Babi cikin rubutunku na musamman da ke nuna ladabi kuna nufin ku kun fi Annabi (S. A. W. W) ladabi ne wanda shi ba ya yi ku kuma kuke koyar da mutane  ?


(5)- Ko kuma kuna nufin hakan shine nuna soyayyarku gare shi (S. A. W. W)  ?


MU DAI MUN BARRANTA DAGA IRIN WADANNAN KALAMAI NAKU  !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


1st March, 2021/  18th Rajab, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post