TASIRIN KALAMAN MAHAIFA AKAN YARANSU !!!

 



( ALLAH YAYI MAKI ALBARKA)


 Inajin dadi sosan gaske, idan naji wani ya fada wannan kalmar akaina wallahi. Ko nayi ana mani addu'o'i na gari.


Iyaye!!! sune mutane na farko da furucin bakinsu yakeda matukar tasiri ga yaransu, na alkhairi ko na sharri, yiwa yara fatan alkhairi ko furuci na alkhairi, yana tasirantarsu ne har karshen rayuwarsu, wanda idan akayi akasin hakan garesu zaya iya yi musu tasiri, kamar yadda na alkhairi yakeyi.


     A yanzu iyaye na sakaci da hakan ga yaransu sosan gaske, wanda rashin hakan Yana taimakawa wurin lalacewan tarbiyyar yaro.


   Naje  gidansu wata kawata aka ce mani ta tafi kitso, sai na bukaci da a rakani inda taje din don inaso mu hadu ne, aka saka kanenta ya rakani har gidan, gidane wanda sukeda Yan mata babu maza a gidan, wanda zasukai su uku zuwa hudu, kuma kowace a cikinsu ta isa aure, amma abinda ya bani mamaki yadda na ga mahaifiyarsu tana ma'amalantar su,  muna nan zaune ina jira a gama mata kitso, sai mahaifiyar ta fito daga daki hannunta dauke da yar karamar kanwarsu, ta cewa daya daga cikin Yan matan " ke dan ubanki anshi yar nan in dora girki" sai yarinyar tace " kam wallahi ban dauka, ki goyata Mana, kita saka mutane aiki suna hutawa" nayi mamakin kalaman yarinyar akan mahaifiyar ta, kuma sai naji mahaifiyar tace "to" kawai, sai ta sake fadar irin abinda ta fadawa wannan ta farko, amma akan wata daban, Aa itama still tace bazata ansaba, sai na fara mamaki sosai ina kallonsu kawai, budar bakin mahaifiyar sai naji ta fara zaginsu, tana tsine masu albarka kamar ba itace ta haifesu ba, suna tayi mata guni ( magana kasa kasa) kamar suna rama zagin.


Nidai haka muka baro gidan cike da mamakin yadda suke rayuwa, bayan mun fito sai nake tambayar kawata, wai wannan matar kuwa ita ta haifa yaran Nan, sai take ce mani, eh mana duka yaranta ne, kuma acikinsu akwai wa'yanda sunyi aure an sakosu ne, shiyasa suka dawo gida, to mahaifinsu baya hanawa, sai tace mani, ai shima haka yake musu duka hada matar, so na nuna mata mamakina sosai akan hakan, sai take ce mani ai nan banga komi ba, idan naji suna zagin mahaifiyar itama tana tsine masu, tana bazasu gama da duniya lafiya ba, sai abin ya bani mamaki,   sai na sake tambayar ta to meye saka suke haka, take ce mani itadai tun basukai haka ba, haka tasan halin mahaifiyar ko yaro na waje yadan yi mata laifi, saita fara tsine masa albarka.


Dana nutsu saina fahinci, tasirin wa'yannan miyagun kalaman data keyi musu ne take gani tun yanzu.

Fadar kalma mai kyau akan yaro yana taimakawa tarbiyyar sa.


Yaku iyaye ku sani cewa yaran da Allah ya baku, amana ne gareku, kuma zaya tambayeku yadda kuka gudanar da tarbiyyar abinda ya baku, ku kyautata kalamanku da lafuzzanku akan yaranku, domin yana tasirantarsu ne.


Allah ya bamu ikon sauke nauyin daya dora mana.


✍️ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post