Tabbas Dole Al'ummar Garin Shinkafi Su Kara Godiya Ga Allah (T), Sakamakon Ludufi da Baiwar Da Allah (t) Yayi Musu Na Tsamo Wasu Gwarazan Matasa Masu Matukar Gwarzan taka Wajen Ganin Sun Kwatowa Garin su da Al'ummar da Suke Rayuwa 'Yanci Ko hakan Zai sa su Shiga ko wane Irin Hali !!
Kuma Sadaukai Masu Sadaukarwa, Basa Tunanen Kudin su ko Ince Dukiyar Su Wajen Ganin Sun Fitar da Ita Wajen Ganin Sun Biya Bukatun Na kusa ko na nesa Daga Cikin Al'ummar da Suke Rayuwa a tare dasu, Basu Dauki Kansu Wasu ba, Sun Dauki kayan su na Al'umma ne, Kuma Damuwar su Shi ne dame Al'umma Suka damu, Kuma Mi Al'umma Ke so?? Domin Ganin Sunyi iya Kokarin Su Wajen Ganin Sun Yi Abunda yadace ga Al'ummar Nan, Indai Abunda Al'ummar ke So baisabawa Hurumin Addini ba.
, Hazikan Jarumai ne marasa Girman Kai, Duk da Acewa A Al'adar Da Adam Mafi Yawanmu Idan munsamu Rufin Assirin duniya (Kudi) to zamu Ringa Yiwa na Kasanmu Dagawa Da Cin magani da Nuna fifiko Tare da Girman Kai, Amma Su Sun Baranta da Wadannan ababen Duk da Rufin Assirin da suke Tattare Dashi....
SHIN WAI WADANNAN MATASAN SU WAYE??
LATE ALHJ JAMILU JAGABA |
Matashi Na Farko Wanda Alkalami na Bazai Bani Damar Sanin Iya Alkhairy da yayiba A Rayuwa ga Al'ummar Garin Shinkafi, Wanda Mafi Akasarin Mutanen Shinkafi ke Masa Lakabi da {MARGYAYI JAMILU JAGABA } Allah Ya Jikanshi ya Gafarta Masa Ya yafe kura kuransa , ya Haskaka makwancin sa Alfarmar manzo da iyalan Gidansa Tsarkaka....
Tabbas jamilu yayi Abunda Har Jokokin Mutanen Shinkafi Bazasu Manta Dashi ba Acikin Kankanen Lokaci da Damar da Allah ya Bashi, Wanda Shi ne Matashi Na Farko da Ganarwa Shinkafi Tarihin da har yau Babin Farko ake na karantashi, Tabbas Tarihin jamilu da Kyuatar shi, tare da Ayyukkan Alkhairy Kaje Shinkafi Kayi Tambaya Koda Kankanen Yaro ne Dan Shekara Biyar Zai Sanar Dakai waye JAGABA Acikin mintuna biyu, In Allah yaso Zanyi Rubutu akan sa da Izinin Allah (T).
Allah ka Kara Haske a kabarin Jagaba, ka yaye kura-kuransa Ka Albarkaci Zuriyarsa , ka yaye mishi talauchin Lahira, ka Ni'imantashi da ni'imar da kakeyiwa bayinka mangarka Alfarmar Manzon Allah (sa)
WAYE MATASHI NA BIYU ??
ALHJ AHMED BALA MATHS |
Matashi Na biyu Jajirtaccen Dan Kasuwar Nan Kuma Jarumin namiji Gwarzo Wanda yake debe Mana kewar jamilu Bayan Bashi (ALHJ AHMED BALA MATHS) Wanda Akafi sani da MATHS COMMUNICATION Wanda Shi ne Famunan Sakatare na Kungiyar UNION COMMUNICATION na Garin Shinkafi, Kungiya ce ta Matasan Yan Kasuwa Masu Harka kayayyakin Wuta (Electronic) da Jarumin ke jagoranta...
Na Zabi inyi Wannan Rubutun ne akan Wannan Matashi Haikan Saboda Ganin Yadda Naga Al'ummar Garin Shinkafi nata Murnar Fitowar 'Yan uwanmu da Ke tsare, Sai Naga Nima nayi Wannan Rubutu na Taya Wadannan Jarumai biyu Murna Cikar Burin su a Irin Wannan Lokaci.
Duk da Banso Kawo Aikin Wannan matashin ba Amma Dole Tasa Sai na Kawo Kadan Daga Cikin Abunda nasani Daga Taimako na Bangaren sana'arsa kadai, Basai munkoma Wani fanni ba..
ALHJ MATHS:- Shi ne Jarumin Matashi Kwara Daya , da ya Shiga ya fita ba dare ba Rana tare da Rubuce-Rubuce Dakai da Kawo ta kowace Siga Da Sadaukar da kak kudi Lokaci dss Akan Ganin ansaki Matasan mu da Aka Rufe a Gidan yarin Gusau kusan kwanakki Fiye da 60, Kuma Har Allah yasa Yayi Nasara Anbasu belin su Kamar Yadda kuke Ganin shi tare dasu a Photon dake kasa
Muna Godiya Mutanen Shinkafi da Wannan Karamci Da kayyi mana
Tabbas tun Bankare Secondry ba nake Ganin mafi Yawan matasan Shinkafi na Amfana da Arzikin Wannan Dan Kasuwar Ta Dalili nai Nasan Ya Samar wa mutum Fiye da 30 talatin Computer K.Y.C Ta Kamfanonin Glo, mtn, dss Domin Su nemawa Kai Rufin Assiri.
A Lokacin Bani Daga Ciki Amma na Amfana da Wadanda Aka Baiwa Wadannan Ababen Domin A Lokacin ne Mafara sana'ar layuka ta karkashin Wadanda yayiwa innuwa Wanda Nima Ina tare da Yaro 10 Wadanda Suke ci ta karkashin Wannan Inuwar, Inda zanbasu layuka da memory sai sun siyar Zasu Kawo man Nima naje na siyo Wasu a saukake su Samu Nima insamu Kafin yanayi ya canza na Chanji Rayuwa, Kamar Yadda Photon kasa ke Bayyana Muku hakika
ALHJ MATHS:- Na tuna Wani Lokaci Satin Karamar Sallah a Garin Shinkafi ga Azumi ga Zafin Rana, gashi Gwamnati Bata Biya Ma'aikata albashi ba sai Ana Jajibirin Karamar Sallah ga Mutane Dawainiyya tayi musu yawa Kowa son yake ya Debo kudi yayiwa iyalinshi Hidima Domin Ganin Sunyi Sallah Cikin Farin Ciki Amma ba dama Saboda Banki Guda ne kadai a Shinkafi Kuma ga tururuwar Al'umma, Cunkuso yayiwa, Gashi ba kudi ga bankin, Wasuma Garin Suke Bari Sutafi makwabta Domin Ciro kudi, Kuma Lokacin ga Karancin P.O.S a Garin, Alhaj Ahmed Math na Ganin Haka ya je ya Siyo P.O.S ya Ajiye a Dayan Shagon Shi kowa yazo Ya Debi kudi Batare da Shamaki ba, Cikin Iyawar Allah Sai Gashi Duk mafi yawa Sun Samu biyan bukatun su Cikin Gaggawa, Mutanen Gari Suka Ta saka mishi Albarka, tare Da Fatan Alkhairy a Shekarun Baya.
Alhj Muna Godiya da Wannan...
Acikin Alkhairan Zahiri da Alhaj keyi Mana Shi ne Tursasawa Dole Sai kamfani M.T.N Ya Kawo Mana Sola A Garin Shinkafi A Lokacin da bamuda Wuta Wadda akafi Dani Da LUMOS SOLA A Lokacin a farashi Mai Sauki Domin bazata Kasawa Dubu 12,000 da Wani Abu ba har sakata, Kuma Alhamd Mutanen Shinkafi sun Amfana da Wannan Taimako harzuwa yanzu da Abun duniya ya canza Inda take kusan Dubu 30'000 da Wani Abu.
Muna Godiya Alhj MATHS
A Karshe-Karshen Nan Alhj Yaga yadda mutane keshan wuya akan NATIONAL I. D CARD, da Yawan Mutanen Garin Shinkafi sai Sufi sati biyu Suna Zuwa Basu Samu ba ba Yaro ba tsoho ba maza ba Mata, Bayan anyima sai Kayita Yan zagaye Da Dawowa Wajen karba dss, Alhj Maths ya Kawo Sabuwar Computer ya Samu matasa Ankoyar dasu Aikin yanzu Ananan anayi A Shagon sa nanan Bakin kasuwa a Saukake Sha yanzu magani yanzu Basai anwalar Dakai ba, Cikin mutumci da karamci.. Inda Al'ummar Shinkafi Keta Sam barka Da Addu'ar Allah Sa Kafi Haka .
Allah kasawa kasuwancin ka Albarka Alfarmar Manzon Allah (s) kasa Riba ta Ta Rubanya Uwa sau Adadin da harshe Bai iya lissafi, Allah ka haskaka zukatanku Yagafarwa Zunubban ku, ya Yalwata Arzikin ku, illahy ya Kara Tsawon Rai da Karin Karfin Arziki Alfarmar Manzon Allah da Iyalan Gidansa Tsarkaka.
@Alkalamin Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999