@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HUJJAR DA ABUBUKAR YA FAKE DA ITA SUKA ZALUNCI SAYYIDAH FATIMAH (S. A)
Don gujewa tsawaita rubutu ba za muyi doguwar shimfida ba, amma dai da wannan hujja aka dogara wajen hanawa Sayyidah Fatimah (S. A) gadon mahaifinta (S. A. W. W), wanda yin hakan yaci karo da ayar Alqur'ani mai tsarki.
Domin fayyace wannan al'amari za muyi nazari cikin wadannan hadisai da kuma ayar da za mu kawo cikin wannan rubutu insha Allahu.
Ya zo cikin Sahihul-Bukhari cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
(3092)- حدثنا عبد العزيز بن عبد الله: حدثنا إبراهيم بن سعد، عن صالح، عن ابن شهاب قال: أخبرني عروة بن الزبير: أن عائشة أم
المؤمنين رضي الله عنها أخبرته:
أن فاطمة عليها السلام، ابنة رسول الله صلى الله عليه وسلم: سألت أبا بكر الصديق بعد وفاة رسول الله صلى الله عليه وسلم: أن يقسم لها ميراثها، ما ترك رسول الله صلى الله عليه وسلم مما أفاء الله عليه، فقال أبو بكر: إن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: (لا نورث، ما تركنا صدقة)
Abdul-Azeez Bn Abdullahi ya bamu labari, Ibrahim Bn Sa'ad ya bamu labari daga Salihu, daga Ibn Shihaab yace : Urwata Bn Zubair ya bani labari yace : Ummul-muminina A'isha (R. A) ta bashi labari : " Lalle Fadimatu (A. S) 'Yar Manzon Allah (S. A. W. W) ta tambayi Abubakar Siddiq bayan wafatin Manzon Allah (S. A. W. W) cewa ya bata gadonta na abinda Manzon Allah (S. A. W. W) ya bari na daga Ganimar da Allah ya ba shi. Sai Abubakar yace; " Lalle Manzon Allah (S. A. W. W) yace, " MU BA A GADONMU, ABINDA MUKA BARI SADAQA CE ."
Cikin hadisi na 3093 dake cikin littafin wanda suka tsallake shi cikin wannan application dana ciro A'isha ta cigaba da cewa;
" Sai Fadimatu 'yar Manzon Allah (S. A. W. W) tayi fushi, ta qauracewa Abubakar, kuma bata gushe ba tana me qaurace masa har tayi wafati. Kuma ta rayu ne bayan Manzon Allah (S. A. W. W) da wata shida (6). (A'isha) Tace;
" Fadimatu ta kasance tana tambayar Abubakar rabonta ne na daga abinda Manzon Allah (S. A. W. W) ya bari na daga Khaibar da Fadak da kuma sadaqa a Madinah, sai Abubakarya yaqi ya bata. Sai yace;
" NI BAN KASANCE MAI BARIN WANI ABU DA NAGA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YANA AIKATAWA BA FACE NAYI AIKI DASHI , DOMIN NI INA JIN TSORO KADA NA KARKACE IN HAR NA BAR WANI ABU DAGA AL'AMARINSA ." Amma ita sadaqa (Ganima) ta Madinah Umar ya damqata zuwa ga Aliyu da Abbas . Amma Khaibar da Fadak Umar ya riqe su yace; " SU WADANNAN SADAQA CE TA MANZON ALLAH (S. A. W. W) . SUN KASANCE HAQQOQINSA NE WADANDA AKE SARRAFA SU DA NA'IBANSA, KUMA AL'AMARINSU YANA GA WANDA YA JAGORANCI AL'AMARI NE ." Yace;
" KUMA AKAN HAKA SUKE HAR ZUWA YAU !"
NAZARI
----------------
Anya idan wannan magana ta Abubakar gaskiya ce ya akayi ita Sayyidah Fatimah (S. A) bata sani ba, sannan babu wani wanda yasan maganar sai shi ? Ko da shike cikin wani hadisin sunce Umar ya tuhumi Imam Ali (A. S) da Abbas cewa tsakaninsu da Allah basu san wannan magana cewa wai Annabi (S. A. W. W) yace ba a gadonsu ba ? Wai sai suka ce eh sun sani.
Idan kuwa gaskiya ne sun sani, me yasa basu hana Fatimah furta wannan zancen ba? Ko kuma suna nufi tayi abinta ne kai tsaye ba tare da iznin mijinta ba ?
Idan kuma suka ce sun miqa Ganima zuwa ga Aliyu da Abbas ne saboda haqqi ne na iyalan gidansa (A. S), to, me yasa Fatimah bata daga cikin wadanda aka bawa wannan Ganima ? Alhali Allah (T) na cewa;
" مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ........ (٧)
" ABINDA ALLAH YA SANYA SHI GANIMA GA MANZONSA NA DAGA MUTANEN QAUYUKA, TO, NA ALLAH NE KUMA NA MANZONSA NE, DA KUMA MAKUSANTA DA MARAYU DA MISKINAI .........
(SURATUL-HASHRI:7)
To, idan ana maganar makusanta kuwa akwai wanda yafi Sayyidah Fatimah ce wajen babanta (S. A. W. W) ?
Shi kuma wannan hadisi da za mu kawo yana da tsaho sosai, amma mun tafi qarshensa mun kwafo muku maganar, mai son ganin cikakkiyar maganar sai ya duba shi a hadisi mai lamba 3094. Ga shi kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
(3094)-........، ثم توفي الله أبا بكر، فكنت أنا ولي أبي بكر، فقبضتها سنتين من إمارتي، أعمل فيها بما عمل رسول الله صلى الله عليه وسلم وما عمل فيها أبو بكر، والله يعلم: إني فيها لصادق بار راشد تابع للحق، ثم جئتماني تكلماني، وكلمتكما واحدة وأمركما واحد، جئتني يا عباس تسألني نصيبك من ابن أخيك، وجاءني هذا - يريد عليا - يريد نصيب امرأته من أبيها، فقلت لكما: إن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: (لا نورث، ما تركنا صدقة)...............
.....Umar yace, " Sai Abubakar ya rasu, sai na kasance nine majibincin Abubakar, na karbe su (Khaibar da Fadak) na tsahon shekaru biyu daga mulkina, ina yin aiki cikinsu da irin abinda Manzon Allah (S. A. W. W) yayi aiki dasu, da kuma abinda Abubakar yayi aiki a cikinsu.
Allah yana sani, lalle ni mai gaskiya ne a cikinsu kuma kubutacce shiryayye mai bin gaskiya, sannan kuma kuzo min kuna yimin magana kuma dukkanku kalmarku iri daya ? Al'amranku iri daya ?
Kai ka zo min yaa Abbas kana tambayata rabonka na daga dan dan'uwanka (you are asking me about your share from what your brother's son left). Wannan ma yazo min (yana nufin Aliyu) yana buqatar kason matarsa na daga mahaifinta (he claims about the share of his wife from what her father left. )
To, ina ce muku: Lalle Manzon Allah (S. A. W. W) yace; " MU BA A GADONMU, DUK ABINDA MUKA BARI SADAQA CE......"
(SAHIHUL-BUKHARI, KITABU FARDHIL-KHUMUSI, HADISI NA 3092, 3093, 3094)
NAZARI
------------------
Dan Allah idan dai har wannan magana da aka kawo cikin wannan hadisi na 3094 gaskiya ne, su Abbas da Imam Ali (A. S) suka qara dawowa wajen Umar suna bidar haqqinsu a wajensa alhali tun zamanin Abubakar an tabbatar musu da cewa su Annabawa (S. A. W. W) ba a gadonsu ?
Suna nufin Abbas da Imam Ali (A. S) suna saba abinda Annabi (S. A. W. W) yayi magana a kansu kenan ?
Sannan kuma ta yaya ma Abbas zai nemi gadon abinda Manzon Allah (S. A. W. W) ya bari alhali yana da 'ya a raye ?
Maganar gaskiya ma dai ita ce, wadannan hadisai na qarya ne, domin an qirqirosu ne kawai don a hanawa 'yar Manzon Allah (S. A. W. W) cin gadon mahaifinta. Sannan kuma hadisan sunci karo da ayar Alqur'ani dake cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنۡهُ أَوۡ كَثُرَۚ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا ." ( ٧ )
" ('YA'YA) MAZA NA DA KASO NA DAGA ABINDA IYAYE BIYU DA DANGI SUKA BARI , KUMA SU MA ('YA'YA) MATA NA DA KASO NA DAGA ABINDA IYAYE DA MAKUSANTA SUKA BARI, KOMAI QANQANTARSA KUMA KOMAI YAWANSA. RABO NE YANKAKKE (daga Allah) ."
(SURATUL-NISA'I :7)
Kuma cikin wannan aya babu inda akace banda 'ya'yan Annabawa kuma babu inda aka ce iyaye Annabawa ba su daga cikin wadanda ake gadonsu.
Saboda haka ba za a iya gamsar damu ba dole sai an kawo aya wacce tace ba a gadon iyaye Annabawa kamar yadda aka nuna 'ya'ya na gadon mahaifansu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
27th March, 2021/ 14th Sha'aban, 1442.