TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) A TAQAICE
Salsalar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) :
Tarihi mafi inganci da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da kansa, ya faxi cewa asali iyayensa sun fito ne daga Magrib (Moroko); Daga nan suka zo birnin Shingixi na tsohuwar daular qasar Mali, amma yanzu birnin na Shingixi mai tsohon tarihi yana qasar Mauritaniya ne, daga garin Shingixi kakanninsa suka yo qaura zuwa birnin Mabruk da ke qasar Mali, daga nan kuma suka zauna a birnin Timbuktu, daga birnin Tumbuktu ne kuma suka taho wannan qasa Nijeriya cikin qarni na 12. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 09 zuwa 11).
Nasabarsa :
KU LATSA HOTON NAN DAKE DOMIN KARANTA LABARAI SAHIHAI CIKIN HARSHEN HAUSA>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
Salsala ko nasabar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta jero ne kamar haka; Shaikh Ibraheem xan Ya’aqub, xan Aliyu, xan Muhammad Tajuddeen, xan Liman Hussain Batoronke, shi Liman Hussain Bafulatani ne daga qabilar Toronkawa wanda ya zo qasar Hausa daga Mali a zamanin Shehu Usman bin Fodiye, inda ya zama babban limami a garin da yake zaune a yankin Sakkwato. Daga bisani sai xansa Malam Tajuddeen wanda almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne ya biyo tawagar wakilin Xanfodiye na Zazzau, wato Sarkin Zazzau Malam Musa suka taho Zariya tare dan ya riqa karantarwa. Mafi yawan tarihin da ake rubutawa na salsalar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) yana tuqewa ne akan Liman Hussain, wataqil don gudun tsawaitawa, domin jerin nasabar Shaikh (H) tana tuqewa ne ga Imami na biyu cikin limaman shiriya na Ahlul-Bait (AS), wato jikan Manzon Allah (S) Imam Hassan Al-Mujtaba bin Aliy bin Abiy-Talib (AS), xan Sayyida Fatimah Azzahra (SA), wan Imam Hussain shahidin Karbala (AS).
Zamu cigaba...
Daga wakilinmu:
Auwal M Tukur
Daga littafin da Cibiyar wallafa jawaban Sheikh Zakzaky ta buga Mai suna "Sheikh Zakzaky Ikon Allah".
KU LATSA HOTON NAN DAKE DOMIN KARANTA LABARAI SAHIHAI CIKIN HARSHEN HAUSA>>>>>>>>>>>>>>>>>>>