@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
GASKIYA BAKU QADDARAWA ALLAH HAQQIN GADDARARSA BA
Wani lokaci idan kaji magana sai ka zaci kamar daga bakin mashayin Giya ta fito yayin da yake cikin maye, amma kuma sai kaji ana cewa ai maganar gaskiya ce, ko da kuwa ya sabawa hankali da shari'a.
Mu kanyi qoqarin zaqulo irin wadannan maganganu ne don mu tsabtace addininmu na muslimci wanda wasu suka najastar dashi tare dayi masa baqin fenti a idon maqiyanmu, amma sai kaji wasu na qoqarin yin suka ga masu wannan yunquri bisa jahilci (Jahlan).
Wannan magana ta zo ne cikin littafin Bukhairi wanda ya inganta shi da kansa kuma wasu suka yarda da maganarsa alhali sun san shi ba ma'asumi bane ballantana ace ba zaiyi kuskure ba.
Ga dai abinda riwayar ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
"وتقول هل من مزيد" 30
(4849)- حدثنا محمد بن موسى القطان: حدثنا أبو سفيان الحميري سعيد بن يحيى بن مهدي: حدثنا عوف، عن محمد، عن أبي هريرة رفعه، وأكثر ما كان يوقفه أبو سفيان:
(يقال لجهنم: هل امتلأت، وتقول: هل من مزيد، فيضع الرب تبارك وتعالى قدمه عليها، فتقول: قط قط)
Bukhari ya riwaito cewa, Muhammad Bn Musa Al-Quddaniy ya bamu labari: Auf ya bamu labari daga Muhammad, daga Abu Hurairata ya daukaka shi, kuma mafi yawancin abinda ke tsayar dashi shine Abu Sufyan: Ana cewa Jahannamah : " SHIN, KIN CIKA KUWA ?" Kuma tana cewa : " SHIN, AKWAI QARI NE ?"
SAI UBANGIJI WANDA GIRMA DA 'DAUKAKA YA TABBATA A GARE SHI YA SANYA DIDDIGENSA A KANKA, SAI TACE; " NA CIKA NA CIKA (I am fully enough). "
(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUL-TAFSIR, BABIN KUMA SAI TACE, SHIN AKWAI QARI NE? HADISI MAI LAMBA 4849)
Duk da cewa sun inganta hadisin, amma kwata-kwata ya sabawa shari'a kuma ya ci karo da ayar Alqur'ani mai tsarki.
Sun kawo wannan hadisi ne qarqashin wannan aya,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
يَوۡمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمۡتَلَأۡتِ وَتَقُولُ هَلۡ مِن مَّزِيدٖ ٠٣
" RANAR DA ZA MU CEWA JAHANNAMA, SHIN KIN CIKA ? SAI TACE, " SHIN, AKWAI WANI QARI NE ?"
(SURATUL-QAAF:30)
Shine suka ce za ayi ta qara mata amma ba za ta cika ba har sai Allah ya sanya diddigenSa a cikinta sannan ta cika.
(1)- Idan muka nazarci wannan hadisi za muga cewa haqiqa suna sadarwa Allah gangar jiki ne irin ta dan Adam, sannan ana nuna masa gazawa wajen ikonsa. Wannan hadisi ya ci karo da wannan aya dake cewa :
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" إِنَّمَآ أَمۡرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيۡـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ ." ( ٢٨)
" ABIN SANI SHI AL'AMARINSA IDAN YAYI NUFIN ABU SAI YACE MASA KASANCE, SAI YA KASANCE (abinda yake so) ."
(SURATUL-YASEEN:82)
To, yanzu wanda ke da wannan iko na komai ya kasance abinda yake so sannan ace ba shi da ikon cika wuta sai ya sanya diddigenSa ?
(2)- Allah (T) na cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" وَلَوۡ شِئۡنَا لَأٓتَيۡنَا كُلَّ نَفۡسٍ هُدَىٰهَا وَلَٰكِنۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ مِنِّي لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ." (٣١ )
" DA ACE MUN SO DA MUN BAIWA KOWACCE RAI SHIRIYARTA, SAI DAI MAGANA CE TA GASKIYA TA TABBATA GARE NI, LALLE ZAN CIKA JAHANNAMAH DAGA ALJANNU DA MUTANE BAKI 'DAYA !"
(SURATUL-SAJDAH:13)
Abinda ya tabbata daga Allah shine, alqawarinSa ne cewa zai cika Jahannama ne da Aljannu da Mutane, amma shi Bukhari yana qaryata Shi ne cewa a'a, sai ya sanya diddigensa kafin ta cika.
TAMBAYA
- Shin, wannan ayar an soketa ne ko kuma a ina ne Allah yace ya saba wannan alqawari nasa ?
- Ko kuma bangaren jikin Allah cikamakon wuta tunda kun ba shi jiki ?
HABA, A RIQA MAGANA DA TUNANI MANA, DOMIN FA DA AKWAI MASU HANKALI CIKIN MASU KARANTA LITTAFANKU.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
23rd March, 2021/ 10th Sha'aban, 1442.