Da sunan Ubangiji Madaukaki, wanda yai mana arzikin samun Mujaddadi mataimakin Mahdi. Tsira da amincin Allah su kara wanzuwa ga Manzon Allah (S) da Ahlul baitinsa masu tsarki har zuwa ga shugaban zamani, Imamul Hujja (A.F).
Ranar 15 ga Sha'aban din kowace shekara takan zo wa muminai ma'abota wilaya da farinciki na musamman.
Kasancewar a irin ranar ce aka haifi limamin zamani, Imamul Mahdi (A.F) tare da jagoranmu, mujaddadin karninmu kuma babba daga cikin kwamandojin mai zamani Imam Almuntazar Almahdi, wato Sharafuddin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H).
Mafi alherin ni'ima da Allah ya yi wa Biladi Sudan ita ce samuwar Mujaddadin addini Sayyid Ibrahim Zakzaky (H).Saboda haka al'amarin raya Nisfu Sha'aban ba kawai mujarradin taya juna murna da farinciki ba ne, haka kuma ba zai wadatar ba ya zamo kawai an gabatar da shagulgulan bukukuwa ba, girman abin ya zarce haka.
Wadannan bai wuce wani bangare karami ba na abin da ya kamaci muminai ma'abota gwagwarmaya a irin wannan rana.
Alkiblar tunani da hangenmu a kan jagora wajibi ne a daidai wannan rana ya samu garanbawul. Mu dubi yadda lokaci ke kurewa; mu kalli kuma yadda mu a kashin kanmu muka riki aikinmu. Yaya muke da jagoranmu ta fuskar wilaya da taimakonsa? Yaya bunkasar fikirarmu da sabunta tunanukanmu a kan al'amarin jagora? Wane shiri muke na fuskantar kalubalen da suke tunkaro mu a kullum a kan ayyukanmu? Yaya alakarmu da junanmu wajen cicciba aikin da muke dauke da shi har mu cim ma hadafinmu? Mu tuna aikinmu kai tsaye yana da mikakkiyar alaka ne da Sahibul Asr (A.F). Munasabar Nisfu Sha'aban lokaci ne na kakkabe wasu baragurbin tunani a kwakwalenmu na cewar muna da tabbacin wanzuwar rayuwar jagora (H) zuwa wani lokaci mai tsawo.
Ko tunanin ba sai mun matsa wajen sa'ayin kubutar jagora ba, saboda Allah yana tare da shi da makamantan wadannan tunanin. Mu waiga baya mana mu gani yadda aka yi wa sashen bayin Allah da mujaddadai.
Waki'ar Karbala babbar ishara ce da za ta tsinkayar da mu zuwa ga shiga taitayi da karatun ta natsu. Dole mu yi jifa da makamantan wadannan tunanin wadanda suke mana shinge kuma suke dakushe mana kumaji da muhimmantar da ayyukanmu yadda ya kamata.
Muna sane cewa, a kasar Iraki, mummunan al'amari ya faru da almajiran Sayyid Sadr sakamakon sakacinsu da wargi; inda Allah ya dauke Sayyid Sadr saboda watsi da al'amarinsa da almajiransa suka yi. Sayyida Sadr kuma a fili yake cewa Mujaddadi ne. Mu dauki kanmu mu dora a wannan mizani, shin mu ma muna da tabbacin kubuta daga irin wannan kalubale? Ayyukanmu sun kai matsayin da za su gamsar da mu tsirarmu daga makamancin abin da ya faru da almajiran Sayyid Sadr a Iraki? Wane dalili ne na zahiri ko boyayye ya samar mana da yakini har muka samu tunanin jagoranmu lallai sai ya kai wani adadin shekaru nan gaba?
Dama wata aba ce da take da sauri da saukin kubucewa, sannan tana da wahalar dawowa. Mu yi amfani da damarmu tun yanzu kafin kubucewarta. Lokaci kayyadajje ne kuma kurarre ne, da zarar ya wuce ba tare da an yi amfani da shi yadda ya kamata ba, ba shakka wasa da shi ba zai haifar da da mai ido ba.
Don haka wajibi ne mu sarrafa tunaninmu da damar da muka samu wajen lizimtar wazifar da ke kanmu, kuma mu tabbatar mun sauke ta.
*SHEKARA SABA'IN FA BA KWANA SABA'IN BANE,BAMU TAIMAKA DA KOMAI BA KUMA WAI MUNE QASHIN BAYA.*
Wannan rubutun sadaukarwane zuwaga Ruhin Shaheed muhseen Jafar Minna.
*JASAZ SHUHADA*
*31th march, 2021*