SHIN ZAI YI NASARA KUWA?
Babu labarin da ke tashe a arewacin Nijeriya a halin yanzu irin batun Muqabalar Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da gungun makiya guda uku, Wahabiyawa, Tijjanawa da kuma gwamnatin Nijeriya ta cikin rigar gwamnatin jahar Kano.
Wadannan gungun makiya da ke kokarin ganin bayan wannan bawan Allah da kawar da sautinsa daga samuwa, kowa a cikinsu yana da dalilan kiyayyarsa ga Shaikh Abduljabbar.
Su dai Wahabiyawa babban ginshikin gaba da kiyayyarsu ga Abduljabbar ita ce batun Akida, shi Bawahabiye a duk inda yake a duniya ba abin da yaki jinin ya ji irin ambaton Ahlul-Bait ko kokarin nuna darajoji ko Kususiyyar Aliyu Bin Abiy Talib (As).
Wahabiyawa ba su da jimirin jurewa Ass akan nuna daraja ko wani fifiko na Sarkin Muminai, Qanin Manzon Allah (S), Surukin Annabi na gaske, Mataimaki (Deputyn) Annabi (S), Khalifan Manzon Allah na hakika, wanda Musulunci ya kafu da kaifin takobinsa!
Wahabiyawa ba su da matsala da Abduljabbar in ba wannan ba. Kenan ba wani abin da za a gamsar da su da shi in ba kawar musu da Abduljabbar daga samuwa, ko kulle musu bakinsa da kowane irin matakin karfi aka yi ba.
Su ba zancen hujja ce ta dame su ba, ba kuma wata hujja suke nema kan abin da yake yi ba, kawai buri da fatansu shi ne kawai a share shi daga samuwa a duniya, ko akalla a shafe muryarsa daga amon da take yi zuwa kunnuwan mutane.
Abin tambaya anan shi ne, shin Wahabiyawan za su cimma burinsu?
Amsar wannan tambayar abu ne mai sauki, musamman in mutum ya sa tabaran hangen nesa ya kyallara idon basirarsa a ciki.
Wahabiyawa dai su ke da mulkin duniya a halin yanzu, kashi 97 na gwamnatocin kasashen musulmi na duniya Wahabiyawa da Wahabiyanci ke rike da su.
A gefe guda, algungumar da ta haifi Wahabiyanci kuma take daukar nauyinsa Saudi Arabia sam ba ta raina fada da duk wani mai kiran sunan Aliyu Bin Abiy Talib (As), komai karantar mutum, kuma ko a wane lungu yake a duniya, indai labari ya ke mata cewa yana ambaton Aliy (As), to za ta dauki nauyin kashe ko dala biliyan nawa ne don a kawar mata da shi.
Masu ganin Issuen Abduljabbar a matsayin wani karamin batu ne da ya shafi gwamnatin Kano da Wahabiyawan Kano lallai sun goce a tunaninsu, wallahi ba komai Ganduje ke aiwatarwa ba in banda umarnin Aali-Sa'ud, shi kwangila ce yake yi, wacce zai samu sakamakon ta in ya cimma nasarar abin da aka nema ya yi.
A gefe na biyu, Dukkanin gwamnatocin kafircin duniya Wahabiyanci ne zabinsu a cikin musulmi, Ingila, Amurka, Faransa, da uwa uba Isra'ila, ba wadanda suka dauka abokan tafiyarsu irin Wahabiyawa, ta cikin Wahabiyanci suke cimma duk wani buri nasu akan Musulmi da Musulunci.
To shin a ganinku za su bari Abduljabbar ya yi nasara akan yaransu? Wannan abu ne mai kamar wuya!!
Bangare na Biyu cikin masu nuna kiyayya ga Abduljabbar sune wasu kaso mai tsoka na Tijjanawa, ya isa abin mamaki a duniya a ce Badarike yana fada da Abduljabbar, to amma babu abin mamaki a ciki, domin su suna fada da Abduljabbar ne saboda ya tattaba musu babbar Alkiblarsu, ya sha sukan mujaddadin darikar ta Tijjaniya Shaikh Ibrahim Inyas Al-Khaulakhiy a lokutan baya cikin rikicinsu da wasu masu sukarsa a 'yan Tijjaniyar.
Wannan batu na sukar Shaikh Inyas da ma wasu manyan malaman Tijjaniya da Shaikh Abduljabbar ya yi a baya, ya sanya tsana da tsananin kiyayya daga mafi yawan Tijjanawa gare shi, yayin da wasu suka kure maleji wajan yaki da shi.
A nan, za mu lura da bambancin manufa (Interest), ko ban hannun makahon da ke tsakanin manufofi biyu na fada da Abduljabbar, a yayin da Wahabiya ke fada da shi akan Akida, su Tijjanawa suna fada da shi ne akan cin zarafin magabatansu, duk da cewa dama bisa al'ada gaba takan rika fadada har wasu abubuwan da ba su ne tushe ba su shigo, amma dai wancan dalilin shi ne jigon adawarsu gare shi.
Kamar yadda aka sani, a duk fadin duniya in ka cire Wahabiyawa, to 'yan Dariku ne Musulmi na biyu a yawan adadi da karfin fada a ji, domin su ma suna da gwamnatoci da kuma kaso mai kauri na biya a kusan dukkan kasashen musulmi na duniya.
A Nijeriya da kuma musamman birnin Kano, 'yan 'Dariqu suna da karfin fada a ji, wanda zai yi wuya a kaucewa biyan buƙatar su kai tsaye.
Wannan shi kansa wata katanga ce da ke gaban Shaikh Abduljabbar mai wuyar hudawa a kokarinsa na samun nasara.
Bangare na uku a wannan fagen daga shi ne bangaren Gwamnatin Nijeriya, wacce ita ce uwar gwamnatin jahar Kano, kuma gwamnatin Kanon ba komai take yi ba illa zartar da muradunta, (duk da cewa da wuya mutane su gane wannan ikirarin, domin su da Kemarar ido suke kallon abubuwan da ke faruwa ba da Kemarar hankali ba).
Gwamnatin Nijeriya shediyar gwamnati ce da ta tsani addinin Muslunci na gaskiya, tunda aka kafa kasar shekaru 60 zuwa yanzu, tsarin kasar yana hidima ne ga kafarci da zalunci, duk abin da yake shiriya ne ko hakikanin addini gwamnatin Nijeriya ba ta son shi, kai tana ma yaki da shi ne, kawai tana fakewa cikin rigar addini a fagen hidimtawa addinin da iyayen gijinta na yammacin Turai suka yarda da shi (wato Wahabiyanci).
Shaikh Abduljabbar ya cika dukkanin rukunnai na sabawa gwamnatin Nijeriya, don haka dole ta yake shi ta cikin rigar malamai, domin na farko dai ba ya zuwa Bara a wajanta, wato ba ya zuwa neman alfarma kulliyaumin, wanda hakan babban barazana ne ga gwamnati.
Ita gwamnatin Nijeriya ba ta yarda wani malamin addini mai jama'a ya dogara da kansa ba, wannan babbar barazana ce gareta, dole ka zamo yaronta, in ba haka ba kuwa sai ta yi maganinka!
Na biyu, Shaikh Abduljabbar yana karantar da hakikanin addini, wanda lallai hakan babbar barazana ce ga gwamnati, ita gwamnati ta fi goyon bayan a tarawa mutane bola da shara da tarkacen tsiya a kwakwalensu a matsayin addini.
Don haka, kare Manzon Allah (S) da Abduljabbar ke yi mugun laifi ne ga gwamnati, ta fi son a tafi akan dangantawa Manzon Allah (S) mugayen siffofi, a ce yana kware al'aurarsa akan bola a bakin hanya ya yi fitsari a tsaye.
A ce yana zuwan matar aure ya kwanta ya yi bacci akan cinyarta!
A ce mata suna zuwa yana kebewa da su yana biya musu bukata!
A ce yana ganin matar aure ya yi sha'awarta al'aurarsa ta motsa ya shiga gida ya tara da matarsa.
A ce yana Sallah da maniyyi a jikin tufafinsa.
A ce yana tsotsar al'aurar jikansa namiji a cikin bakinsa.
A ce mata 'yan rawar Qoroso suna cashewa a cikin gidansa yana zaune yana kallo yana kyalkyala dariya!
A ce Shedan yana yaudararsa har a cikin Sallolin farillarsa!
A ce ya taba bautawa gumaka ya yi sujjada a gare su.
A ce ya taba cusa shirka a cikin Alkur'ani, ya ce Lata da Uzza da Manata duk Alloli ne, har sai da Allah ya shafe shirkar da ya cuso din!
A ce bai da kyakkyawar Hadda ta Alkur'ani, yana karatun Sallah yana bata karatu Sahabbai suna gyara masa.
A ce bai da ƙwaƙwalwa da kyakkyawan tunani, Ummaru ya fi shi sanin matakin da ya kamata a dauka.
Da dimbin ire-iren waɗannan shirmataku.
Bisa la'akari da waɗannan katangu uku da ke kewaye da Shaikh Abduljabbar, anya kuna ganin akwai fata na cewa Abduljabbar zai gamsar da mutanen nan a wannan mukabala da za a yi, balle har ya iya kubuta daga tarkonsu???
Ni dai na san ba yadda za a yi Abduljabbar ya gamsar da su komai dubbun hujjarsa, balle su ba shi dama ko su kyale shi ya ci gaba da daukaka wannan sauti nasa, ita kanta shirya mukabalar daya ne daga matakan cimma burin dakile shi a bisa hujja!!
LOKACI ALKALI NE!!
Baban Fatimah.