Sahabi Umar Ne Ya Haramta Auren Mutu'ah ba Annabi (s) ba, Inji Sahihul Muslim !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MALAMAN SUNNAH SUN ZARGU DA SARQA (CHAIN) A WUYANSU 


Hausawa suka ce qarya fure take ba ta 'ya'ya, duk abinda aka gina shi da qarya sunansa rusasshe abin rushewa. Sannan a duk lokacin da aka qirqiri qarya sai an qara qirqiro wasu qarerayin don a kare wannan qaryar. 


Yiwa Annabi (S. A. W. W) qarya dai ba farau bane kuma ba qarau bane, shi yasa ma yace duk wanda yayi masa qarya ya tanadi gurin zamana a wuta.


Mu munce muku halascin Mutu'ah nanan daram tun daga zamanin Manzon Allah (S. A. W. W) zuwa wannan lokaci da muke ciki, domin duk abinda ya halasta a zamaninsa kuma ya bar duniya bai haramta shi ba, to, halascinsa na nan har tashin alqiyama. 


RIWAYOYI CIKIN SAHIHUL-MUSLIM 


Littafin Muslim na daga cikin ingantattun littafai shida (6) wadanda kuke lissafowa, kuma shine ma na biyu bayan Sahihul-Bukhari a girman inganci. To, ga abinda yazo cikinsa game da haramcin auren Mutu'ah. Ku biyo mu don ganewa da idanuwanku. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



(1)- وحدثنا الحسن الحلواني حدثنا عبد الرزاق أخبرنا بن جريج قال قال عطاء قدم جابر بن عبد الله معتمرا فجئناه في منزله فسأله القوم عن أشياء ثم ذكروا المتعة فقال نعم استمتعنا على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم وأبي بكر وعمر


Hassan Al-Hawaniy ya bamu labari, Abdurrazaq ya bamu labari, Ibn Juraij ya bamu labari yace;  Adda'u yace, " Jabir Bn Abdullahi ya zo Umra sai muka je masa a masaukinsa, sai jama'ah suka tambaye shi kan abubuwa (da dama),  sa'an nan suka ambaci Mutu'ah, sai yace; 


" NA'AM, MUNYI MUTU'AH A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ZAMANIN ABUBAKAR DA UMAR  ."


Tambaya anan ita ce, idan kuwa sunyi Mutu'ah a zamanin Abubakar da Umar, to, ina matsayin cewa Annabi (S. A. W. W) ne ya haramta  ?


Kuna tabbatar mana ne cewa su Abubakar da Umar masu aikata abinda Annabi (S. A. W. W) yayi hani a kansa ne  ?



(2)- حدثني محمد بن رافع حدثنا عبد الرزاق أخبرنا بن جريج أخبرني أبو الزبير قال سمعت جابر بن عبد الله يقول كنا نستمتع بالقبضة من التمر والدقيق الأيام على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم وأبي بكر حتى نهى عنه عمر في شأن عمرو بن حريث



Muhammad Bn Rafi'i ya bamu labari, Abdurrazaq ya bamu labari, Ibn Juraij ya bamu labari, baban Zubair ya bani labari yace;  " Na ji Jabir Bn Abdullahi (R. A) yana cewa; 


" MUN KASANCE MUNA YIN MUTU'AH DA DAMQI NA DABINO DA 'DAN WANI ABU (Daqeeq) NA WASU KWANAKI A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ABUBAKAR, HAR UMAR YAYI HANI GAME DA ITA KAN WANI AL'AMARI GA AMRUU BN HAREETH  ."


Cikin wannan hadisin ma an qara tabbatar mana cewa har zamanin Abubakar ana yi, a zamanin Umar ma ana yi,  sai daga baya ya haramta kan al'amarin Amruu Bn Hareeth. 


Kunga Umar din ma ba ya haramta saboda Annabi (S. A. W. W) ne ya haramta ba, kuma bai ce haka ba. Shi dai ya haramta ne saboda abinda ya faru game da wani mutum. 



(3)- حدثنا حامد بن عمر البكراوي حدثنا عبد الواحد يعني بن زياد عن عاصم عن أبي نضرة قال كنت عند جابر بن عبد الله فأتاه آت فقال بن عباس وابن الزبير اختلفا في المتعتين فقال جابر فعلناهما مع رسول الله صلى الله عليه وسلم ثم نهانا عنهما عمر فلم نعد لهما



Haamid Bn Umar Al-Bakaraawiy ya bamu labari, Abdulwaaheed ya bamu labari ana nufin Ibn Ziyaad, daga Aseem, daga baban Nadhrata yace, " Mun kasance a wajen Jabir Abdullahi (R. A), sai wani mai zuwa yazo masa, sai Ibn Abbas (R. A) da Ibn Zubair suka ce, sunyi sabani cikin mutu'o'i biyu (mutu'ar aure da Mutu'ar aikin Hajji) , sai Jabir yace; 


" MUN AIKATA SU (dukka biyun)  TARE DA MANZON ALLAH (S. A. W. W), SANNAN UMAR YA HANA MU GAME DA SU, (tun daga lokacin) BAMU QARA KOMA MUSU BA. "


(SAHIHUL-MUSLIM, KITABUN NIKHAH) 


Na'am, muna sane da riwayoyin da aka kawo cewa wai Annabi (S. A. W. W)  ne ya haramta, amma tunda akwai tufka -da-warwara cikin littafan da kuma ce duk abinda yazo cikinsu ya inganta dole muyi muku tambayoyi kamar haka :-


(1)-  Me yasa aka sami riwayoyi masu cin karo da juna cikin wadannan littafan da kuka inganta su  ?


(2)- Idan kuka ce wadanda aka kawo cewa Annabi (S. A. W. W) ya haramta suka inganta, to,  wacce hujja ce ta ingantar da hakan  ?


(3)- Idan kuka ce riwayoyin Muslim ne masu cewa Umar ne ya haramta basu inganta ba, to,  me yasa basu inganta ba alhali sun zo cikin ingantaccen littafi  ?


YA KAMATA KU WARWARE MANA WANNAN AL'AMARI  !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


17th March, 2021/  4th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post