@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HAR HIRAR ANNABI (S. A. W. W) MUKE YI KAN HAKA IN JI ANAS BN MALIK
A duk lokacin da muka yi magana kan irin wadannan cin zarafi dake cikin ingantattun littattafan Sunnah sai wasu suce mana wai menene amfani ko fa'idar kawo irin wannan maganganu ?
Amsar da za mu ba su da ma kai mai irin wannan fahinta ita ce, shin, menene fa'idar rubuta su cikin littafai aka inganta su har ake karantar dasu?
Duk wani abinda kaga marubuci (Author) ya rubuta shi cikin littafinsa akwai babban abinda yake son isarwa ko da kuwa kai baka fahinci hakan ba. Duk abinda kaga an rubuta shi babu manufa, to, ka kira wannan marubucin Mahaukaci.
Bari mu shiga kai tsaye cikin riwayoyin kamar haka;
Ya zo cikin Sahihul-Muslim yana cewa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
حدثنا عمرو بن علي حدثنا عبد الأعلى حدثنا هشام بن أبي عبد الله عن أبي الزبير عن جابر أن رسول الله صلى الله عليه وسلم رأى امرأة فأتى امرأته زينب وهي تمعس منيئة لها فقضى حاجته ثم خرج إلى أصحابه فقال ان المرأة تقبل في صورة شيطان وتدبر في صورة شيطان فإذا أبصر أحدكم امرأة فليأت أهله فإن ذلك يرد ما في نفسه
(1)- Amruu Bn Aliyu ya bamu labari, Abdul-A'alah ya bamu labari, Hishaam Bn Abdullahi ya bamu labari daga baban Zubar, daga Jabir cewa,
" Lalle Annabi (S. A. W. W) ya ga wata mata (wacce ta ba shi sha'awa), sai ya jewa matarsa Zainab yayin da take jimar matarta ya biya buqatarsa (don kawar da wannan sha'awa tasa). Sa'an nan ya fito zuwa ga Sahabbansa yace,
" LALLE ITA MACE TANA FUSKANTOWA NE DA SIFFAR SHAIDAN, KUMA TAKAN JUYA DA SIFFAR SHAIDAN. IDAN 'DAYANKU YAGA WATA MACE (har ta ba shi sha'awa), TO, YA JEWA MATARSA, DOMIN HAKAN ZAI KAWAR DA ABINDA KE ZUCIYARSA (na sha'awa) ."
وحدثني سلمة بن شبيب حدثنا الحسن بن أعين حدثنا معقل عن أبي الزبير قال قال جابر سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول إذا أحدكم أعجبته المرأة فوقعت في قلبه فليعمد إلى امرأته فليواقعها فإن ذلك يرد ما في نفسه
(2)- .......Jabir yace, " Na ji Annabi(S.A.W.W) yana cewa,
" IDAN MACE TA BAWA 'DAYANKU SHA'AWA HAR YA JI WANI ABU CIKIN ZUCIYARSA, TO, YA JEWA MATARSA YA AFKATA MATA, DOMIN HAKAN ZAI KAWAR DA ABINDA KE CIKIN ZUCIYARSA ."
(KITABUN-NIKAH, BABIN WANDA YAGA MACE TA BA SHI SHA'AWAH YA JEWA MATARSA YA BIYA BUQATARSA)
Idan kuma muka koma cikin Qur'ani za muga inda Allah ke umartar Annabi (S. A. W. W) da cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
قُل لِّلۡمُؤۡمِنِينَ يَغُضُّواْ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِمۡ وَيَحۡفَظُواْ فُرُوجَهُمۡۚ ذَٰلِكَ أَزۡكَىٰ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ ٠٣
" KA FADAWA MUMINAI MAZA SU RINTSE IDANUWANSU KUMA SU TSARE FARJOJINSU, HAKAN YA FI TSARKI GARE SU, ALLAH MASANI/MAI BADA LABARI NE GAME DA ABINDA SUKE AIKATAWA ."
(SURATUL-NURR, AYA TA 30)
Annabi (S. A. W. W) shi yafi kowa kiyaye dokokin Allah da kuma aikata umarninSa, saboda haka ya isar da wannan saqo gare su har ma ya hane su zama a bakin hanya don kada suna kallon mata masu wucewa.
Ga maganar nan kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
حديث رقم :190
السابع: عن أَبي سعيد الخُدري رضي الله عنه،
عن النَّبيّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: (إيَّاكُمْ وَالجُلُوسَ في الطُّرُقَاتِ!) فقالوا: يَا رَسُول الله، مَا لنا مِنْ مجالِسِنا بُدٌّ، نتحدث فِيهَا. فَقَالَ رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: (فَإذَا أبَيْتُمْ إلاَّ المَجْلِسَ، فَأَعْطُوا الطَّريقَ حَقَّهُ). قالوا: وما حَقُّ الطَّريقِ يَا رسولَ الله؟ قَالَ: (غَضُّ البَصَرِ، وَكَفُّ الأَذَى، وَرَدُّ السَّلامِ، وَالأمْرُ بِالمَعْرُوفِ، والنَّهيُ عن المُنْكَرِ) مُتَّفَقٌ عَلَيهِ.
Daga baban Sa'eed Al-Khudriy, cewa Annabi (S. A. W. W) yace;
" NA HANE KU GAME DA ZAMA AKAN HANYA. "
Sai suka ce, " Yaa Ma'aikin Allah ! Menene matsala cikin zamanmu matuqar dai hirarmu muke yi a gurin ?" Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" IDAN DAI KUN QI CEWA LALLE SAI KUN ZAUNA (saboda tsarin kanku), TO, KU BAIWA HANYA HAQQOQINTA. "
Suka ce, " Menene haqqoqin hanya yaa Ma'aikin Allah ?" Yace;
" RINTSE IDANUWA DA KAWAR DA ABIN CUTARWA DA AMSA SALLAMA DA UMARNI GAME DA ABU MAI KYAU DA KUMA HANI GAME DA MUMMUNA ."
(RIYADUS-SALIHEEN, KITABUL MUQADDIMA, BABI MAI MAGANA KAN UMARNI DA KYAKKYAWA DA KUMA HANI KAN MUMMUNA, HADISI MAI LAMBA 190)
Amma duk da wannan umarni da Allah yayi masa da kuma yadda shi ma ya isarwa Sahabbansa amma anan suna tabbatar mana ne cewa Shi fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W) fada yake yi ba aiki, domin su sun fi shi kiyayewa tunda za su zauna tare da shi ba tare da sun bude ido sun kalli mace har ta basu sha'awa ba, shi kuma kalle-kalle yake yi har ya hango mace wacce za ta ba shi sha'awa.
" TSARKI YA TABBATA GA MANZONSA GAME DA ABINDA KUKE SIFFANTAWA. "
Sannan kuma idan muka koma cikin Sahihul-Bukhari za muga riwayoyi kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
(إذا جامع ثم عاد، ومن دار على نسائه في غسل واحد)
(268) - حدثنا محمد بن بشار قال: حدثنا معاذ بن هشام قال: حدثني أبي، عن قتادة قال: حدثنا أنس بن مالك قال:
كان النبي صلى الله عليه وسلم يدور على نسائه في الساعة الواحدة، من الليل والنهار، وهن إحدى عشرة قال: قلت لأنس: أو كان يطيقه؟ قال: كنا نتحدث أنه أعطي قوة ثلاثين
وقال سعيد، عن قتادة: إن أنسا حدثهم: تسع نسوة
Bukhairi yace, Muhammad Bn Bashar ya bamu labari yace, Mu'azu Bn Hishaam ya bamu labari yace, Ubaiyu ya bamu labari daga Qatadata yace, Anas Bn Malik ya bamu labari yace,
" Annabi (S. A. W. W) ya kasance yana kewayawa kan matansa (da jima'i) cikin lokaci guda, daga dare da yini, su kuwa (matan nasa) su goma sha daya (11) ne ."
(Qatadata) yace, " Sai muka cewa Anas, yanzu har yana iyawa ? (suna mamaki). Anas yace ;
" AI MUN KASANCE MUNA TATTAUNAWA CEWA AI SHI AN BA SHI QARFIN MUTUM TALATIN (30) ."
Sa'eed kuma yace, daga Qatadata: Lalle Anas ya basu labari cewa mata tara (9).
( KITABUL-GHUSLI, BABIN DAKE MAGANA KAN WANDA YAYI JIMA'I KUMA YA MAIMAITA, DA KUMA WANDA YA KEWAYA KAN MATANSA CIKIN WANKA 'DAYA, HADISI ME LAMBA 268)
Kunga anan su Sahabban da kansu har zama suke yi suna hira a kansa (S. A. W. W. W) game da yadda yake yi da matansa.
Dole anan muyi tambaya cewa shine ya fada musu haka ko kuma wata daga cikin matan ne suka ba su labari ? Ko kuma Anas din yana bibiyarsa ne cikin dakunansa (S. A. W. W) cikin dare da yini ?
Idan muka matsa cikin Babi na gaba mai cewa,
(WANKE MAZIYYI DA KUMA YIN ALWALA DOMINSA)
(غسل المذي والوضوء منه)
Za muga wani hadisi kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
269 - حدثنا أبو الوليد قال: حدثنا زائدة، عن أبي حصين، عن أبي عبد الرحمن، عن علي قال:
كنت رجلا مذاء، فأمرت رجلا أن يسأل النبي صلى الله عليه وسلم، لمكان ابنته، فسأل فقال: (توضأ واغسل ذكرك) [ر: 132]
Baban Walid ya bamu labari yace, Za'idata ya bamu labari, daga baban Hussaini, daga baban Abdurrahman, (wai) daga Aliyu (wai) yace;
" NI NA KASANCE MUTUM NE MAI YAWAN (fitar da) MAZIYYI, SAI NA UMARCI WANI MUTUM DON YA TAMBAYO MIN ANNABI (S A W. W) SABODA MATSAYIN 'YARSA DAKE TARE DANI. SAI YA TAMBAYA, SAI YACE;
" ZA KAYI ALWALA KUMA KA WANKE ZAKARINKA ."
(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUL-GHUSLI)
ABIN LURA
--------------------------
Shi dai maziyyi wani ruwa ne dake fitowa daga Zakarin namiji yayin qaramar sha'awa, sannan kuma haka kawai mutum ba zai yi sha'awa ba dole sai ya ga mace ko kuma ya sanya tunaninta cikin zuciyarsa. Shi kuma wannan tunani nata ba wai saboda ita mace bace, a'a, saboda sha'awar da yake mata ne.
Kunga anan a kaikaice ana so ne a nuna mana cewa su suka fi kowa sha'awar mata tunda su kadai ne aka kawo cewa wani ya hangi mace kawai sai sha'awarta ta tayar masa da tasa sha'awa, wani kuma a kullum cikin sha'awarsu yake.
Idan kuka ce ba haka bane sai nace, to, me yasa ko cikin rarrauna hadisi ba ku kawo wani mai irin wannan dabi'a ba sai su? Kuma ma kuka kawo cikin hadisan ku wadanda kuka ce duk abinda ke cikinsu ya inganta ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
10th March, 2021/ 27th Rajab, 1442.