Matsalolin Yin Aure A Cikin Watanni Biyu Kafin Azumi ( Rajab da Sha'aban ) !!!



Aure sunnah ne na ma'aikin Allah, sannan yana zaman wajibi ne ga duk wanda yake da ikon yin hakan, Allah da manzonsa suna farin ciki da duk wanda ya raya wannan sunnah mai albarka.


Sai dai mafiya yawan lokuta, mukan kaucewa wasu ababen da ya kamata ace muna duba dasu Kafin auren ko saka ranar auren, duba da yanayin zubi da tsari na halittan kowane dan Adam, yanada kyau musan wane lokaci ne ma ya kamata mu rika gudanar da shagulgulan auren mu, akwai ranaku masu muhimmanci a kowane wata, wa'yanda yin aure a cikinsu Allah zaya karawa auren albarka, sannan ma'auratan zasu sami albarkan dake cikin wannan rana din, haka akwai ranekun da kwata kwata baima kamata ayi koda saka ranar aure aciki ba, misalin Nahisan ranaku na kowane wata, saboda hadarin da ranekun ke kunshe dashi.



A yanzu bama duba da irin wa'yannan ababen, dama wasu da daman gaske wa'yanda ba wajibi bane, amma suna zaman nemawa kai rahama da yardan Allah idan akayi aure ko saka rana aciki.


MATSALOLIN YIN AURE CIKIN WATANNI BIYUN KAFIN AZUMI (RAJAB DA SHA'ABAN) : wa'yannan watanni na daya daga cikin watanni masu muhimmanci, cikin watanni goma sha biyu dake garemu a musulunci, sunada falala sosan gaske sannan akwai A'amal da yawan gaske da akeyi a Ciki, tun daga azumi sallah da sauransu, suna daf ne da watan Ramadan wanda akeyin azumi na wajibi a cikinsa, wanda dole indai ba wani larura na rashin lafiya ba to dole ne ga duk wani baligin dan Adam wanda yake ansa sunan shi musulmi ne.



A lokutan baya, kakanninmu sukan aurar da iyayenmu cikin irin wa'yannan watanni, kuma ba wani abu da yake faruwa dalilin hakan, amma a yanzu zamani ya sanja komi, yin aure a irin wannan lokutan yana taka muhimmiyar rawa wurin sabawa Allah a lokacin yin ibadar wajibi wato azumin Ramadan, a yanzu kan kowa ya waye da sunan zamani, yawan kallace kallacen fina finai da videos marasa kyau, shigar banza da matanmu sukeyi, kuma suke daukanta wayewa da maganganu marasa kan gado, su kadai sukan tadawa matasa da yan mata na yanzu sha'awa ba sai an kebe tsakanin mace da namiji ba, wanda hakan ya tasirantu sosan gaske ga jikunna da zukatan matasa da yan matan yanzu, shine kuma yake taimakawa idan anyi aure ba'a iya hakura ko hadiye wannan sha'awa din, indai ana gani kuma anajin juna,  saboda dama tun kafin ayi auren yana hakuri ne itama haka.......... 


Zan cigaba insha Allah


✍🏽Zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post