SHIRU KAKE JI...
Bayan janye ka'idar da 'yan maja suka fake da ita na hana *Mukabala*/Zaman tutsiye da Dr. Abduljabbar Kabara kamar yadda suke fada sai muka ji tsit, sun yi shiru kamar an dauke NEPA ko kuma ince kamar anyi ruwa an dauke, akan batun Mukabala da Sheikh Abduljabbar malaman maja sai zillewa suke yi tun a wancan karon da gwamnatin Kano tasa lokaci da wuri domin tantancewa tsakanin gaskiya da kuma karya Wanda matakin yasha suka daga mabanbantan bangarori Wanda wadannan malamai suka fito daga cikinsu.
Gwamna ya dauki wancan mataki ne domin yiwa Dr. Abduljabbar da kuma tsagensa adalci kamar yadda shi ya nema da a zauna domin jama'a su gane gaskiya shi kuma ya fita daga zargin da mafi yawan wadanda basu fahimci abin ba suke yi masa.
Sun fake da wata kara da wani lauyan gwamnati ya shigar tun a kwanakin baya da cewa Kotu ta hana zaman Mukabala da Sheikh Abduljabbar amma da zarar kotu ta janye wancan umarnin to ashirye suke da su zauna dashi domin tuhuma/tutsiye akan abin da suka yadawa al'umma na sharri da kage Wanda suka yi masa.
Allah(SWT) cikin ikonsa da buwayarsa wancan umarni na kotu yakau (babu shi) sakamakon janye kara da shi lauyan da ya shigar da karan yayi, baya ga haka sai malamai 'yan maja suka yi tsit, shiru kake ji a shafukansu na sada zaumunta, Masallatansu da kuma wurare da suke gabatar da Karatuttuka inda suke kage da yada sharri ga Sheikh Abduljabbar ba don komai ba sai don ruruta wutar gaba da kiyayya a tsakanin al-umma da kara taimakawa wajen rabuwar kawunan al-umma da yin tunzuri ga mabiyansu domin su tada tarzoma.
Sun ki fitowa fili a masallatan, wuraren karatun da shafukan sada zumuntan domin su bayyana amincewarsu akan zaman mukabala da Sheikh Abduljabbar kamar yadda a baya suka yi ta kumfan baki cewa a shirye suke su zauna da shi da zarar gwamnati ta saka lokaci kuma kotu ta janye wancan umarnin da tayi.
Sai dai kash! Abin yaci tura, yanzu a kano a rasa malamin da zai fito domin kare Shugaba (S) da sahabbansa kamar yadda suke ikirari?
Kada Ku dubi lamuran duniya ko wani Abu da zai iya saminku a wannan duniya domin zaku barta kuma komai mai wucewa ne , Ku dubi girman Allah, martabar Manzo(S), iyalan gidansa (AS) da sahabbansa ku fito Ku tutsiye Malam Abduljabbar kamar yadda kuke yadawa mutane a baya kafin su ganeku, shi kuma Malam ya kare kansa, Abu ne na 'yan muntoci ba wani lokaci za'a dauka ba shikenan a yi a gama kowa ya huta.
Abin da malaman maja basu sani ba a yanzu shine: mafi yawan daliban da suke zaune a gabansu sun fara ganosu domin kuwa suna ji kuma suna ganin abin da abin da yake zuwa yana zauwa, domin sun fara tambayoyi, kuma Alhamdulillah ko anan aka tsaya Sheikh Abduljabbar yaci nasara saboda ya canza system din karatun addini a kasarnan, ada idan kayi tambaya idan babu amsar da za'a baka sai ayi kokarin rufe maka baki da wasu maganganu Wanda ko hikima babu a cikinsu domin dai kawai a tsorata ka kada ka cika bincike ka gano gaskiya, kuma da dama hakan na budewa matasa sassaukar hanyar afkawa cikin Ilhadi (atheism). Su kuma malamai irin 'yan majar kano daga ranar da gaskiya ta bayyana to tasu ta kare shiyasa suke ta kokarin kada ayi wancan zama domin tantance tsakanin tsakuwa da tsaba a bainar jama'a.
Amma yanzu tambayoyi kake ji ta ko'ina kamar ruwa suna sauka a kowane masallaci, wurin karatu ko shafin sada zumunta kuma sun gagaresu sannan basu da amsoshin da zasu bayar, wannan shine babban dalilin yi gamayyarsu a kano domin basu da wata sahihiyar hanya ta amsa wadancan tambayoyi to sai suka kulla makirci suka yiwa Dr. Abduljabbar sharri da cewa wai yana batanci ga Shugaba (SAWA) bayan duk duniya ta shedeshi akan bada kariya ga Annabi (SAWA) a duk inda ya tsinci kansa. Amma a yau saboda tsabar tsagwaron kin Allah na wadannan malamai sai suka yi gayyar maja suka yi gangami suka yada cewa Dr. Abduljabbar yana batanci ga Shugaba (SAWA) ko kunya babu.
A tsarinsu, su abin da suka so a kasheshi shiyasa suke ta nuna rashin goyan-bayansu akan Zama dashi, wasu jigogi daga kowane bangare na 'yan maja kama daga wahabiyawa, Tijjanawa da kadirawa sun yi ta zillewa wancan zama na masalaha da gwamnatin kano ta shirya karkashin jagorancin maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin yin adalci ga dukkan bangarori. A cikin wadanda suka dinga zillewa da kawo kushe a cikin masalahar da gwamna ya shirya har da Jama'atu Nasril Islam(JNI) karkashin jagorancin Sarkin musulmi, matsayar JNI da mafi yawa daga cikin masu suka ga masalahar nan ita ce, kawai a zartar masa da hukunci, hukuncinma na kisa, kawai a kashe shi ba tare da bincike ko bashi damar kare kansa ba. Wannan mummunan rashin adalci ne!
Abin da 'yan maja suke mantawa harkulum shine: a yanzu muna karni na 21(wato 21st century) yanzu zamani ne na ilimi a zahirance, ba wai labaran kanzon kurege ba kamar yadda suke yi a masallatai da makarantu.
Hanya mafi sauki da zaku bi domin ganin kun yiwa Dr. Abduljabbar tutsiye ko raddi na yankan shakku shine, Kubi ta hanyar da ya biyo, Ku karanta lafazin hadisi, Ku fadi sunan littafi da lambar shafin da za'a duba a samu hadisi kamar yadda yake yi, sannan kuma nasan Ku da kanku kuna dubawa Ku tabbatar, amma wannan hanya da kuka dauko ba mai bullewa bace domin a iya 'yan kwanakin nan kun fahimci hakan, shi ramin karya kurarrene kuma a Dade ana yi sai gaskiya.
*Malaman Maja sun tabbatar da haka*
Sun tabbatar Sheikh Abduljabbar ba jahili bane, malami ne kuma mai ilimi sosai, sun tabbatar ba mahaukaci bane domin mahaukaci ba zai iya aikin da yake na tantance hadisai ba, sai dai ba zasu iya rabuwa da fahimtar magabatansu ba su bishi saboda magabata ba haka suka fassara ba, sannan kuma ya fito da Sabon abu ne Wanda basu sani ba kuma magabata ba haka suka yi ba.
*Tambaya* : shin ranar kiyama idan kaje gaban Allah cewa zaka yi haka magabata suka yi kuma haka suka ce ayi idan an same ka da wani laifi?
Don Allah Dan uwa ka nutsu ka auna da hankali, 'Da ace Allah yana son kabi abin da magabata suka aikata sau-da-kafa to da ba zai yi maka kwalwa ya saka maka hankali da tunani ba domin tantance mummuna da kyakkyawa' da sai ya yika hakanan ba tare da wadancan muhimman abubuwa ba.
To Amma sai Allah ya saka maka duk wannan domin ka tantance duk wani abu da zaka aikata.
Magabata zasu iya kuskure kai kuma da kazo daga baya ka gyara, sannan kuma su lokacinsu ya wuce wasu abubuwa da dama basu bullo ba sai a lokacinka, ka ga ba dole sai ka ji daga magabata akan wannan batun ba.
A takaice magabata kan iya kuskure a gyara masu kamar yadda kaima bai zallakeka ba.
*Rufewa*
Daga karshe abin da nake so na fito dashi a duk wannan shine:
*a. Tambayoyi da malaman maja suka kasa bada amsoshinsu ga dalibansu shine yasa su yin wannan gamayyar* Wanda na ji daya daga cikinsu yana fada cewa, su kadai suka San musibar da suke fuskanta domin kullum idan Dr. Abduljabbar yayi sabon karatu sai an cikasu da tambayoyi wadanda basu da amsoshinsu.
*b. Jin haushin Sheikh Abduljabbar ya fito da sabon abu Wanda babu wanda ya iya fito dashi daga cikinsu* "don me bamu muka gane ba sai shi kadai?" Tambayar da suke yi a tsakaninsu.
Sai hakuri shi Allah ya zaba ya fahimtar dashi, abin da ya rage muku kawai biyayya.
*c. Hassada da suke yi masa akan dukakar da yake ta samu a kullum*.
Wannan shine dalilin yin maja a kano akan Bawan Allah guda daya tal.
*Allah kayi riko da hannunsa ka kare shi daga dukkan sharri.*
*©A A Wisdom Daura*
AKAFSAN (Katsina).