Mahaifan Annabi (S) 'Yan Wuta ne, _In ji Sahabi Umar Dan Khaddab !!!



MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


HUJJOJI CIKIN LITTAFAN AHLUS-SUNNAH WAL JAMAA'AH


Ban san da me zan iya fassara wannan magana tasu ba, soyayya ga Annabi (S. A. W. W) ce ko kuma dai qiyayyarsu ce gare shi  ? Domin na san kowa na fatan mahaifansa su shiga Aljannah ko da kuwa sun mutu suna kafirai ne saboda ceton da Annabi (S. A. W. W) sai yiwa al'ummarsa.


Akwai wani hadisi dana taba karantawa wanda ke cewa wai wata rana wani mutum ya tambayi Manzon Allah (S. A. W. W) cewa, " INA BABANKA YAKE  ?"


Wai sai Annabi (S. A. W. W) yace masa ;


" BABANA DA BABANKA SUNA WUTA  !"


Nayi qoqarin samo wannan riwaya don na nuna muku ita amma Allah bai Qaddara na samota ba, sai dai duk na haka na kalato muku wasu riwayoyi a matsayin hujja. Ga riwayoyin nan kamar haka :


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وقال الإمام أحمد  حدثنا الحسن بن موسى حدثنا زهير حدثنا زبيد بن الحارث اليامي عن محارب بن دثار عن ابن بريدة عن أبيه قال كنا مع النبي صلى الله عليه وسلم ونحن في سفر فنزل بنا ونحن قريب من ألف راكب فصلى ركعتين ثم أقبل علينا بوجهه وعيناه تذرفان فقام إليه عمر بن الخطاب وفداه بالأب والأم وقال يا رسول الله مالك قال إني سألت ربي عز وجل في الاستغفار لأمي فلم يأذن لي فدمعت عيناي رحمة لها من النار وإني كنت نهيتكم عن ثلاث نهيتكم عن زيارة القبور فزوروها لتذكركم زيارتها خيرا ونهيتكم عن لحوم الأضاحي بعد ثلاث فكلوا وامسكوا ما شئتم ونهيتكم عن الأشربة في الأوعية فاشربوا في أي وعاء شئتم ولا تشربوا مسكرا


Imamu Ahmad yace, Hassan Bn Musa ya bamu labari, Zuhairu ya bamu labari, Zubaid Bn Haarith Al-Yaamiy ya bamu labari daga Maharibu Bn Dithaar, daga Ibn Buraidata, daga babansa yace :


" Mun kasance tare da Annabi (S. A. W. W) yayin da muke cikin wata tafiya, sai ya sauka tare damu, a lokacin mu mahaya (riders) munyi kusan dubu (1000), sai muka yi sallah raka'ah biyu, sannan ya juyo gare mu da fuskarsa idanuwansa (S. A. W. W) na zubar da hawaye (tears). Sai Umar Bn Khaddab ya miqe zuwa gare shi ya nemi fansarsa da Uwa da Uba, sai yace ; " Yaa Ma'aikin Allah  ! Menene (wannan) gare ka  ?" Sai yace :


" LALLE NI NA ROQI UBANGIJINA MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NE DON NEMAWA MAHAIFIYATA GAFARA AMMA BAI YI MIN IZNI BA. SHINE IDANUWA KE ZUBAR DA HAWAYE SABODA TAUSAYINTA DAGA WUTA. KUMA NI NA KASANCE NA HANE KU GAME DA ABUBUWA UKU, (a baya) NA HANE KU GAME DA ZIYARTAR QABARI AMMA YANZU KU ZIYARCE SHI DOMIN ZIYARAR TATATA TUNA MUKU AIKHAIRI, KUMA NA HANE KU GAME DA (cin) NAMAN LAHIYA BAYAN KWANA UKU, TO, (yanzu) KUCI KUMA KU 'DEBI ABINDA KUKE SO, SANNAN KUMA NA HANE KU DA SHA CIKIN KWANUKA, YANZU KU SHA CIKIN KOWANNE KWANO DA KUKE SO, AMMA KADA KU SHA ABINDA KE SA MAYE  ."


(MUSNAD-AHMAD , J:5, SH:355 ).


Cikin riwaya ta 'Dabari kuma yana cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وروى ابن جرير من حديث علقمة بن مرثد عن سليمان بن بريدة عن أبيه أن النبي صلى الله عليه وسلم لما قدم مكة أتى رسم قبر فجلس إليه فجعل يخاطب ثم قال مستعبرا فقلنا يا رسول الله إنا رابنا ماصنعت قال إني استأذنت ربي في زيارة قبر أمي فأذن لي واستأذنته في الاستغفار لها فلم يأذن لي فما رؤي باكيا أكثر من يومئذ



Ibn Jareer ya riwaito daga hadisin Alqamata Bn Marthadi, daga Sulaiman Bn Buraidata, daga babansa cewa,  


" Yayin da Annabi (S. A. W. W) ya iso Makkah sai ya tafi kan wani Qabari, sai ya zauna a wajensa yana ta yin Khuduba, sa'an nan ya miqe da hanzari. Sai muka ce masa, Yaa Ma'akin Allah  ! Lalle munga abinda ka aikata . " Yace ;


" LALLE NI NA NEMI IZNIN UBANGIJINA NE KAN ZIYARTAR QABARIN MAHAIFIYATA SAI YAYI MIN IZNI, SAI NA NEMI IZNINSA DON NEMA MATA GAFARA AMMA (ya qi) BAI YI MIN IZNI BA  ." (Baban Buraidata yace), " Bamu taba ganin kuka mai yawa daga wannan lokacin ba  ."


Ma'ana, tun da suke a rayuwa basu taba ganin wanda yayi kuka kamar Manzon Allah (S. A. W. W) kafin da kuma bayan wannan lokaci ba saboda Allah ya qi amince masa ya nemawa mahaifiyarsa gafara). 


Shi kuma Ibn Abiy Haateem cewa yayi; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 وقال ابن أبي حاتم في تفسيره حدثنا أبي حدثنا خالد بن خداش حدثنا عبد الله بن وهب عن ابن جريج عن أيوب بن هانئ عن مسروق عن عبد اللهبن مسعود قال خرج رسول الله صلى الله عليه وسلم يوما إلى المقابر فاتبعناه فجاء حتى جلس إلى قبر منها فناجاه طويلا ثم بكى فبكينا لبكائه ثم قام فقام إليه عمر بن الخطاب فدعاه ثم دعانا فقال ما أبكاكم فقلنا بكينا لبكائك قال إن القبر الذي جلست عنده قبر آمنة وإني استأذنت ربي في زيارتها فأذن لي ثم أورده من وجه آخر ثم ذكر من حديث ابن مسعود قريبا منه وفيه وإني استأذنت ربي في الدعاء لها فلم يأذن لي وأنزل علي « ما كان للنبي والذين آمنوا » الآية فأخذني ما يأخذ الولد للوالد وكنت نهيتكم عن زيارة القبور فزوروها فإنها تذكر الآخرة


Ibn Abiy Haateem ya fada cikin Tafsiri nasa cewa, babana ya bani labari, Khalid Bn Khaddash ya bamu labari daga Abdullahi Bn Wahbin, daga Ibn Juraij, daga Ayuba Bn Haani'I, daga Masruq, daga Abdul-Lahabin Masruq yace, " Wata rana Manzon Allah (S. A. W. W) ya fita zuwa Maqabarta sai muka bi shi, yazo har ya zauna a jikin wani Qabari, ya gana dashi tsahon lokaci sannan yayi kuka  ! Sai muma muka yi kuka saboda (ganin) kukansa (S. A. W. W), sa'an nan ya miqe, sai Umar Bn Khaddab ma ya miqe zuwa gare shi , ya kiraye shi sannan muma ya kiraye mu. Sai yace; 


" KUKAN ME KUKE YI  ?"


Sai muka ce, " Muna kuka ne saboda ganin kukanka  ." Yace; 


" KUNGA WANNAN QABARIN DANA ZAUNA A WAJENSA (ai) QABARIN AMINA (mahaifiyata) CE, NA ROQI UBANGIJINA NE DON ZIYARTARTA SAI KUMA YAYI MIN. "


Ya qara riwaito shi kuma ta wata fuskar , sannan ya ambato cikin hadisin Ibn Mas'ud (mai ma'ana) kamar tasa, a cikin nasa ya qara da cewa; 


" KUMA NI NA NEMI IZNIN UBANGIJINA NE DON NAYI MATA ADDU'AH (ta neman gafara gare ta) AMMA (Allah) BAI YI MIN IZNI BA. (maimakon hakan ma) SAI AKA SAUKAR A KAINA 😢 😢 😢; 


" BA YA KASANCEWA GA ANNABI DA MA WADANDA SUKA YI IMANI....... "


" SAI IRIN ABINDA KE KAMA MAHAIFI GA 'DA (tausayi) YA KAMA NI. NA KASANCE NA HANE KU GAME DA ZIYARTAR QABARI (a baya, amma yanzu) KU ZIYARCE SHI DOMIN SHI YANA TUNATAR DA LAHIRA. "


A wani hadisi na dabam kuma 'Dabarani yace, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 « حديث آخر » في معناه قال الطبراني  حدثنا محمد بن علي المروزي حدثنا أبو الدرداء عبد العزيز بن منيب حدثنا إسحاق بن عبد الله بن كيسان عن أبيه عن عكرمة عن ابن عباس أن رسول الله صلى الله عليه وسلم لما أقبل من غزوة تبوك واعتمر فلما هبط من ثنية عسفان أمر أصحابه أن استندوا إلى العقبة حتى أرجع إليكم فذهب فنزل على قبر أمه فناجى ربه طويلا ثم إنه بكى فاشتد بكاؤه وبكى هؤلاء لبكائه وقالوا مابكى نبي الله بهذا المكان إلا وقد أحدث في أمته شيئا لا تطيقه فلما بكى بكى هؤلاء معه قام فرجع اليهم فقال ما يبكيكم قالوا يانبي الله بكينا لبكائك فقلنا لعله أحدث في أمتك شيء لا تطيقه قال لا وقد كان بعضه ولكن نزلت على قبر أمي فسألت الله أن يأذن لي في شفاعتها يوم القيامة فأبى الله أن يأذن لي فرحمتها وهي أمي فبكيت ثم جاءني جبريل فقال « وما كان استغفار إبراهيم لأبيه إلا عن موعدة وعدها إياه فلما تبين له أنه عدو لله تبرأ منه » فتبرأ أنت من أمك كما تبرأ إبراهيم من أبيه فرحمتها ............


Muhammad Bn Aliyu Al-Marwizeey ya bamu labari, Abu Darda'i Abdul-Azeez Bn Muneeb ya bamu labari ,Ishaq Bn Abdullahi Bn Kaisaan ya bamu labari daga babansa daga Ikramata daga Ibn Abbas cewa yayin da Manzon Allah (S. A. W. W) ya dawo daga yaqin Tabuka da kuma Umra, yayin daya sauka a wani guri da ake kira Asfaan sai ya umarci  Sahabbansa cewa;


" KU TSAYA A AQABA HAR SAI NA DAWO GARE KU  ."


Sai ya tafi ya sauka a Qabarin mahaifiyarsa ya gana da Ubangijinsa na tsahon lokaci, sa'an nan yayi kuka 😭😭😭, kukan nasa yayi tsanani !  Sai wadannan ma suka yi kuka 😭😭😭😭😭😭😭 saboda kukansa (S. A. W. W). Suka ce, 


" Kai  ! Annabin Allah ba ya kuka a wannan guri face an ba shi labarin wani abu ne ga al'ummarsa wanda ba za su iya dauka ba. 


To, yayin da yayi kuka suma wadanda ke tare da shi suka yi kuka sai ya miqe ya dawo gare su yace; 


" KUKAN ME KUKE YI NE  ?"


" Yaa Ma'aikin Allah  ! Muna kuka ne saboda kukanka. Muka ce wataqila an saukar da wani abu ne kan al'ummarka wanda ba za su iya dauka ba  ." Yace; 


" A'A, YA KASANCE DAI SASHENSA NE, SAI DAI NA SAUKA NE A QABARIN MAHAIFIYTA NA ROQI ALLAH YA BANI CETONTA RANAR ALQIYAMA, AMMA SAI ALLAH YA QI YAYI MIN IZNI. SAI NA TAUSAYA MATA 😭😭😭😭SABODA MAHAIFIYATA CE, SAI NAYI KUKA.  SA'AN NAN JIBRILU YAZO MIN YACE; 


" AI ISTIGFARIN NAN DA IBRAHIM YA YIWA MAHAIFINSA BAI KASANCE BA FACE WANI ALQAWARI NE DA AKA ALQAWARANTA MASA, AMMA YAYIN DA TA BAYYANA GARE SHI CEWA SHI (baban nasa) MAQIYIN ALLAH NE SAI YA BARRANTA DAGA GARE SHI ."


(Saboda haka)  " KAIMA KA BARRANTA DAGA MAHAIFIYARKA  😭😭😭😭😭 KAMAR YADDA IBRAHIM YA BARRANTA DAGA MAHAIFINSA.  SHINE NA TAUSAYA MATA.......... "


(TAFSIRIL-'DABARIY,  11/12049 )


Wannan shine abinda ya tabbata daga cikin littafan Ahlus-Sunnah masu da'awar wai sune masoyan Annabi (S. A. W. W)  kuma wai masu bin sunnarsa amma suka kai mahaifansa wuta ba tare da wata hujja ba sai dai tsananin qiyayyarsu gare shi (S. A. W. W). 



Amma da shike ba kunya ce gare su ba sun iya riwaitowa cikin littafinsu cewa Annabi (S. A. W. W)  zai cece al'ummarsa, amma kuma Allah zai ba shi wannan damar ce kadai kan iyayensu banda mahaifansa ko da ma ya tabbata suna wutan, tunda sunce Allah ya qi ya bashi cetonsu har Annabi (S. A. W. W) yayi kuka wanda basu taba ganin irinsa ba. 


Ga abinda suka fada cikin Sahihul-Muslim game da ceton da Annabi (S. A. W. W) zai yi ga al'ummarsa. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



وحدثني محمد بن أحمد بن أبي خلف حدثنا روح حدثنا بن جريح قال أخبرني أبو الزبير أنه سمع جابر بن عبد الله يقول عن النبي صلى الله عليه وسلم لكل نبي دعوة قد دعا بها في أمته وخبأت دعوتي شفاعة لأمتي يوم القيامة


Muhammad Bn Ahmad Bn Abiy Khalfu ya bamu labari , Rauhu ya bamu labari, Ibn Juraij ya bamu labari yace, baban Zubair  ya bani labari cewa ya ji Jabir Bn Abdullahi (R. A) yana cewa, daga Annabi(S.A.W.W) yace; 


" KOWANNE ANNABI AKWAI WATA ADDU'AR DA YAYI ROQO DA ITA CIKIN AL'UMMARSA, NI KUMA NA ZABI ADDU'AH TA ITA CE CETON AL'UMMATA RANAR ALQIYAMA  ."


Wannan hadisi yazo ne cikin Babin da ke cewa,



 12- لكل نبي دعوة قد دعا بها في أمته وخبأت دعوتي شفاعة لأمتي يوم القيامة


(MUSLIM, KITABUL IMAAN, BABIN DA KE MAGANA KAN CEWA ABINDA ANNABI (S. A. W. W) YA ZABA SHINE CETON AL'UMMARSA RANAR ALQIYAMA)


Yaa Ubangiji Allah ina roqonka ka kaini duk gurin da ka kai mahaifan Manzonka Muhammad (S. A. W. W). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


          (08137925034)


9th March, 2021/  26th Rajab, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post