*Gabatarwa:*
Da sunan Ubangijin nan da yai alkawarin jarraba Muminai don ya dauki wasunsu a matsayin shahidai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda ya zo da tafarkin shahada, da iyalansa shugabannin shahidai.
Ba shakka, mun sani ko ba mu sani ba, sadaukarwar shahidanmu ne ta zamo mana garkuwar da ke ba mu karfin guiwar tunkarar zalunci da azzalumai a kullum. Saboda haka, a bayyane yake cewa da bazar wadannan shahidai masu girma muke ci gaba da numfashi sannan muke iya tabuka dan abin da muke iyawa.
Wadannan muklisan bayin Allah jarumai, haka suka rufe ido suka fanshi rayuwarmu da tasu. Suka bayar da rayuwarsu don wanzuwar addini. Ashe babu abin da za mu saka musu da shi kamar mu tsayu a kan tafarkin da suka tafi, mu ci gaba da ayyukansu da suka bar mana.
Daukar fansarsu da muke ambatawa a kullum, mun karyata da ayyukan gabobinmu. Wace rana ce ba mu furta za mu dauki fansarsu ba? Tsakani da Allah mun dauki hanyar daukar fansar jinanen nasu da gaske bayan mun kasa tsaiwa yadda ya kamata a kan ayyukan da suka bar mana? Ashe hakan ba tabar da jagoranmu ba ne?
Matakin farko na daukar fansar jinanen shahidanmu masu alfarma shi ne tabbatuwa da wanzuwa a kan turbar da suka yi shahada. Yanzu za mu iya kwatanta tazarar himmarmu a da, da kuma a yanzu? Yaya za mu auna irin rauni da tozarcin da muka yafa wa kanmu na sakaci da kuma yin biris ko sako sako da ayyukan da wadannan shahidai masu girma suka bar mana mu ci gaba da aikatawa?
Ashe ba mu muke fadin cewa, kewar shuhada tana kara mana kumaji a kan wannan aikin ba? Rashinsu kuma yana zaburar da mu ba? Muka ce ayyukan da suka yi za su ci gaba da kasancewa dalilin kara dakewarmu a kan addini.
Har muka ce su rayayyu ne a zukatanmu, kuma masu tasiri ne a ayyukanmu. Me ya sa muka saba wadannan maganganun a yau? Da wane ido za mu kalli shahidanmu? Ashe bai zama cin amanar alkawarin da muke yi wa shahidanmu na tabbata a tafarkinsu ba? Ashe karya ce da yaudara kawai muke furtawa?
Mu ne fa muke ambatawa a dare da rana cewar tunaninsu a zuciya wani rayayyen radadi ne a rayuwa wanda yake shajja'a mu a kowane lokaci, kuma yake ba mu dalilin kara daura damara, shi yake ba mu kwarin guiwa a tafarkin gwagwarmaya. Da gaske yanzun haka muke?
Ba mu ne muka ce, alkawari ne jininsu ba zai zuba a banza ba? Ba mu furta cewa bin hakkin jininsu wani asasi ne da makiya suka assasa da kawukansu ba? Kuma muka ce radadin rasa su tamkar wani kurji ne a tsakiyar zuciya da azzalumai suka samar, shin kurjin bai mana ciwo ne? Ko kuma yanzu kurjin ya warke ne? Ashe ba za mu sanya makiya nadamar ayyukansu tun da wuri kafin kurewar lokaci ba?
Ya zama wajibi kuma kalubale ne mafi girma a gare mu, mu canza. Mu hankalta tun muna da sauran lokaci. Dama aba ce mai gaggawar kubucewa, kuma mai jinkirin dawowa. Ba shakka wannan shi ne abu mafi soyuwa ga shahidanmu.
Muna fatan Allah ya tausaya mana ya dube mu da idon rahama, ya taimake mu wajen faranta ran shahidanmu masu daraja, ta hanyar tsaiwa a kan ayyukan da suka bar mana, kuma suka mana wasiyyar tabbatuwa a kansu har mu riskesu. Allah ya kara wa shahidanmu daukaka da matsayi, ya sa mu riske su a matsayinsu.
*Ankaranta wannan takardar Ranar Maulidin Abulfadal Abbas* *(a.s) A Abuja. a wannan ranar ta*
*18/03/2021*
*JASAZ SHUHADA*
*31th march, 2021*