Ko Ka San Wannan Acikin Shekaru 40 Na Da'awar Sherkh Zakzaky (h) ??

 


A cikin shekaru Arba'in na da'awar sa ya canza Miliyoyin mutane tare da karantar da su sahihiyar hanyar da Manzon Allah (Saww), yayi wasiya akanta. A cikin wannan shekarun da yayi yana wa'azi, Azzalumai da Munafukai da Yahudawa makiya Addinin Allah (swt), sun daure shi a gidajen kurkuku daban-daban inda ya shiga gidan Yari daban-daban sama da goma, wanda yanzu haka da nake rubutunan Malam Zakzaky (h) yana hannun Gwamnatin Nigeria a tsare, sama da shekara Biyar bayan sun dauke shi ba ya Lumfashi a gidan sa da ke Zaria, Kaduna.



Kowa ya sani kafin suyi hakan sai da suka kashe sama da Mutum Dubu a cikin Almajiransa ciki harda Ya'yansa guda Ukku. NAN GABA KAƊAN AL'UMMA NIGERIA ZASU KILLA CE TARIHIN WANNAN GWARZON JAGORAN, TARE DA SADA SHI ZUWA GA YA'YA DA JIKOKI. MAFITARMU ITACE SALLAMAWA DA YI MASA BAI'A.



Babban abin da ya sa nake kara jinjina ga Malam Zakzaky (H), shi ne ta yadda Allah ya bashi zukatan Muminai masana ilimi da aiki da shi. Kaf Al'ummar Nigeria babu mutanen da suka kai Yan Shi'a daidai to akan dukkan abin da ya shafi mu'amalar Rayuwa. Gaskiya, Rikon Amana, Nema Ilimi da aiki dashi, son zaman lafiya, da neman Sakayya akan duk wanda aka zalunta. Basa bari a zalunce su, kuma basu yarda suyi zalunci ba. 



Daga cikin koyarwar Malam Zakzaky akwai son juna da hadin kan Al'ummar musulmi. Kusan a wannan bangaren wannan bawan Allah yayi nisa, duk inda kaga dan shi'a zaka gansa akwai son hadin kai komin yadda kuke kiyayya dashi, in wani abu na murna ko na bakin ciki ya samu zai zo ya tayaka jaje ko murna. 



ALLAH YA KARA TAIMAKON WANNAN BABBA GWARZON SHAIKH IBRAHEEM YAQOUB ZAKZAKY (H), KA CIKA MASA BURINSA.



_j. Sabo

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post